Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kuka fara soyyayar da har zakayi zancen auren kabari ku k'ara fahimtar junanku mana.. Kai tsaya nifa akan auren nan zan iya yin f'ada da koma waye ..fahimtar juna na nawa ?wly zamu iya batawa da kowa(๐Ÿ˜ณda kowa fa kace Rid ..tab illale Boka yayi aiki .anya kuwa๐Ÿค”?)idanma baka sona da itane to zan raba kayana da kai , Kai duk Wanda ma baya son auren nan to yaja baya dan damasu so za'ayi, Tunda yafara magana ya saki baki yana kallonshi a ranshi yana ayyana anya wannan Rid ne kuwa ?dan tuncen da yan mata basu dame shiba amman gashi yanzu har yana fad'a akan mace ...dayaga abun bana karewa bane dan se fad'a yake .se yace yi hakuri d'an uwa nima ba ina k'in auren bane nagani de yaushema kuka had'u ,kuma dukama 6months(6mois)dayin aurenka da Manane har kake zancen wani aman tunda abun naka yakai har haka muje na rakaka ,se lokaci ya saki fuska yana dariya yace yawwa ko kaifa brother haka suka fice gidan Papyn Shide Haidar kallonshi kawai yake yana mamakin canzawar shi a y'an kwanakin nan... .Sun iskeshi bisa sallaya da tazbaha a hannun shi suka zauna bayan sun gaisheshi se kuma sukayi shiru yyii dariya yace to ku fad'i abunda ke tafe daku kunzo kun sakani gaba kun tsare ni da idanu kamar wanda naci bashin ku ban biyaba cikeda tsokana yake maganar . Carap Rid ya karb'e zancen da fadin ai kaci bashin mu da dadewa shine mukazo mutuna ma idan ka manta... ya gyara zama yace ina sauraren ku .. bako kunya Rid yace zancen aurena ne naga har yau ba'ayi zancen ba gashi har kusan two week dayin maganar A lokaci guda Elh Faycal da Haidar suka kalli juna suka meda duban su zuwa Rid wanda bema san sunayi ba yanata fadin maganganu.. gani shirmen nashi yafara yin yawa dan har yafara fadin duk wanda yake kin auren nan to nima zan iya yanke alakata dashi,maganganu dai iri2 ,Elh Faycal yace ya isa haka ka kwantar da hankalin ka zanyiwa mahaifan naku bayani sai aje a tambayo maka da fara'a yatashi yana fadin yawwa Papyna amma fa karya huce satin nan yafice warshi danshi yama manta tare da Haidar suka zo. Bayan fitar shi Papy ya kalli Haidar yace mike damun dan uwanka gaba daya ya susuce akan auren nan wly ni kaina abun ya dauren kai dan 2 days d'in nan bashida aiki sena zancen auren .. to Allah ya kyauta ya zab'a abunda yafi alheri..ameen yatashi dan anfara kiraye2 sallah magrib..... Bayan dรฎner Elh Faycal ya tuna musu da zancen auren sannan yace dasu Abba su shirya ranan alhamis nan da kwana biyar kenan suje tambayar auren .. Adam yace wai daman ba'abar zancen auren nanba? Nan fa Rid ya watso mishi harara yana maganganu kasa2, wanda duka *zuri'ar* seda tayi mamaki dan ba halinshi bane dan haka kowa yaja bakinshi yafara mishi fatan Allah sanya alheiri banda Mom da Momy da suke banka mishi harara..... Manane ko tunda Elh Faycal yafara magana zuciyarta take mata lugude kwalla har tacika mata ido(wayoo Manane ๐Ÿ˜”) ,haka aka watse kawa da abinda yake ayyanawa a cikin ranshi. Ranar Manane kusan kwana tayi batayi bacci ba sai kuka da tayi2 ,ita kanta tana mamakin kuka da take dan bata san dalilin yinshi ba kawai de ta tsinci kanta dayin shi ga wani abu dayake zowa ya tokare mata ma k'oshi(to kode kishi kike Manane?