Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ke da girki ba ta shirya tafice gidan Sam dan tanada yakinin can zata wuni Sosai sukayi farin cikin ganin juna saboda Sam bata koma school ba tun bayan auren ta one week kenan nan gidan ta wuni har bayan la'asar ...suna cikin hirar su wayar Manane tayi ringing sai da gaban ta ya fadi da taga number Abba dan ba kasafai ba yake kiran ta da sauri ta d'aga tace hello Abba ina wuni ..........ta d'an jima tana sauraren shi se tace What!!! sai kawai wayar ta fad'i a hannunta tana fadin innalilahi wa....... Da sauri Sam ta d'auki phone din tana fadin minene Manane waye ba lafiya? Ita kuwa kasa magana tayi dab'as ta zauna zaman dirshan girgizata takeyi amman shiru da sauri ta dauki phone din takirayi Yesmine bata d'auka ba ta kirayi Umma itama sai a ringing na hudu ta d'auka tace hllo Umma ga Manane nanfa.. Bata karasa zancen ba Umma ta katse ta da fadin kunji rasuwar ko? Ras gaban ta yafadi tace Umma wa ya rasu ? Tace Allah yayiwa momyn Khalifa(Salma) cikawa sakin wayar tayi itama ta fashe da kuka sai asan nan Manane ta samu kukan yazo mata suka rungume juna suna ta kukan Sun jima ahakan sannan suka rarrashi juna suka tafo gidan Papy inda nan ne za ayi sutura... Sosai *Zuri'ar* sukaji mutuwar a jikin su dan Salma yarinyace ce me biyyaya ,,ladabi da iya zaman duniya ga kuma girmama na gaba Suna k'ara tausayin yaran da ta bari wanda ko shekara biyu baiyi ba. Har akayi sadakar sati amma Halima sau daya tazo shima badan ra'ayin taba sai dan Rid ya nuna fushinshi akan hakan.......... Dan ita shagulgulan gabanta takeyi domin neman hanyar da zata sakamishi magani takeyi. Saboda tasha zuba mishi amman cikin ikon Allah wani abu seya gifta Allah yake k'ara kareshi daga tugon ta har maganin nata yayi end dan haka ta k'udiri aniyar komawa wurin'' boka gobe da nisa.'' One month later A b'angaren Haider kuwa Sosai mutuwar matarshi ta shigeshi dan har yau bai koma wurin aikin shi ba kullum yana makale da d'an shi Khalifa baya iya rabuwa da shi sai in har yana jin yunwa ko kuma in dare yayi sai yakai sa wurin Umma dan yanzu Khalifan a hannunta yake. A bangaren Rid kuwa gaba daya aikin clinic din ya dawo hannun shi dan yanzu bashida lokacin kanshi ma bare na matanshi. ******* zaune take gaban boka gobe da nisa tana zayyana mishi rashin nasarar da tayi da kuma canjin da bata ganiba a wajen mijin nata dan har yanzu yana makale da dangin nashi. Wata mahaukaciyar dariya ya kwashe da ita se kuma ya kuma daure fuska...yace ungo na wani kullin maganin ya bata yace ta zuba mishi a abunci ko na abun sha amman da sharadin kada tabari kowa yaganta lokacin da take zubawa. Bangaren aljani dan kundalo kuwa ki kwantar da hankalinki yayi tafiya kuma gobe2 nan zai dawo sosai taji dadin maganar ta zube mishi kudin annan cike da karfin guiwa ta koma gida. Washe garin ranar Manane shigar 10h take amman duk da haka sai data yi musu break ta jere musu bisa dinning koma warta room ke da wuya Halima ta fito tayi dan dube2n ta dan a tunanin ta Manane ta tafi school dan haka ta bude isotherme (kular tea)ta fara zubawa tana tsaka da zubawar sai ga Manane ta fito zaro ido waje tayi tayi takoma da baya ta lab'e tana kalon ikon Allah a ranta tace to ita wannan miye take zubawa kadade abunda Sam ta fadi da da dad'ewa gaskiyane? ganin zata