Chapter 12
Chapter 12
suka cigaba da hirar su har akayi Kiran Sallah azahar suka tashi suka gabatar da sallah... Suko basu suka shigo gidan ba se bayan sunyi sallah azahar,anan masallacin suka gamu da ya Adam dan haka direct gidan Doc Rid suka fice....koda suka shigo sun isko su suna hirar su ,bayan su gaishesu se akaci gaba da hira ,can Rid yace kai nifa' ''j'ai faim''(i am hungry)dan haka idan ku baku jinta sekuyi ta zama ya tashi ya nufi dining,,, suka kwashe da dariya sannan safara tace to ai dining d'in baze dauke muba muduka dan haka dawo muci anan palon,,ya dawo ya zauna yana jira dan yau yayi ta kai komo a office shiyasa ya kwaso yunwa.... Kuyi hakuri da wannan🙏🙏 Love you all❤ Fasma&Aïcha [27/1 21:04] ❤Fasma&Aïcha❤: 💓💞👪👨👩👧👦👨👧👦 *Zuri'ar* *mu* ( *Notre* *Famille* ) 👨👩👧👨👩👧👧👩👧👦💕💞 Story&written by 🇳🇪 ~Aïcha~ and ~Fasma~ 🇳🇪 *Dedicated to ZURI'AR MU hausa novel fans🙏love you all* 45__50 Lédar cin abinci madedeta biyu ta kawo ta shimfid'a sanna ita da su Muhsana suka d'auko kulolin tare da plateau plat)guda biyu ,da tarmos da cup suka aje ,,duk suka sauko kasa Manane ta fara zuba abincin plat biyu tayi na mazan daban na mata ma haka ,,tunda ta bude kulolin Rid ya fara lumshe ido so kawai yake tagama zubawa ya sa hannu..tana idawa kuwa ya saka hannu tare da Bismillah..su ya Adam suka fara ci tun suna gumtse dariya har suka dinga yimishi ita dan hannu baka hannu kwarya yake ci tare da zuba santi ,yana fad'i wai tuwan na gidan Ummata ne ko kuma na gidan Mom ne? Haider yace mika gani? d'and'anon ne da kuma dad'in kamar na gidan Umma kuma kamar na gidan Mom... Humm kaide ka sani., seda yaji nat tukon ya dauk'i kunun ayar ya fara kwonkwad'a... .seda Ya Adam yace to kadade ka shanye mu bamu shaba ,, yana dariya yace anty Safara amma abinna daga gidan umma na aka kawoshi ko?,. .tace wai da gaske baka gane abinci wani gida bane? to idan na sani zan tambaya ne.?.. .to na gidan kane ,,matarka Manane ta girka duka tuwon nan harma kunun ayar. .haba shiya sa naji maggi yaso yayi yawa ,sanna sucre(sugar)yayi yawa cikin kunun ko ta'aza kowa irin tane da nan karen son zaki ,itade bata yi magana ba illa turo baki da take tana gunguni kasa2 ,,ya Adam yace daga baya kenan seda kagama santi naka yanzu zakace wai wani sugar yayi yawa haba Malam kawai ka yarda matarka ta iya girki ko dayake horon Umma da Mom ne dole ta iya ai ..haba wani santi kawai de dan ina jin yinwa ne.. suka kwashe mishi da dariya duka ,, haka sukayi tayin hirar su da tsokanar junan su har aka fara Kiran sallar asr suka yi alwala suka tafi masallaci,,bayan sun dawo ma hirar ce sukayi tayi har sallah magrib tukon suka watse dan shiryawa zuwa cin dinner gidan Papy .bayan sun gama cin dinner ne Doc Rid ya sako zancen cigaban karatun ta ,,kowa yayi murna tare da sa alkhairi.... Washe garin ranar ,,kamar kullum tayi gyaran d'akunan da palon tare dasa turaren wuta nan danan gidan ya d'auki kamshi danshi nema ya tada Rid,, da Sauri yatashi ya fad'a toilette dan har ya kusa yin late... ita ko bayan ta gama gyare2 seta fad'a cuisine (kitchen)danyi abin kari dan yau sha'awar cin kosai da kunun gujiya take ,,,,kafin ya fito har ta jera bisa dining tukon tashiga wanka.. Bayan ya shirya ya fito direct dining ya nufa ya Budé kular se yaga kosai ..da har ze rufe se kuma ya dauki daya yaci haba ai ko seya zauna ya zuba tare da kunun ya fara ci ,har cikin ranshi ya jinjinawa iya girkinta uwa uba ga tsapta ,,koda yake ai raina su umma ce dole tayi tsapta...