Chapter 31
Chapter 31
da su ya dena zuwa gidan Papy kai da duk sauran gidajen ma ....da Manane kuwa wasan b'uya sukeyi dan gani goma ze mata to seya ci zarafinta so goman...sosai Zuri'ar ta shiga wani yanayi...Addu'a kawai suke mishi dan ko sunan daya daga cikin Zuri'ar yaji se kanshi ya fara juyawa..... Halima kam se gasa mishi aya a hannu take ...gashi ba wani girki take mishi ba bare ayi zancen ta kula dashi baya zuwa office kullum yana gida ..duk ya bi ya rame kowa ya ganshi yanzu se ya tausaya mishi ba kamar Manane ba.... Mom ...Umma da Manane sosai suka duk'ufa wajen kaiwa Ubangiji kukansu..... Yauma kamar kullum Mom ta sallamo gidan dan gani lafiya itama. Manane ta d'auke musu k'afa kwana biyu....kuma in ankirata a waya ma bata d'auka..... Se da tayi salama tafi sau biyar amman ba'a amsa mata ba ...tura kofar palon tayi ta shiga ...ai kuwa se ganin Halima da Rid tayi suna falon suna kallon tv abunsu... Daka musu tsawa tayi kan sunaji tana sallama amma sunki amsawa..... Shikam Rid kicin2 da fuska yayi bece komi ba.. Bud'ar bakin Halima se cewa tayi yo ba muga damar ansawa bane ...wai ma miya kawoki gidan nan...? Daga bayanta taji ance ...... Kuyi hakuri kuyi manage da wannan... Muje zuwa .fans. Fasma&AΓ―cha [9/2 15:05] πππͺπ¨βπ©βπ§βπ¦π¨βπ§βπ¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) π¨βπ©βπ§π¨βπ©βπ§βπ§π©βπ§βπ¦ππ Story&written by π³πͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ π³πͺ _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ 130__135 ```Manzon Allah (SAW) ya ce:''ku kiyayi zato.lallai shi zato shi ne mafi karyar zance'' Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` Daga bayanta taji ance Ubanki tazoyi gidan marar kunya kawai... Juyawar da za tayi se kawai taga Manane se zabga mata harara take ashe tun lokacin da taji muryar Mom tafito .... Da gudu Manane ta zagayo ta rungume Mom tana fadin welcom my sweetMom .....ta kamota suka karaso Palon ta kuwa cike mata gabanta da kayan motsa baki suka dan tab'a fira ...bata wani jima ba ta mike zata koma gida.... Bude bakin da Halima za tayi kawai tayi tsoki tace an dey ji kunya kina uwar miji amma kina bin gidan ya'yanki A fusace Manane ta mike tsaye har bata san lokacin da ta isa wurinta ta bige mata baki har sai da jini ya zubo tace kema gidan d'anta kikace dan haka tana da dama da ikon zuwa lokacin da taga dama tayi kuma abunda taga dama banza sha3 mai kama da angulu... Dafe baki tayi tace ni zaki fasawa baki .... Ee an fasad'in inda akwai abinda zakiyi kiyi .. An fada din yo ba abin kunyar tayi bane.. Ai Manane batasan sanda ta kwasheta da mari ta medota tace in uwarki ce zaki ce tayi abin kunya neh ....sakara marar tunani.. Dakata yarinya ya isheki haka.ta d'aga hannu da niyyar ramawa.... Tsawa ya daka musu yace in hayaniya zakuyi ku tafi can waje kuyi abunku bana san damu kallo nike. Mom da Manane sukayi shaaa da baki suna kallonshi Manane ce tayi k'arfin halin yi mishi magana tace kai yanzu Ridwan kana kallo wannan shegiyar matar taka tana yiwa Mom rashin kunya amman kayi shiru? da farko jikinshi yayi sanyi yana son bada hakuri amma bakinshi yayi mishi nauyi sai kawai tsintar bakinshi yayi da fadin to mi ruwana ciki kuma ai ita takawo kanta har a kayimata rashin kunyar. itako Mom abun ya matukar bata mamaki sai kawai wasu hawaye masu zafi suka zubomata a ranta tace wai Ridwan ne mai ladabi da biya wanda ko magana wahala take