Chapter 40
Chapter 40
ya samo goribar ya kawo mata tana ci har wani rufe idanu take ..daya tal taci ta kuma cewa d'an tama tsitsi take so........ 😧😳haba baby Mynane a ina zan samo miki shi ....... Tab walahi koma ina ne katafi ka samo min dan shi nake son sha.....ta shagwabe mishi .. Allah ya taimake shi yemine ta iya ..shima da kyar Haider ya bari tayi wai haka kawai ze saka mishi amariya a kitchen ....seda ya marerece tukon ya bari tayi..... Tare da dan waken ya kawo mata ta kuwa ci dayawa...se lokacin ya samu saukin abun.... Ranar wata subdu aka d'aura auren Wanda dubbunan jama'a suka sheda auren Haider Ismaël da amariyar shi Yesmin Mamandu ..da kuma Areef Ismaël da Muhsana A.Wahid.......anyi shagulgula anci ansha anyi barin kudi .........an kai kowace gidanta Sede muce Allah ya bada zaman lafiya da *Zuri'ar* d'ayyiba....... Angwaye kam basu dagawa amaren su kafa ba dan Haider zage wa yayi ya gurji amarcin shi duk da sun sha wuya cikin satin ko wata soyaya ce me karfi ta shiga tsaka nin su dan Yesmine ta kamu da son mijin nata duk dama can bâ wani kinshi ta keyi ba .kuma bayan satin aka kawo mata yaronta Khaleel A bangaren manya su Manane ko honey moon ya shirya musu kasar paris suka tafi daga can su fice kasa me tsarki dan sauke farali sun kwashi ruwan soyyaya seda sukayi three month suka dawo shima dan vacation ya kare da cikinta titsitsi dan har yakey wata shida ta dawo dayawa sunyi mamakin abun wanda basu san da shi ba. Dayawa sun tausaya mata saboda zama dakel tashi dakel sosai cikin yake rinjayarta ko school ma haka yake tarerayarta itako sai zuba mishi shagawaba take(um su Manane an samu abun yi dama banza2 ma shagwaba bale an samu abun yi🤪) Sosai suke burge dalibai. Cikinta nakaiwa wata tara Mom ta tattaro ta medo ta wajanta. Bayan sati ranar wata alhamis tun safe ta take jin cikinta na murd'awa ..ga kafafunta sun rike...daurewa kawai takeyi...ai kuwa cikin dare ta tashi da wani matsanan cin ciwon mara nakuda tazo mata gadan2 tun tanayi a silent har takey ga tada Mom.dayake itama ta lura da ita tun safen ganin halin da take ciki yasa ta kirayi Rid hankali tashe ya shigo dakin ganin halin da take ya sashi kara rud'ewa koda ya duba yaga har kan d'a ya fara futowa ....dole ya daure ya karb'i haihuwar dan koda sun kama hanya baza su isa ba.zata haihun........ Ba jimawa kuwa ta santalo yaron ta fari tas dashi ya cire cibi ya bekawa Mom...ta jima mahaifa bata fado ba hankalin Mom ya dad'a tashi.... Ganin tana wani nishi yasa Mom fadin wata nakudar take fa... Yace Mom ai dama yan biyu ne.. Nan suka taimaka mata da iznin Allah ta sake zankad'o yaronta namiji.....se kuwa ga mahaifa ta fad'o.....nan Mom ta gyara su ita da yaran sak ubansu tasaka turaren wuta kamshi ya gauraye dakiiii..... Washe gari gidan ya cika da yan barka ...kowa se Macha Allah ya ke Fadi.....amman duk yawan mutanen nan be hana Rid shiga da fice ba bini2 se yazoya d'auki twins seda Mom ta mishi jan ido tukon yad'an sarara shigowa dan taga rashin ta idon yayi me yawa... Ranar suna suka ci sunan Abdulrahamane da Abdulrahime....anci ansha sosai yara sukayi goshi tako ina sunsha Kaya da kyautitika ...anan mukaga yan ENSP and University na zinder suma sun kawo tasu gudunmuwar ...su Nadiya da Natasha se kwasar shoki suke.... Zuri'ar mu fans 1&2 suma sunzo da tasu gudumuwar nan mukaga Anty Mira..Aisha...Maman