Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,211 words 0 views Progress saved
Download Book

tab'a fatar jikinta me laushi da kuma kanshi turaren ta me gusar da hankali..se murmushi yake shi kad'e(uhmm😏 su Rid manya) Wata wutar sha'awar Manane ce ta taso mishi sakamakon yawon tunanin na ta dayayi tayi wanda ya sashi dole yanemi Halima dan ya rage zafin abunda yakeji duk da bawani hadin kai ta bashiba.dan da kyar ma ta yarda.. Four days later Yau takama samedi ba school kuma yau ne Halima ta cika satinta dan har ta sakar wa Manane girki duk da dama ba ita keyi ba Manane ce meyin shi jefi2.shima se idan Rid ya mata jan ido ko kuma taga yanan son.ya lalatsata . tun safe Manane ke gyara2 gidan saboda yau itake da Boss gashi kuma yau cikin *Zuri'ar* su zasu yi diner dan tayi missing din wasa da dariyar da barkwacin da kuma tsokanar da sukeyi ita da yan uwanta.. Tun bayan sallah la'asar ta fara girke2 dan abinci masu rai da lafiya kalla biyu tayi ......tare da wani had'ad'an juice na garin 'dan kuka' da madara(masu son koyan juice din sumini magana ta private) Sai wajejan magrib tagama tayi sallah sannan tayi wanka wata tsadadiyar shada ce ta saka wanda tasha aikin hannu gashi kuma ta amshe ta dan dinkin doguwar rigane sai bayan isha'i yazo suka fice suduka uku itama Halima wani shegen leshe ta saka dinkin riga da sket tayi kyau abunta Dukan su simple make up ne sukayi Doc Rid se satar kallon Manane yake dan sosai ta birgeshi dan yau ta kara yi mishi kyau. Koda suka shigo duk su ya Adam da su Safara sunanan zaune sai fira suke ,iyayen ne kawai ake jira su iso .. Suma da kamar minti goma suka iso nan fa aka shiga murnar ganin su..sosai sukayi wa Halima tarba se nan2 akeyi da ita duk dan kar taji sun wareta.. Itako haushin su ma takeji Aka zuzuba abinci aka fara ci suna tsaka daci Papy ya fara yin magana cike da tsokana yace amman juice din nan fa ya min dadi caraf Ariff yace Papy ba kai kad'e ba ni nama kasa gane name nene akayi .. Gaba daya palon aka kwashe da dariya banda Halima da murshine kawai tayi Haider yace haba shiya sa naga mutumin se shining yake kwana biyun nan ashe gara yake kwasa.. Rid ya b'ata fuska ya ce ya ishe ka haka fa ..dan sa ido kawai.. Wata dariyar aka sake yi.. Ita de Manane ko a bata ceba .. Sosai ran Halima ya qara b'aci tana qara samun qarfin guiwar aiwatar da qudirinta. Se goma kowa yaja iyalinshi suka fice. Koda suka iso kowa dakin shi ya nufa Ita Halima gado kawai ta fada ta fara bacci ..don bacci sosai takeji Manane ko wanka tayi tare dayin yan nafilfili..ta shafa lotion sanan tabi duk gab'ob'in jikinta da humra wani sihirtacce kamshi jikinta ke fitarwa..tayi brosh rigar bacci ta coton tasa doguwa har guiwarta tasa fula sanan tabi lafiyar gado dan haka takeyi kullum ,,data ta kunna dan wunin yau bata hau ba..tayi sa'a kuwa sambaby da antySadiya na online dan haka se fira ta b'arke .. Docta ko bayan yayi komi na al'adarshi gadoya hau ya kwanta yana zaman jiran Manane .sha daya (11)shiru bega Manane ba .yana nan har sha biyu shiru kake ji a ranshi yace kadade yarinyar taki zawwa fa..(😏yo da wayace ma zowa zatayi ne?)tashi yayi ya nufin dakin nata . Tana kwance rub da ciki wayar a hannunta se shat take abunta tana dariya mara sauti bata ma san da shigowar shiba... Seji tayi ance ke b... Wash kuyi hakuri da wannanπŸ™πŸ™ Gaisuwa garku yan group din''Secret des femmes''Allah ya bar kauna.