๐Ÿ˜ณ tab) Sekusan uku na dare b'arawon bacci ya saceta. Koda yatashi da asuba bai ganta a dakin ba seya ficewarshi dan yayi tsamanin tana douche (toilet) seda yafito yayi turus ganinta nan palon bisa kujera daga gani batajin dadin bacci a ranshi yace bade anan ta kwanaba?ya matso ya tsuguna agabanta yana kallonta har cikin ranshi yana tausayawa yar kanwar tashi to bayanda ya'iyane dan jiyake inbe aure Halima ba tofa ze'iya mutuwa ma...ya jima nan zaune yana kallonta yana saka da warwara seda yaji har ana shiri shiga sallah sanan ya tashi ya shiga dakinshi karan rufe kofarne ya tada Manane. Idanunta duk sun kumbura tayi ficewartar itama . Da safe da matsanecin ciwon kai ta tashi sama2 tayi gyaran gidan tayi musu break koci batayi ba ta koma ta kwanta dan bata jin zata iya zuwa school yau ... .lokacinda ze fita ya leko dakinta dan bata fito yin break ba ganin har 8 ta kusa..ya tadata yatambaye ta bata zuwa school ne..? Tace a'a yau ba muda lecture. kai kawai ya gyada ya fita tabi bayan shi da harara sanan ta meda kanta tacigaba da bacci ta.. Sai karfe sha daya ta bude ido wanka kawai tayi break d'inma sama2 tayi shi dan batada appรฉtit tayi ficewarta gidan Umma tun kafin ta zauna Umma ta lura da idanunta sun yi luhu2 alamun tasha kuka kenan a sanyaye ta gaishe ta itama Umma duk jikinta yayi sanyi tace yau ba school ne? Akwai kawai de bana jin dadin jikina ne har cikin ranta tana tausayawa yar tata dan kaf cikin *zuri'ar* ita kade ce za'ama kishiya gata yarinya yar kankanuwa,ita kanta Umma tana nuna halin ko'inkula ne dan Mom da Momy suna mata kara shima kuma Rid yana mata biyyaya kamar ita ta haifeshi .shiya sa take kauda kai ...ta jima tana yima Manane nasiha tunbata ce komi ba harta fara kuka .. tsakanin d'a da uwa se Allah dan haka se ta janyo ta jikinta ta tana lallashin ta tare dayi mata nasiha dajan hankali cike da dabara da wayo take mata nasihar kan hakuri,akan zaman duniya dakuma tazauna da kishiyarta lafiya.. kuma idan akwai abinda bata fahimta azamantakewar auren to kada ta boye ta sanar mata ko kuma to ta gayama Mom dinta,nan danan taji zuciyarta wasai ta rage zogin datake mata . .Allah sarki Manane.. , daga nanma gidan Momy ta nufa a nan ta wuni se wajejen biyar na yamma ta koma gidanta........... Muje zuwa fans.. Muna neman afuwarku akan rashin jinmu kwana biyu ayyukane sukamana yawa ga school ta sankomu gaba muna barar addu'ar ku๐Ÿ™๐Ÿ˜˜ love you allโคโค Samira mun gode da kaunar da kike nuna mana Allah yabar kauna.๐Ÿ˜ Fasma&Aรฏcha [27/1 21:04] โคFasma&Aรฏchaโค: ๐Ÿ’“๐Ÿ’ž๐Ÿ‘ช๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ’•๐Ÿ’ž Story&written by ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช ~Aรฏcha~ and ~Fasma~ ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช _Dedicated_ _to_ _Ramatou 80__85 Da zuwanta ko minti goma batayi ba kawarta Sambaby tazo nan fa suka fara murnar ganin junansu ,,tacika mata gabanta da kayan ciye2 bayan sun d'an tab'a hira sambaby tace wai miya hanaki zowa school yau ne? Tace bani da lafiya ne.... ayya kode har mun samu baby ne ?ta fada cike da tsokana ... ta buga mata harara wani baby?kawai de head pain(maux de tรชte) ne ,, to Allah ya baki lafiya... Ameen.... To ciwon kan ne ya haddasa miki damuwa? damuwa kuma ?nibani da wata damuwa.. haba Manane kadafa kimanta na sanki farin sani gashi har wata yar rama kikayi amma kice min bakida damuwa... Taja ajiyar zuciya tace hakane sam bakomi ke haddasa min wannan damuwar face qarin auren da ya Rid ke shirin yi ..dan nanda 5days za'atafi yin tambaya ma Sam ta dafe kirji tace ๐Ÿ˜ณwai da gaske ne ko wasa? Hum kede bari ai ba'awasa da irin wannan maganar ....kuma

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41