Chapter 19
Chapter 19
kinma san wacce ze aura? Aa ina zan sani. Ina wannan yar lukutar da muka ji ranarnan suna firarshi? Kada de Halima wacce take aji na 3?marar kyan nan ? Ee itafa. Tab to walahi da wata a qasa,.... Kamar yafa? Ke bakiji abunda suke fad'a ranar bane? Naji amman fa kin san zargi ba kyau ,.. Hakane to Allah ya shige mana gaba Ameen thouma amin.. To Manane meze hana ki bari nasakaki groups din nan dana miki zancensu kwanaki dan wly akwaiabubuwau qaruwa ciki da kuma novels da ake turowa ki bari nasakaki kodan qaruwar kanki.. kuma zaki qara sanin yanda zaki kara kula da gidanki ..iya tattalin miji da iya kissa dade sauransu... Okk sambaby ki tura number na se asakani ciki.. Suna cikin haka wayar Sam tayi kara . Tunda ta dauka take wani kashe murya se wani shagwab'a take Manane ta saki baki da hanci tana kallonta Takusa ten minute sanan ta kashe Manane takai mata dundu tana fadin wanan kashe muryar fa? Ta kauce tana dariya bafa wani bane Doc ARazak ne.. A'a kawas ina tayaki murna dan kiyi dacen miji.. Ke befa furta yana sona ba kawai de muna d'an gaisawa ne .. Ana kan hanya kenan..to Allah ya tabbatar mana da abunda yafi alheri.. Kasa2 tace Ameen Mi Manane zatayi inba dariya ba .. Sun sha firar su har kusan magrib sannan tamata sallama .. (π€tofa fans kunji inda Doc A.Razak ya dawo..?) Ranar alhamis su Abba suka tafi gidan su Halima ..a kuma basu basu dan har sunbada sadaki kuma ansa ranar aure nan da 1 month(1mois).. Yana zaune a office Haider ya shigo yake sanar mishi ansa ranar auren nan da 1month ... Nanfa Rid yafara fada akan mi za asa har wata daya ina laifin 2 or 3 weeks danni har na fara shirye2 na , Shikam Haidar kallonshi kawai yake dan yanzu abun na Rid tsoro yake bashi..har ya qari bambamin shi bece dashi komi ba... Haka Rid yake ta shirye2 event din daza'ayi dan Halima tace auren kece raini za'ayi.aure na gani na fada saboda event ma wajen kala biyar za'ayi ..paty ne nacikon na shida ... Yau sauran 1 week sosai Rid da Haider ke shirye2 ba akama hannun yaro , duk da Haider yana kauda kanshi kan wasu abun saboda Manane ga kuma kashe kudin da Rid keyi.. Haka cikin *Zuri'ar* ma suna shirye2 aman bame daukin auren dama2 Umma .. Halima anata bangaren se tatsar Rid take yana bata kudi.. Adam da Haider zaune suna tattaunawa game da irin kashe da b'arin kudin da Rid keyi dan har ya fara taba account din _Zuri'ar_Wanda duk qarchen wata kowa ke kawo contribution ..sega Rid yazo ze giftasu Adam ne ya kirawoshi.. Bayan ya zauna Adam ya kalleshi yace wai Rid mikakeyi haka da kudi yanzu ace har ka fara taba account din *Zuri'ar* gashi yanzu har su Abba suna tambaya .. Yayi dariya yace wly kawai event ne sekuma gidan danake ginawa my love acan unguwar ''city''dan har na kusan gamawa..dan my love tace bazata zauna a unguwar nanba. Suka zaro idanu waje atare suke fadin 'gini fa kace?' Haider zeyi magana .. sekuma maganar Dad ta katse shi yana fadin to baku isaba daga kai har ita.dan ka raina mutane banda cin fuska dakama dauther na kuma yar uwaka hadda wani ginin gida ka tsira awata unguwar?to wly bari kaji idan de har bazaka had'asu gida guda ba ,ko kuma ka gina mata wani gidan a unguwar nan tunda akwai filaye ..imba haka ba sena sasab'a maka shasha wanda besan ciwon kashi ba..tunda ka taso waka gani ya ware awata unguwar ?se kai?..seda Dad ya wankeshi tatas sanan yayi gaba abunshi .. Ya Adam da Haider suketa