❀😍 For coment :99951593 Fasma&Aisha [27/1 21:04] ❀Fasma&AΓ―cha❀: πŸ’“πŸ’žπŸ‘ͺπŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ‘¨β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ’•πŸ’ž Story&written by πŸ‡³πŸ‡ͺ ~AΓ―cha~ and ~Fasma~ πŸ‡³πŸ‡ͺ _Dedicated_ _by_ _Ramatou_ 100__105 ```__Manzon(SAW)ya ce:''bai halatta ba ga matar da ta yi imani da Allah da ranar lahira ta yi tafiyar kwana uku saidai tare da muharraminta'' ' Muslim ne ya rawaito shi_``` Seji tayi ance ke ban wayar nan . Firgit ta tashi zaune tana kallonshi cike da mamaki kwance a fuskarta a ranta tace to miya kawoshi rom dina cikin daren nan Bata gama tunanin ba taji yace inba ma renin hankali ba ina can ina jiranki asheke bakida alamun zuwama ..wai ma miya hana ki zuwa daki na? B'oye wayar tayi a bayan ta tana fadin dakin ka kuma to ni mi zanyi a dakin ka cikin daren nan.. Gadan2 ya fara tunkaro ta yace ban wayar na ce Kasa2 tace ni wlh bazan bayar ba salon ka anshe min irin na wacan lokacin ta sake boye ta a baya. Gadon ya hayo yashi ga kiciniar kwace wayar yana fadin wai yaushe reni ya shiga tsakanin mu da ke da har zance kiban abu ki k'i kicin2 da rai tayi ta cinno me baki cike da shagwaba take mishi gungunin to wai ma mizakiyi da wayana ne? Hannushi ya kai bayanta yace ina ruwanki da abu'da zanyi da'ita .. Sosai suka shiga kokawar kwace wayar itako se kara meda hannun baya take tana kokarin b'oye wayar Salon kokowar ne ya fara changΓ©(canzawa)lokacin da Rid ya fara dan shashafa ta shi saboda laushi da kamshin da fatar ta take yi shi kanshi yana mamakin yanda kwanan yake kasa resiter idan fatarsu ta hadu wanda dacan bahaka ba yakeji .gashi kuma yanzu beson b'acin ranta...amma irin girma kai na Rid se ya dangantashi da dan yana yayanta ne.. Jin abunda ya fara yimata ta fara tutureshi dago bakinta tayi dede kunanshi ta saki kuka tace dan Allah yaya ka barni ni bana so irin salon da tayi anfani wurin maganar ne ya kara rikitar da shi da ker ya dawo daga duniyar daya tafi dan har ya fara sakin layi .. sakamakon kukan da takeyi tashi yayi tare da karbe wayar .. Ya fara dibawa baiga komiba sai chat dinta da sam da kuma na groups ya jima yana bincike ko zega na miji amma baiga komi (πŸ€”miye na bincikin wayar kodey mutuman yafara kamuwa ne😜) Mika mata wayar yayi yace ina jiran ki a dakina sauran ki b'atan lokaci ya fice, kasa2 tace ni fa ba inda zani taja bargo ta mirgina tayi konciyarta..bajimawa ko bacci yayi awon gaba da ita Yakai rabin awa yana jiran ta bata zoba bayada ya iya dole yatashi ya nufi dakin akwance ya iskota tayi d'aya2 tana baccin ta hankali kwance kara sawwa yayi ya ya kwanta suna face din juna jawota jikin shi yayi yana kara kare ma fuskarta kallo sei barawon baccine ya sace shi. Asuba alheri Ta rigaishi farkawa da asuba jinta jikin mutum ya sata qara bude ido ta sauke su kan kyakyawar fuskarshi ta jima tana kallon shi dan yayi mata da kyau da bacci ..tana kuma mamakin wai itace yau jikin Rid bisa fafadan kirjin shi me tsada bata san lokacinda murmushi ya kubce mata .ta jima a haka sanan ta miki dan jin an fara asalatu toilet ta nufa ta rifo kofar .k'arar rufa k'ofar ne ya tada Rid da salati a bakinshi ya farka sanan yayi addu'ar tashi daga bacci..ya jima nan zaune seda yaji ana famar shiga massalaci sanan

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41