Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

Manane kad'awa se kawai taja motarta itama ta mara mishi baya saboda yanda taga ya tada hankalinshi tasan ba lfy... Da wani irin ihu ta farka tana fadin wayoo nayi gamo duk a tsorace take se zare ido take se kuma ta kece da dariya wanda ya bama *Zuri'ar* tsoro... Dede shigowar su Manane take fad'in walahi se na haukataki Manane daga ke har Rid din...e'e Boka ya bani maganin harda na mallaka ma tanayi tana rawa daga gani kasan ta fara haukacewa. .ganin Manane yasa ta daka wani uban tsale ta isa gareta ta shako wuyanta tana fad'in yau se na kasheki shegiya... Idanun Manane duk sun firfito saboda damkar. .da kyar Rid da Haider suka b'anb'are Halima ..ai kuwa se ta dawo kan Rid din...beyi wata2 ba ya fara zabga maya marruruka se Haider ya janyeshi... Bakinta be mutu ba tacigaba da da fadin ee nice nayi sanadin rabaka da *Zuri'ar* ka...gaba daya ta tonawa kanta asiri.. Ganin hauka ne take ainun yasa aka kira sécurité aka kaita dakin mahaukata .. Manane kam se kuka take jin irin abunda Halima ta furta....su Umma duk jikin su yayi sanyi... Dole aka kirayi dangi Halima aka sanar musu...nan dan kuwa se gasu sun cika clinik din. Haider da Rid kuwa wurin doctan dayayi traitement dinta suka shiga... Doctan yace shi fa a iya binci ken shi babu abunda ya shafi kwakwaluwar ta se de sutafi ayi mata na gida sanna kuma tana da ciki har na tsayon wata biyu amma *SANADIN ACCIDENT (littafin Fasma na gaba insha Allah)* din cikin ya zube..... Wani irin ihu Rid ya saki jin Halima na da ciki...se kawai jiri ya d'auke shi ya fad'i nan... Ya kusan rabin awa san nan ya medo hankalinshi su Umma ..Mom etc duk suna tsaye2 a kanshi...ganin ya bude ido ya sasu kara matsowa kusa da shi... da salati ya farka se kuma ya fara fadin Halima kin cuceni.Allah ya isa tsakani da kee...bazan taba yafe maki ba....se kuma ya fashe da kuka kamar karamin yaro.... Nan de suka rarrashe shi dan yana tune da komi ya k'ara nema su yafe mishi ...ya zaro takarda da biro ya fara rubutu akai... Da sauri umma ta rike mishi hannu tace mi kake shirin aikatawa ne haka... Cike da takaici yace takardar sakin Halima ce...dan daman bana cikin hankalina lokacin da na aureta...blablabla Umma tace kasan de saki bashi da kyau..kayi hakuri ... Bata gama ba Momy da Mom suka ce haba umma yanzu duk abunda yarinyar nan tayi amma kike goyon bayan ta.... Zata kuma yin magana suka ga Rid har ya fita ashe tuni ya rubuta takardar .... Yana zuwa ya mikawa Yan gidan su ya bar clinik din ma gaba daya.. Dole suma *Zuri'ar* suka komo dan daman saboda shi sukazo .... Wunin ranar kowa beyi shi cikin jin dadi ba ..... Suma dangi Halima haka suka kwashe ta akayi gida da ita...dan abun nata se kara gaba yake....