ba Dad hakuri ..shiko gogon yayi shiru amman zuciyar nan tashi se tafarfasa take... Manane ma de ba abarta a baya ba wajen gyaran kanta dan sanadiyar group's whatsapp da take tana qara koyon girke2 sanan se yanzu take qara fahimtar manufa dama mahimmacin abubuwan dasu momy kebata ,,saboda a baya idan de bame zaki bane ko me madara da zuma tofa bata ma kallan su bare tasha ko kuma ta faki idonsu ta zubar ,Wanda ko ake aiko mata har gida to a drower take aje su dan ita bataga anfanin suba tunda ita nata miji har yau yana mata kallon yarinya .... Dadinta guda tana zuwa school sekuma whatsapp dake debe mata kewa dan yanzu har novels take karantawa ,,,sosai take qaruwa da abubuwa da dama barema wajen girke2 dan pratical takeyi.... Ana saura kwana uku daurin aure AREEF ya diro kasar dan ya gama karatunshi na zama cikkebken soja' wato _colonel_ '' ,sosai kowa yayi murnar dawowarshi (idan baku manta ba Areef qanene ga Haider ) Biki ya kankama se shige da fice ake ,,dan har anyi wa amarya jere ,an shirya mata dakinta .. Manane ma Dad ya sake mata kayan daki duk da bawani tsufa sukayi ba .... Gidan yana dauke da baban palo se kitchen da toilet se daki daya kusa da kitchen anan veranda ....sanan in aka hau stair akwai wanin dan matsakecin palo se wani coridor wanda ze sadaka da dakuna gudan 3 jere ..dan haka se suka saka Rid a tsakiya inda kowani daki ke dauke da palo da kurya se toilet...,, Ba karamar drama akayi ba tsakani Rid da Halima kafin ta amince zata zauna gida daya da Manane.. Rid ne zaune gaban Mom tana mishi fadan kan kayan fadar kishiya dabe yi wa Manane ba kuma da alamu bashida niyyaryi..sosai Mom ke fada tukon daga baya ta shiga yi mishi nasiha dakuma ya kwatanta adalci.. Ba yanda ya iya haka ya shiryawa Manane kayan masu kyau da tsada sede be kai na Halima yawa ba..... ''Ranar aure'' Ranae wata juma'a ne aka diaura auren Ridwan tare da amaryarsa Halimatu ,ba laifi anyi taro Rid se murna yake baki nan har kunne ..anci ansha ,anyi barin kudi.. Bayan magrib aka kai bride gidan mijinta.., Sun isko Momy Safara da salma se kuma uwar gida Manane ..sun musu tarba ta kirki.bayan sun gaisa sanan yan uwan Halima suka damka amanar ta a hannun uwar gidanta Manane,,, Sosai aka musu fada da nasiha . .daga karshe Momy tace suyi musabaha,kowacce seda ta danne kishinta tukon ta iya meqa hannu.. Ba kamar Halima ba da tunda ta shigo take kallonta a ranta tace wly da sake daman haka Manane keda shegen kyau kamar watar aljana? Tofa fans kunji Halima da kafin hali..ta isko Manane cikin gidanta aman tana fadin da sake....mitake nufi da hakanπ€? Ku biyo mu danji yanda zata kaya... Love you allβ€π Fasma&AΓ―cha [27/1 21:04] β€Fasma&AΓ―chaβ€: πππͺπ¨βπ©βπ§βπ¦π¨βπ§βπ¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) π¨βπ©βπ§π¨βπ©βπ§βπ§π©βπ§βπ¦ππ Story&written by π³πͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ π³πͺ *Ya Yusuf ,MH Dala,, *Khairat* *Asiya Usman da* *Kuma *Aicha muna godiya* *da soyyayar ku garemu Allah ya qara dankon Zumunci...wannan page din nakune* love you allπβ€π _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ 85__90 Wajejan takwas na dare aka fara shirin zuwa patyn dan karfe tara za'a fara sannan babu African time.. Bayanda su Safara basuyi da Manane ba kan ta halarci patyn amman se ta bige da bata jin dadi itako bakomi ne ya hanata zuwan illa Kishi ,,dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41