(kanka de ake ji...) Daya gama ci ya tashi ya fice har ze bude voiture(mota)ta fito tana fadin yaya ''arrête'' (stop) ya tsaya yana jiran ta kamar ranan babu de hijab..ta iso tace bonjour bien réveiller j'espère ? (Ina kwana da fatan ka tashi lfy?) ya amsa da oui (yes)et toi?(ke fa?) tace pareil également (same too you), ,to que veux tu?(mi kike so) dama je veux aller au marché (i want to go to thé market) qu'est ce tu vas acheté (mi zaki siyo). Beaucoup des choses (a bubuwa da yawa) d'accord (OK)idan kin bude drower na akwai kudi seki tafi amma faut mettre du hijab (kisa hijab) tana dariya tace thanks jazzakillahou khairan,, amin...ta juya zata fice ,har ya shiga motar ya fito yace ko kuma ma bari idan na dawo zan kaiki ,,dan nasan ki da gilgilwar kai kada kije ki jima. .tace to adawo lafiya..amin .. Koda ya fita se ya biya gidan Mom ,ana shirin aiko musu da break ,,ya gaishe ta..tace to zauna kayi Karin in yaso ita se akai mata nata.. ya fara Sosa kai yace na karya fa Mom ,, a ina? Manane tayi mana kayan Kari yau,,.. Manane d'in..? eeh Mom.. Nida cewa nayi ma da adaina turo mana se ta ringa yin dan hannu ta ya fad'a tayi jimm se tace ,shikenan amma zan samu wadda zata ringa tayata aikin... OK Mom amman fa girki ita zata ringa yi... to naji jeka kada kayi retard (latti)kana mita. To se anjima ..ya fice.. Bayan futar shi ta kirayi Manane sukayi gaishe2,tukon tace yanzu mijinki yake fad'a min kekiyi kayan break d'in yau sannan yace a bari ki ringa yi ko kya kware ,,OK Mom ba matsala hakan ma yayi dan yanzu ina sha'awar yin girki.. .amman zan samo miki wacce zata ringa taya ki aikin. .kai Mom da kin barta ma ,haba wannen sharar gidan naki me fili ma aikine.ga kuma école daza akama nan da 2semaines(2weeks)tunda vacance (vacation) d'in ya kare. ..shike nan thanks My Mom.. Sukaci gaba da hira se cen suka yi salama.. Manane komawa tayi ta kwanta tunda tasan baze dawo ba se bayan sallar azahar... Ba ita ta tashi ba se 12h ,da Sauri ta fad'a toilette ta wanke fuskarta tare da kurkurar baki tafice cuisine.. Farar Maka ce ta dafa da miyar viande haché (nama nikake),,ta gama ta jera bisa dining ta sa turaren wuta nan danan gidan ya d'auke da kamshi tashiga wanka,,da alwala ta fito ,tasa atampa kalar maron(choculate),tasa hijab tayi sallah... Be shigo gidan ba se 15h.(ukku na rana).direct d'akin shi ya fice ya Watso ruwa ya dawo dining ,ya zauna dayaga bata da alamun fitowa seya kwalla mata kira .ta fito ta mishii sannu da zuwa sannan ta fara zuba mishi,. .takoma palo tana kallo..bayan ya gama ya dawo palon shima ,tace na dauko hijab ina mutafi. ? .a'a se anyi salla ,,Daga haka babu Wanda ya k'ara cewa komi ,har aka kirayi sallah ya tafi masallaci.kan ya dawo hartayi sallah ta saka hijab tana jiran shi...koda ya dawo ya kalle ta yace kaikam kin shiga ukku ,har kin wani shirya to se ki jirani na shirya ,,ya shige d'akinshi. .bayan kamar minti goma yafito suka fice...a motar tace NANAS's market zaka kaini . Koda suka je babu abunda ta d'auka dukkayan zak'i ne ice cream. chocolat.biscuits dade sauran su...ya biya suka fice yace daman wanan abune kike
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41