(duniya kenan gashi kina neman haukatar da Manane kekin haukacen ..Allah baya barin wani da wani ..kuma dama ance ramin mugunta gina shi kad'an dan watara na zaka iya fada ciki.....rayuwa kenan *ABINDA KA SHUKA* (Littafin Anty Mira dukda ma de ta Shuka mu😜) shi zaka girba.... Allah ya shiyar da mu sannan ya karemu daga sharri masu sharri ..ameen Two days later.. A kwana biyun nan sosai Rid ya saki jikinshi da yan uwashi banda Manane dake d'ari2 da shi...... Yauma kamar kullum ko break batayi ba ta fito cikin shirinta na zywa school...shiga motarta kenan taga Rid na tunkaro ta yayi mata kyau matuka amma se..tayi kamar bata ganshi ba .... Har ya zagayo ta side dinta ya tura kanshi cikin motar. .. Kanta a kasa ta gaisheshi ..jin be amsaba ya sa ta d'aga kai ta kalleshi aka kuwa yi sa'a sukayi ido hudu ..kasa dauke idanunta tayi seda taji yace ina zaki ne da wanna shigar? A takaice tace shool mana... Nunata yayi da dan yatsa yace ji nake da dad'ewa nayi miki magana kan irin shigar nan Kallon kanta tayi ita bata ga aibun shigarta ba dan Atampa. Ce sanna ta daura after dress ta saka baby hijab.. Ganin batada niyyar yimishi magana ya sa yace idan har kina son zuwa school yau to tun wuri ki koma ki sauya kaya.. turo baki tayi tace haba ya Rid nafa kusa yin latti ..kumafa after dress ce.. Daure fuska yayi yace na de gaya miki .. Ganin tayi kikam ya sa ya fizgo ta da karfin tsiya har se da ta kusa faduwa da sauri kuma ya kamo abun shi.. tace kai yaya ai se ka karya ni irin wannan fizgar Baice komi ba ya fara janta ganin ya nufin part din shi na gidan ya sa tafara tirjewa tana fadin miye haka Har tsakiyar falon suka isa yayi jifa da ita ta fada bisa kujera Ya dawo ya ce tunda kin zabi zaman gidan se ki zauna ai Yasa kai ze fice Da sauri tasha gaban shi ta kalle shi cikin ido tace ban gane ba mikake nufi da in zauna a gida ba.. Tsawon lokaci suka dauka suna kallon junansu.. dukan su wani abu suke ji yana musu yawo a jiki seshi yayi karfin hali ya janye idon shi saboda yarinyar duk wani kwar jini take mi shi ga wani shakkun ta da yakeji be san itama karfin hali take yi ba Ya dake ya ce matsa ki ban wuri ina wasa dake ne Ta rike guku ta ce aa amma kasan baka mini adalci ba idan ka hanani zuwa school ina son zuwa bibliothèque(library) dan iyin review dan da alama test din da zaka yi zeyi wahala Dariya keta yayi mata yace sosai ma ko zeyi wuya yayi gaba abun shi Da gudu tayi ma kofar key ta zaré ta ce walahi yanda bazan tafi ba kaima baka je ba da gudu yafara binta Nan fa Suka fara zagayan falon ya kasa kama ta tana tayi mishi dariya dan ya gaji dole ya dawo ya zauna ya na meda nunfashi yana dariya kasa2 shima Itama dawowa tayi kusa da shi tana fadin kai yaya ja dinga yin sport d'an gudun nan har ka gaji Ba shiri taji ya damko ta ya ce wana kama.. ta ce kai yaya kasan ni da kai ba ta baci ta shagwabe fuska ta ce dan Allah yaya ka barni in tafi sambaby na can na jira na tayi yinkurin tashi Fizgo ta yayi se da ta fada kirjin shi wani shok suka kara ji irin na wacan lokacin nunfashin ta ne ya nemi dauke wa ta kara zaro ido ta kalle shi yayin da shima yake kallonta se kimuma ta meda kallonta zuwa bakinshi .....tana son yimishi magana amma ta kasa se kawai ta fashe da kuka Da hannun shi biyu ya kamo fuskarta yana fadin what happen ?my baby Batace komi ba .. bata yi aune ba sey jin bakin shi tayi cikin nata sun jima suna budirin su kawai se muka aje biro da takarda muka zuba wa sarautar Allah ido na so in ce musu tara(9) tayi Aïcha ta ce in rabu da su ai sunsan da wannan sun jima suna Abu daya

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41