Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fito harabar gidan babu kowa duk an watse se wata farar mota kirar CAMRY fara an mata ado da fulawa da kuma ballon(bata)jajaye ,dan ita ta tsaya gyaira kwalliya saboda hawayen da tayi ,koda ta iso kusan motar se ta tsaya Salma ta fito daga gidan gaba ta bud'e mata gidan baya tana murmushi tare da fad'in wannan d'auka wanka haka,ai se kisa Docteur susucewa,ita de batayi magana ba illa b'ata fuska da zub'ura baki da tayi kana ta shiga ta zauna , wani dadaden kamshi ne ya daki hancin ta wanda yayi sanadiyar d'ago kanta ,Karap suka had'a ido dan shima kamshi turarenta ne ya Sanyashi jiyowa ya kalleta lokacin da idon su ya sarke cikin juna DAM kirjinsu ya bada kuma sun kasa dauke idon su,se itace ta janye nata idon ta sanda kai dan wani kwarjini ya mata yau d'in.c'en kasa kasan mak'ochi ta furta i..🙄 To muma bari mu d'an futa kafin nan😁😎 Je vous aime tous🙏❤ Fasma&Aïcha [27/1 21:04] ❤Fasma&Aïcha❤: 💓💞👪👨‍👩‍👧‍👦👨‍👧‍👦 *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) 👨‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧👩‍👧‍👦💕💞 Story&written by 🇳🇪 ~Aïcha~ and ~Fasma~ 🇳🇪 *Anty Nafissa,Kadija samba,Fanta ,dakuma,Mariama* *munga sakon ku mun gode da kulawarku Allah yabar zumunci* 🙏🙏 _Dedicated_ _To_ _all_ _students_ _of_ ```ENSP``` _and_ ```University``` _de_ ~Zinder~ 35---40 Cen karkashi makoshinta ta furta Bonsoir(g.evening) yaya shima can kasa2n ya amsa da bonsoir ,daga haka babu Wanda ya sakeyin magana se Haider da matarshi da suke ta tsokanar su ,,koda suka iso suka firfito suka kama hanyar shiga hall d'in Wanda cike yake da mutane da Sauri Haider ya matso ya mishi rad'a akunne dayake a bayan su suke se yajuyo ya buga mishi harara daga bisani kuma yaja tsuka ,ya juwo ya sakalo hannuchi cikin na Manane da Sauri ta kalle shi zata yi magana amman se taga fuskar nan a murke dan haka tawha jinni jikinta ta kyale ita se asannan ma ta lura da couleur (color)d'in kayansu iri d'aya ne sede shi shadda farace tasha aikin hannu se meko take,ya kafa fula ja da kuma takalmi ja shima ,a ranta tace ashe ya Rid beyda laifi dan kayan nan sun haskashi(hum Manane duba da kyau de dan ba kayan bane suka fiddo shi cqn daman shi me kyaune),, Shima cikin ranshi fad'i Yake ashe yarinyar nan tanada Kyau Masha Allah se de karancin shekarun ta(hum🙄kwade ji da gulmar ku),tun shigowasu DJ ya saki kid'a ,bayan sun zauna ,Safara ta matso tace wow wai kun ganku kuwa ?gaskiya shigarnan tayi muku kyau ,dan wannan ''idée'' d'in ya Adam ce,, Sambaby ta matso itama tana fad'in ashe da gaskiyar mutane da suke fad'in kuna kama sosai nima se yau na k'ara gaskatawa, habawa eh..kuwa Manane se tafara turo baki cike da shagwab'a wanda ta zame mata jiki take fad'in haba sambaby ina kama anan ni wly na fishi kyau.. shiko tsayawa yayi yana kallonta.... bayan jawabe2 DJ ya buk'aci ce su dasu tashi su nan taka rawa, suka fito tsakar hall d'in suduka de a tsaye suke se d'an d'aga kafa dasuke,yen uwa da abokan arzuki se kari suke musu ,cqn Sega A.Razak ma yazo yana musu kari yana kuma musu fatan alkhairi tare da fatan samun zaman lfy ,ita ko tunda ya iso take murmushi ,ganni haka yasa Rid bata fuska ,se kawai ya jata suka koma wurin zamansu har aka tashi amman fuskar nan tumau(umm Doc Rid manya).. Dayake dagan nan za'a huce da ita gidan ta dan haka bayan antashi daga patyn Motar su Momy aka sakata ,a hanya suka k'ara