mishi shine yau yake fadin wannan maganar lalle da walakin goro a miya . Cikin ido Manane takale shi ta nuna shi da d'an yatsa tace amma wly kai kunyarka ragagace har ka kalli Mom ka gaya mata wanan maganar .. A fusace ya tashi yana fadin ke har kin isa ki nuna ni da dan yatsa . . Itako tace an nuna kan ko da abunda zakayi ne. Hannu ya daga da niyyar marinta.. carab Mom tarike hannun shi tace kul kada inji kada na gani Juyo wa yayi da niyyar yin magana sai yaga tayi mishi kwarjini sai kawai ya fice dakinshi yana huci. Halima ko shewa tayi tare da wata irin dariya tayi dakinta. Manane kuwa fad'awa jikin Mom tayi ta fashe da kuka.. rarashin ta tashiga yi tare da bata hakuri tace barni da shi .zezo ya sameni ne... Da sauri tace da Allah Mom kada kiyi fushi dashi dan ba laifinshi bane inada yakinin da sa hannun Halima cikin al'amarin nan. Nan ta kwashe ta gayamata duk abinda tagani da kuma taji Halima tayi..waccar ranar... Jum tayi tace tun da ko hakane zamu duk'ufa da kaiwa Allah kukan mu.... Tayi mata sallama ta fice... ** *** One month later Yesmine ce da Muhsana zaune suna hira wani asstement sunyi zurfi.. se kawai wayar Muhsana tayi kara... Tun kafin ta daga ta fara murmushi tana d'agawa takuwa wani kara kashe murya tana murmushi tafi minti goma tana wayar sannan ta katse... mi Yesmine zatayi in ba dariya ba tace wakika samu haka kike kashemishi murya kode kode.... Dariyar itama tayi tace lΓ bawani bane ba fah yaya Areef ne kuma kusan kulun sai yakirayeni mun gaisa .. Ummm su gaisawa manya shine ni baya kirana kawai akwai wata a k'asa.. . Da kuwa kin sani kullum sai yace na gaishe ki...kuma babu komi a kasan .ehe. Kude kuka sani da gulmarku.intayi wari maji *********** Bari muleko b'angaren su Manane .. zauna suke a cafetaria suna hira Manane sai tsokanar Sambaby take tana fadin uhmm su kawa har an kunso abun daga shigarki har kin samo ciki. Dariya tayi tace zauna dey nan kin tsaya sanya... suna cikin haka sai ga wata yar classmate d'insu tashigo ta zauna kusa da Sam tace way kunji wata sabuwa? Wani labari kika zo mana da shi dayake kullum kina da shi. Wai fa lecture d'in ''dΓ©ontologie'' ne fa yace yau da yamma zai anshi assitement din daya bada ...... Sambaby tace Allah yasoni nakawo nawa Ke fah Manane. Wly nayishi amma na baroshi gida dole na koma kenan tattara kayan ta tayi ta fice tace sai nadawo fad'ar Manane kenan.. Dede shiga palon taji muryar Halima na fad'in ai wly kad'an ma suka gani... Cak ta tsaya jin Halima tacigaba da cewa sai naraba shi da kaf *Zuri'ar* tashi ke inaga ma d'auke shi zanyi da ga unguwar dan har yau in na tuna kallan manshi na wai shi bayada sha'awar k'ara aure kuma koda ma zai yi saide ya zab'a a cikin *Zuri'ar* su kuma wai dan karewar wulakanci bana cikin tsarin matan daya ke so... Har yau zuciya ta zafi take idan na tuna... Shek'ewa kawarta tayi da dariya tace ai ki godewa boka gobe da nisa da yayi surkullen had'a auren ku da kuma turo mishi aljani dan kundalo dan rabashi da _Zuri'ar_ dayake takama da ita ai kuwa kinga kin dau fansa a kanshi..tunda yanzu ko zuwa gidansu bayayi...sake shekewa da wata dariya sukayi suka tafa. Dam gaban Manane ya tsinke tace boka? Aljani? Inalilahi....... Danne zuciyarta tayi ta tura kofar tare da sallama bata jirayi amsawar suba tayi shigewarta daki. Sukuwa da harara suka bita tare da tab'e baki.. Kaya ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41