Shuren...Dala ...Yusuf...and so one kuna yawa . se washe Baki suke ana korawa da juce 😁....... Sede muce Allah ya raya yasa cikon addine ne..ameen Lokacin da kawarta Sam zata tafi tace to Maman yan biyu Allah yasa bad'i ya warhaka munzo wani bikin twins cike da tsokana ta fad'i haka... Bude bakin Manane se cewa tayi tab ai inaga ma nida wata haihuwar se nan da shekaru biyar inda dadi kema ki haihun mana seni ... Gaba daya dakin suka kwashe mata da dariya. ...Safara tace kada fa kiyi cika baki se kawai mu ganki da wani cikin.... Turo baki tayi ta kyale su dan taga sun meda ita birin wasansu..... *** #*** A bangaren Halima kuwa hauka turben take ta rame tayi baki fuskar nan tawani jeme babu kyan gani dole tasa yan uwanta suka kaita likitan mahaukata dan kuwa kulum abin nata kara gaba yake .....(shiyasa akace ramin mugunta ginashi bame zirfi ba dan zaka iya afkawa ciki...Allah ya shiryi masu iri wannan hali.......)ameen **** ****** *** Bayan one month twins da Mamansu sunyi b'ub'ul da su don Mom na kula dasu yanda ya kamata ga wani gyara na musaman da take yiwa Manane dan takaga taken2 Rid kwata2 yanzu bashida ta ido inde akan Manane da yaransa ne tana so ya barsu nan gidan suyi koda 3 month ne ko sa kara warwarewa tunda tana zuwa school don ta samu ta ringa tayata rainan su ........amma da alama hakan baza ta samu ba .. Yauma kamar kullum koda ya shigo ya gyada Mom dake Falo tana kallon tv se kawai ya shige dakin da Manane take .......girgiza kai kawai tayi taci gaba da kallonta Tana feeding din twins ya shigo kallo daya ta mishi ta gane yana cikin need dinta ..kwantar da Twins din tayi a bed dinsu ta dawo bisa cinyar shi tayi masauki tasa hannu ta dago fuskarshi wanda har idon shi sun canza kala ido cikin ido tace my king what happen nagan ka wani iri haka..... Dan karamin bakin ta kawai yake kallo yace My canne a sucre ina cikin kewarku sosai fa yaushe zaku dawo ne.. Dan murmushi tayi tace nan da 5 month ne kawai cike da tsokana tayi maganar ... Waro ido yayi yace kafin nan kuma an d'auki gawata ba.......ya dan kalleta yace ki taimaka yau ki barni na rage zafi wly na kasa daurewa ne... Wani iri tausayin shi taji ga azabenben sonshi dayake azalzalarta.......bata yi magana ba hakan ya bashi daman jajjagulata son ranshi....... Mom kuwa gani jima war tayi yawa yasa ta dau waya ta danna wa Manane kira gudun kada taje taji wani abun.. Lokacin kuwa Manane duk tabi ta rikirta ma Umma d'a ta na famar zautar dashi da salonn ta....seda taga ya samu nutsuwa tukon ta barshi wankan ma tare sukayi shi ..ya fito ya fice mosque ...kicibis suka yi da Mom da ta hauro sama ganin sunki daukan wayarrma..harara kawai ta sakar mishi. Shikuwa yayi dariya yana sosai kai ya fice.... Ganin Manane na saka kaya yasa tace ke kuma zauna nan kina biye mishi ya sake d'ibga miki wani ciki ga jinjirai.. Ita abun ma kunya ya bata batace komai ba sede aranta tace habade ni kaina Mom bazan yarda na sake d'aukan wani cikin nan kusa ba a yanda na ci bakar wuyar nan wajen haihuwar su ..ai sai na murmure kona dau wani... Da kyar ya bari tayi 2months yace shifa abashi matarshi... Ganin zaryar tayi yawa yasa Mom ta bashi matarsa da yaran tare da Nani data samowa Manane...sosai suke nunawa junan su soyyaya kamar su had'e junansu... Ai kuwa twins na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41