yimata nasiha ,itakam banda kuka ba abunda take ,da suka iso cikin gidan suka sata fitowa da kafar dama ,tare dayin addu'a ,haka suka Sakata har d'akinta Sannan suka barota tanata kuka,su Sambaby ma tafiyar su sukayi dan har 23h ta fice,.. Shima be shigo ba se wajejan 23h40,koda ya shigo gidan ko takanta bebi ba ya shige d'akin shi ,bayan yayi wanka ya d'auro alwala yayi sallolin shi.ya sanya kayan baccishi.har ze kwanta se kuma ya ga rashin dacewar hakan danko bâ komi k'anwarsa ce gâta kuma yarinya..dan haka se ya fito ya nufi d'akin nata''',a sa grande surprise'(to his surprise) tana kuka har lokacin ya girgiza kai ya iso kusa da ita yace Manane, tad'ago ta kalleshi ,yace kukan mikikeyi ne haka? tace babu komi, ya kuma cewa 'as tu faim?,' (kina jin yunwa? )ne , tace a'a ,OK to jeki kwanta kibar kukan nan haka dan kada yasa miki ciwon kai,tace to yatashi yana fad'in bonne nuit (good night),yana fita ta tashi tayi wakan tayi alwala bayan ta ida Sallah ta hau gado ta kwanta ,nanda nan bacci ya sureta,...,,, Asuba alheri Manane... Kiran sallar farko ta bud'e idonta..ta shiga toilette ta d'auro alwala tayi nafilfili ta zauna tana azkar bayan anyi asaltu ta gabatar da raka'atanul fajar,bayan anyi Kiran sallah ,tayi sallah asuba sannan ta Budé Alkur'ani me Girma ta fara karantawa.. koda ya dawo daga masallaci d'akin ta ya nufa dan tayar da ita amman tun a kofar yaji sautin muryarta tana karatu .nan ya shagala da sauraranta dan karatun cike da nutsuwa da tajwidi take yin shi tare daba kowani harafi hak'inshi ,,se wajejan 6h30 ta rufe takoma gado dan wani bacci me nauyi ne a idonta... Bugon kofar palon,da akeyi ne ya farkar da' ita koda ta bude Yesmine da Mushana ne da kalolin abinci sukace inji Mom.ta amsa tace kushigo ku zauna bari na shiga nayi wanka, hayaniya da karan TV ne ya tasheshi daga baccin yayi tsaki ya tashi ya shiga wanka, da ya fito yayi yan shafe 2 shi ya saka wata shadda ‹'cendre'' (ruwan toka) y'a fito ya isko su Yesmine a palon suka gaishe shi ya amsa. Ya hanhanga yaga bata palon se ya shiga dakin nata, karan ruwa yaji a toilette din tabbacin tana wanka kenan, se ya aje wani abu abisa gadan ya fita, koda ta shirya ciki wata atampa rose(pink) ta futo suka yi break bayan ta gaisheshi ya amsa , Daya kare se ya futa dan akwai abokanen su na américa,kuma yau zasu koma ,dan baka yatafi yi musu godiya da kuma salama,, da fitarshi ba jimawa Safara ta shigo suka gaisa tace Manane Rid be baki wata kyauta yanzu ba ? Kyauta kuma !?? Tami ? Tace tashi mu shiga ciki suna shiga ta sake tambayar kyautar miye wai ? Ita Safara se daga filo take tana fadin ai aladar kasar wanan ce, washe garin aure ango yayiwa amariya kyauta idan har ta fita kumya..... Aranta tace yoni da ba abunda ya shiga tsakanin mu dashi wata kyauta zeban..? Bata gama tunani ba Safara tace amishi nan ga taki kyautar, na bude? kode amshi ki bude da kanki,.. hannu na rawa ta amsa koda ta bude clé (key) ya fado na mota, ta mikawa Safara tace laaa key d'in mota ne gashi. Safara ta washe baki ta na dariya tare da fatan alheri har bata san tayi subul da baka ba tace kai gaskiya Manane yayan nan naki na sonki da yawa. Ita de kallonta kawai take, safara ta futa da clé don nuna wa sauran *Zuri'ar* (hum koya akayi ya mata kyautar mota ? 😏 nasan de be huce shawarar Haidar ce .) haka ta wuni bak'i nata shigowa,,kuma

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41