Chapter 25
Chapter 25
bakisan wani abuba yanda kika san yar bariki haka yarinyar nan take ni wani zubin har mamakinta nike...ta'iya takunta dan juya Rid take kamar wata waina shiya sa nakesan had'ata da boka gobe da nisa dan agaskia wajan iya kissa ta kereni sosai . To ke mesa baza ki tsaya ki kowi kissar ba Haba kawa kin sani sare da'' j'ai pas ce temps là'' kokin manta fansa ce dalilin auren Rid danayi.??dan Wly sena rabashi da kowa nasa To kuwa tunda hakane kina da gaskiya Bokan ne kade zai iya mana maganinta da kuma cika miki burinki(kqji wani shirme ...Allah de ya shirya) amman wani hanzari ba gudu ba bana tsanmanin yana garin saboda ........bata karasa ba Halima taja wani wawan birki jikake qiiiiiiiiiiiiiiii Allah ya taimakesu babu wani bayan su da ya shigesu tace ban ganeba baya gari Kin san fah every five month yake zuwa kasar su Aljani dan kundalo👹 wajan wani event na zubadda jini da sukeyi kuma event din yana daukan kusan one or two months Bakinki yasari danyan kashi to ai idan bamu same shi ba ciwon zuciya yarinyar nan zata sakamin....key yana ma nan taja motar da gudun tsiya .... Isowarsu kenan suka ga wurin wayam alamu sun nuna baya nan din tayi tsaki yafi a kilga sukayi ribos cike da takaici dan harda yar karamar kwalla tayi sai wajejen 16h(hudu na yamma) suka shigo gari ta ajiye kawarta ta fice gida duk da ita ke da girki kuma tasan ana kaiwa gidan Papy dan diner amman tayi shigewar ta daki ta kwanta dan dama bawani girkin ta'iya ba dan ko farar shimkafa bata iya dafawa ba because sau daya tataba dafawa tacikawa rice din ruwa da gishiri dan ko Almajirai kasa ci sukayi...da'aka basu NOTE :gareku iyaye mata ku tilastawa y'ay'aku wurin koyan girki da aikace2 gida kafin ayi musu aure..dan walahi i Saboda namiji duk iya kissa da Iya tarerayar ki idan har baki iya girki ba tofa da sauranki.dan .zakiga kunyi fada da mijinki amman kun shirya wurin cin abinci ... Kuki yaye.. Tunatarwace🙏 Itako Manane ko bayan dawo warta gidan Salma ta tafi dan duba jikinta daga can ma gidan Papy suka huce Bayan isha'i yashigo gidan suka fice shida Halima duk da ya lura da hannunta babu kwanan abinci amma beyi mata magana Isowar su suka ga duka *zuri'ar* sun hallara zama sukayi suma akaci gaba da hira daga baya kuma aka zuba abinci akaci kamar kulum A hanyar su tada wowa ne Umma taja hannun Manane suka keb'e tace ya banga kwanan gidanku ba tace nikaina bansan ya akayi ba dan banice da girki ba kuma ko bayan dawo wata gidan Salma na. Tafi dan duba jikinta gyada kai kawai Umma tayi ta fice bayan sun shigo kowan nan su dakinshi ya nufa Bayan shigarshi daki kamar kullum yayi komi na al'adarshi yabi lafiyar gado A bangaren Halima kuwa wanka tayi ta feshe jikinta da turaruka tasha wata shegiyar rigar bacci net wanda ko cinya bata rufeba ta zauna zaman jiran Rid dan acewarta tunda yana zuwa kwana dakin Manane dole ne ita ma yazo dakinta duk da yau din amatse take da shi har sha biyu ta gota taji shiru dole ta tashi ta fice dakin nashi Kwance ta iske shi yana tunanin Manane bema san da shigowarta se da ta hau gadon ta kira sunanshi ..firgit ya dawo daga duniyar tunanin ya kalleta .. Harara ta watsa mishi tace shine inacan jiranka ka shanya ni? Tsuka yayi ya juya mata baya .. Tabe baki tayi ta kwanta nan