Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

Allah kuwa bayan tasha maganin se taji sauki ,,,dan har gidan tsoho me ran karfe tatafi dan yin dinner . .. Bayan an gama ne Haider yace yana da magana .kirjin Rid yaba da damm danya san maganar auren.shice ze fad'a dan besan ya zasu dauki zancen ba. .yayi gyaran murya yace dama se kuma yayi shiru dan shi kanshi besan ta ina ze fara ba , Abba yace fad'i mana .. yace dama Rid ne keson k'ara aure jika ke dak'in d'ipe kowa yayi shiru ,Manane kuwa suman zaune tayi ta kasa koda motsi se tsikawo muryar Mom da Momy sukayi suna fad'in baze ma yiyu ba ,,,duka ma yaushe yayi aure dazece wani zeyi?kwata2 wata 6 dayin aure dan walakanci yace wani ze sake yi? Umma ta capke zancen da fadin aa e ba haram bane nan fa *Zuri'ar* ta kacame kowa yana fad'in albarkacin bakin shi ..duk jikin shi yayi sanyi kamar yace ya fasa amman jin bakin shi yayi midhi nauyi , ,ita ko Manane hawaye kawai take ta sanda kai kasa... Can Elh Fayรงal yayi gyaran murya yace duk kuyi shiru zan yake hukunci , ,tsit kake ji yace to tunda de yaro yace yana so kuma yaga ze iya to babu yanda muka iya saboda addinimu ya halasta mana dan in mu hana mun toye mishi hakkin shi dan shima yayi mana biyyaya ya auri wacce muka zab'a mishi tunda yanzu ya kawo wacce yake so donmi mu zamu hana shi kada fa kuma manta An hallata ma namiji ya aure mace 1_2_3_4 idan har zeyi adalci tsakanin su ..nande yayi ta musu nasiha har zuciyar su ta karaya jikin su duk yayi sanyi suka yi fatan Alkhairi tare da zaman lafiya..akayi addu'a taro ya watse ..,,tunda suka shigo gidan su ta fashe da kuka da gudu ta shige d'aki. Duk se yaji ba dad'i koda ya shigo palon tana zaune tagama kai da guiwa tana kukan da ita kanta basan dalilin yin shi ba ,,ya iso ya zauna kusa da ita .yace Mananeee yanda yaja sunan seta ji duk yafi kowa iya fad'in sunna ..bata amsa ba amman ta tseda kukan da take ,ya d'ago ta yace kiyi hakurin kinji bawai dan na muzguna miki ko na walakantaki ne yasa ni zan kara aure ,,kawai Allah de ya kaddaro ne nan yayi ta lallashin ta ya rungumeta suduka se da sukaji wani masse(shock) ya fiddo tissu ya goge mata hawaye dan baya san kukan ta tun tana karama koba komi kanwarsa ce (๐Ÿ˜balle ma da komin ba)suna haka har ta dena kukan can tace to yaya damin yanzu ka daina cin abinci na ?yayi murmushi yace ayya yanzu aiki ne yake mun yawa a office..bata ce komi ba sun jima a haka tukon yace dare yayi taje ta kwanta seda ya rakata bakin d'akinta tukon yayi nashi d'akin ,,wanka tayi ta d'auro alwala ta fara jero nafilfili dan duk abinda zezo ya zo mata da sauk'i .. shiko bayan yayi wanka yayi shafa'i da wutri har ze kwanta se kuma ya tashi ya nufi dakin ta . .tana yin sallah ya iskota har ranshi yaji dadin ganin ta tana nafila ,,ya kwanta bisa gadan ,har bacci ya dauke cshi bata gama ba.se 1 da rabi ta kare ta kwanta can karchen gado tana dari2 har itama bacci ya dauke ta ..kiran sallar farko ta bud'e ido amman se ta jita a jikin mutum a rumgume ta zaro ido ta kalli faskar shi amman dhi bacci yake hankali kwance shiya bata damar kare mishi kallo tana ayyana abubuwa daya wa a zuciyar ta d'an karamin bakin shi shiya fi daukar hankalin ta har bata sa sanda ta kai hannu ta ba motsin daya yine ta dawo hayyacin ta da sauri ta rufe ido ,koda ya bude ido shima kallon ta ya tsayayi ya ayyana abubu a ranshi haka yaci gaba da kallonta shi be tashi ba koma be koma bacci ba ita ma Allah Allah take ya tashi ,se da yaji ana Assallatu Khairan Minalyaum tukon fa ya raba jikinshi da nata ya fice dakinshi.. . Yana fita itama ta fada douche (tolet) tayi alwala koda ya dawo har ze shiga ya ta da'ita se yaji tana karatun Alkur'ani dama haka ya zata ya shige dakinshi.... kamar kullum ta gyaran dakunan tayi break tayi fice warta shima ya tafi clinik dan sunada rรฉunion (meeting) A kwana biyun yar shakuwa ta shiga tsakanin su dan kusan kulum d'aki daya suke kwana duk da abinda.ke shiga tsakanin su se satar kalon junan su in dayan yane bacci danshi Rid har yanzu renonta yakeyi yana mata kollon yarinya ....(mukuwa muka ce MACE BATA KAD'AN ,...koba haka ba Fans๐Ÿ˜‰?) Ku biyo mu danjin yanda zata kaya ..shin Rid zema Manane kishiya?ko kuwa yaya de? Kuyi hakurin na rashin gani typing kwana biyu ai yukane suka mana ๐Ÿ™ Mune naku har kulum Fasma&Aรฏcha [27/1 21:04] โคFasma&Aรฏchaโค: ๐Ÿ’“๐Ÿ’ž๐Ÿ‘ช๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ’•๐Ÿ’ž Story&written by ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช ~Aรฏcha~ and ~Fasma~ ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช *Jameeda munga sak'on ki mun gode insha Allah zamu gyara Allah ya bar zumunci Ameen๐Ÿ™๐Ÿ™* Wannan page din nakine kekad'e Jameeda 75__80 2weeks later Soyyaya me karfice ta shiga tsakanin Doc Rid da Halima ., Yauma kamar kullum direct daga office gidan su Halima ya nufa .... Koda yazo ya kusan minti 30 a tsaye a tsakar gidansu tunkon tafito fuskar nan a tamke ta fito bayan gaisuwa bata kara yin wata magana ba , Nan danan Rid ya rude duk yabi ya rikice se tambayarta mike faruwa yake ..gaba d'aya ya susuce yana rok'onta tagaya mishi dan jiyake kamar yayi kuka dan yanzu ba abunda ya tsana kamar b'acin ranta(humm wannan aikin Boka ne) da kyar tace dashi ba kai bane har yanzu baka turo gidan muba gashi yanzu har 2weeks da ka cemin kafad'a a gida amman ji kake shiru ta k'ara murtuk'e fuska ,, ya sassauta murya yace ''mon amour''(my love) ni kaina na matsu ayi auren nan amman kada ki d'aga hankalin ki yau ba se gobe ba dana koma zan sake sanar musu Saboda irin wanna kulawar da kike nunamin nasan bayan auren se tafi haka... .se a lokacin ta saki fuskarta ta jujuya kwayar idanunta tace sosai ma my one , Hakade sukaci gaba da hirar su ta masoya se biyar 5 na yamma yamata sallama ya fice dayake yau week-end ne ba school... A kofar gidan Abba sukayi kicibis da Haider da fara'arsa yace yawwa daman ina san magana da kai ,, to mushiga cikin gidan mana ...a'a se urgently nan ma yayi kuma inaga daga nanma gaba zamuyi to Allah de yasa lfy... eee to ita takawo hakan ma to ina sauraronka Daman maganar aurena da my love ne dan so nake karakan wurin Papy(Elh Fayรงal) muji a ina muka kwana gameda zancen auren dan wly na matsu ayi auren nan Yayi tsaki da akan wannan ne ka tsayar dani ,wai anya ma kanka d'aya ,ni yanzu ta lafiyar matata nike kabari ad'an kwana biyu hankalina ya dawo jikina .. Ayya to Allah ya bata lafiya ,,amman yanzu bazan iya jiranka har wajen two days ba kawai mutafi ka rakan .. Wai kai mike shirin samunka ne ? Yaushe ma

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41