juyo da sauri ta lab'e bayan ''rideau''(labule) Ta kama hanyar stair Tazo giftawa tana dariyar k'eta tana fadin shegiyar yarinyar nan da *Zuri'ar* nan tasu takare dan daga yau zan fara dasa mulkina a *Zuri'ar* nan takara kecewa da wata shegiyar dariya ta hau stair dan shiryawa zuwa school. A bangaren Manane kuwa suman tseye tayi da kyar ta tataro nutsuwarta tana ganin shigarta room da sauri taje ta zubar da tea din sai da ta wanke shi har so biyar amman bata gamsu ba Kai daga karshe ma sauya shi tayi ta zuba wani sabon tea ta kawo dining din. Nan falon ma ta zauna tana gadi dan ita abun yabata tsoro matuka kuma ta kudirci sama Halima ido da duk wani motsinta . Tana nan zaune suka fito tare suka zauna itama sai ta taso har Halima zata zuba mishi Manane ta rike hannunta tace ko kin manta nice keda girki dan haka nike da ikon zubama Honeyna abincin tsuka tayi takoma ta zauna tace yarinya karama dake sai iya barikanci . Dariyar shakiyanci Manane tayi tace aie IYAWA ce in wani ya isa yayi mugani... a ranta ta ce zan gwada miki iya barikin kuwa sama cinyar Doc Rid ta zauna ta fara bashi abincin abaki sai shagwaba take zuba mishi sosai take shishige tana shafa mishi kanshi zuwa bayan shi shikuwa ya saki baki kamar mai kiran Habu a kasuwa Taunar abincin kawai yake yana karajin dadinshi dan yarinyar ta tafi dashi amman a ranshi yana mamakin yanda take kulla dashi ta saki kuma jikinta dashi idan har a gaban Halima ne amman kuma idan suka kadaita su biyu bata iya ko kalon shi Cikin ido Halima kuwa sosai abun ya bak'anta mata rai a ranta tace kuyi abunku ku gama daga yanzune har zata tashi sai taga Manane ta dauko tea da sauri ta koma ta zauna tana washe baki Manane kuwa girgiza kai kawai tayi fara bashi tea din ... D'aga kan datayi taga takwas ba minti goma da sauri ta tashi tace ayya Sweetheart nakusan saka latty tashin yayi shima ya mata kiss a lip din ta yace ai duk laifin kine ...... Dede zai fita daga palon ya juyo ya amshi brefcase dinshi yace rakiyar ta isa daga nan.... Ta sani sare Halima na bayansu se kawai ta Rungumeshi tace'' prend soin de toi my honey''(ka kulamin da kanka)'' et soit prudent'' kamo hancin ta yayi har seda tayi yar kara yace ki kula min da kanki kema ... Duk scène din nan a gaban Halima akayi koda tazo ficewa seda ta bangaje Manane... Ita kuwa ta d'aga murya tace kadan ma kika gani daga iya barikina watakila da kin mini biyyaya a matsayina na uwar gidanki yayarki ba da na taimaka na koya miki wasu salon da zai hana na amshe miki girkinki.tayi Shigewarta d'aki .. tabarta nan. (Umm Manane son girman tsiya) A mota shikade yake ta tunanin shi ....besan me yasa ba in yana tare da Manane yake manta kowa da komi gaba d'aya .yana son su zauna wuri d'aya ko dan ta tunga zuba mishi yarintarta da kuma shagwab'a.....murmushinta....tsaftarta...dressing dinta kai da komi ma nata yanzu burgeshi yake bare in tana dariya fararen hakoranta suka bayyana da yar wushiryar nan tata.....se sakin murmurshi yake har ya iso clinic din.. Zaune yake a office yane yan rubuce2 shi kawai sai yaji kanshi yafara saramishi tare da wata irin juya tun yana iyayin bismilah har ya yanke yafadi kasa sumamme ..... .. To fans mikuke tsanmanin yasamu Rid ? Kadade fa aljani dankundalo ne yayi aikin shi? Masoyan

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41