bayanshi kasa jurewa tayi dan haka seta matso ta shige jikinshi .. Niyyar juyowa yayi ya mata magana kawai setayi sauri ta rungumeshi ta shiga kissing dinshi da mamaki yake kallon ta dan rabon da ta bashi hakkishi ma tun ranar data cika 3days dinta shid'in ma da kyar ta bashi.. Bashida wani zabin da ya fice yabiye mata dan shima a matsan yake soboda kwana biyun nan daya yayi a dakin Manane dauriya kawai ya keyi. suka lula duniyar ma 'aurata kwatsam sai taji yana kiranta da sunan Manane tare da sambatu ai bashiri ta ture shi ta sa wani wawon ihu me hade da kuka shiko k'ara janyota yayi yaci gaba daga inda ya tsaya Seda komai ya lafa yafara lallashinta tare da bata hakuri dan bayin kanshi bane dan shima baisan ya akayi hakan ta kasance ba a ranshi ya qudurta tunda hakane baze sake kwana dakin Manane ba sede inhar itace ta biyoshi dakinshi(tabb zaka dade kuwa bakaga ranar nan ba ) itade jinshi kawai take amma tsanarshi data shegiyar yarinya nan take qara ruruwa a zuciyarta tun ba ma Manane ba dan ji take kamar ta kashe ta (to itako miye laifinta cikin nan?) Faruwar hakan ta k'udirta a ranta da baza ta kara bashi kanta ba sede in har itake da muradin hakan Washe garin ranar ma hakan ta kasance dan ko diner ma Manane ce tayi shi dan gujewa fadan Umma da kuma kare martabar mijinta Koda girkinta ya zagayo Rid be zo dakinta ba itama kuma bata jeba duk da bataso yaki zowa ba..ita kuwa tsoran kai kanta take.. Un mois plus tard Abubuwa diyawa sun faru ciki kuwa har da kusantowar auren Sambaby sosai suke shirye2 Manane kirjin biki se shiga da fice take du da gogan nata yana kaffa2 da ita wai saboda A.razak( inbanda kishi irin na Rid,doc A.razak din da tunni ya safe baben Manane😜) A wata ranar samedi aka daura auren Samira Bassirou tare da angon ta A.Razak Abdallah wanda da dadare ne za'ayi paty Tun bayan magrib Manane ta fara shirye2 ta ankon wani material ne sukayi dark blue dinkin doguwar rigar tayi tasha sarka da da kunne da kuma abun hannu duk blue ..ta kafa daurin diko kamar gwogworo se wani dan yalulun mayafi data yafa a kafad'a ,light make up ne tayi fitowar ta kenan sukayi kicibis da Boss dinta ,kallon up and down ya mata yace ina zaki turo dan karamin bakinta tayi tace paty mana Da izinin wa? Koda na yarje miki kike ganin zan barki ki fita da wannan shigarne? baya taja ta kalli kanta tace to miye aibun shiga ta ? Nuna ta yayi da yatsa wly in kikayi wasa ma hanaki zuwa patyn nan zanyi inba ma raini hankali ba da wannan dan mayafin zaki futa ta turo baki cike da shagwaba haba yaya kekam kacika takura ..ee dey kasan ba hidjab zansa ba ko? To idan har ba hidjab zakisa ba to kibar ma batun fita da aurena akanki kike tsammani zan barki Ki tafi paty haka duk mazan wurin suyita kallonki kike so ?to tun wuri ma koma ki saka hijab ..ya daure fuska Ba yanda ta iya dole ta koma tana bubuga kafa kamar karamar yarinya kamar tayi kuka tafida gwagwaron ta saka hijab fari ta fito yana nan tsaye inda tabarshi kallonta yayi sai yaga tamafi da kyau kicin2 da rai yayi badan yana gudu fadan Mom ba da baze barta zuwa patyn nan ba dan duk gani yake kalle mishi ita za'ayi yaja tsaki A ranshi yace wai ita yarinyar nan duk shigar da tayi sai tayi mata kyau kamar wata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41