Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Zuriarmu Book One Complete Hausa Novels 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

yanzu ta tabbatar da ta kamu da son yayana ta(wayooo Manane kinada jan aiki gabanki....to waima garin ya kika bari kika kamu da son wanda yace bakya cikin tsarin matan dayake so?🤔...tab) Sha daya na dare(11) aka tashi daga patyn direct aka huce da amariya gidanta.. Manane taji shigowar su amman taki fitowa har abokan ango suka fice.. Haider ma yaji dadin hakan dan dama yana kunyar Manane... Se bayan tafiyar su Rid ya rurufe gida da dakuna ya haura sama .... Ya daga waya ya kirayi Manane da har taso taqi dauka sekuma ta daukan ..ki fito palo muna jiran ki abunda kawai ya fad'a ya kashe wayar..... Da gunguni ta iso palon ,,ta zauna d'an nesa dasu dan haushinsu takeji.. Da Bismillah ya fara yayi wa Manzon Allah (SAW) salati.. sanan ya fara musu gargadi da nasihohi kansu zauna lfy ..ya kuma nemi dasu had'a kansu... Ita kam Halima da alama batama san miyake fada ba.. in ya shiga ta wannan kunnen seya futa ta dayan... dan sewani hararar Manane take tana wani girgiza k'afafu .. Daga karshe ya raba musu kwana bibiyu bayan ta ciyye satin ta ya d'ora dacewa duk me aiki ita zatayi girkin gidan sannan du' me girki ita za tazo dakina dan bawacce zan iskota dakinta ...idan dame magana tayi .... Ba wacce tace komi . Yace to Allah ya bamu zaman lafiya da *Zuri'ar*d'ayyiba Da sauri Halima tace cikin ranta tBa ameen ba ...ina ita ina wata *Zuri'ar*itada Boka ''gobe da nisa''ya gindaya mata sharadin kada ta kuskura ta yarda ta dau ciki.. Manane tace Ameen ya kuma baka ikon yin adalci tsaka nin mu.. Ameen ya ansa.. tana ida fad'ar haka ta tashi tana fadin se da safen ku.. Rid ko binta yayi da kallo hartayi shigewar ta dakinta sannan ya meda dubanshi zuwa Halima ,,wanda tayi fam kiris ya rage ta fashe ,a ranta kuwa tana tuna abunda boka ya fad'a mata kan cewa soyyayar da take Tsakani Rid da Manane cikin jinin su take dan haka rabasu farat d'aya ba'abune me sauqi ba ,,sede zeyi iya yinshi..tuna wa da haka yasa ta dan saki fuska. .. Daganan suka huce dakin Rid din ya umarce ta data yi alwala shiko fita kaiwa Manane ledar kajinta yayi.. raka'a biyu sukayi ya dinga kwararo musu addu'a wanda duk rabi guda Halima na ansawa kasa2 da BA Ameen BA ..sanan ya daura hannushi bisa kanta yayi addu'ar da Manzon (SAW)ya koya ...yamata tambayoyi wanda ta ansa 40% ciki dan sauran bata sansu ba.....ya koya mata sauran ..sanan ya bude ledar kaji ya ciyar da ita . daganan kuma abubuwa suka far wanzuwa babu shiri na jayo Aicha a guje muka fito. Dakin Manane muka lek'a dan ganin mitakeyi.. Akan abun sallah take da alama de nafila takeyi (.Allah sarki Manane).daga haka muma muka koma palon dan muyi bacci dan kada mu makara wurin samo muku rahoto.. Kiran sallar farko ta bude ido .ta tashi tayi nafilfili tana nan har aka yi kiran sallah tayi... Bata koma bacci ba dan a al'ada garin inde aka maka kishiya sannan gidan ku guda tofa ke zakayi musu girki har na tsawon one week idan Budurwace ..dan haka tayi gyara2ta kamar kullum tasa turaren wuta tayi musu break .farfesun kayan ciki tayi se kwai da ta soya da plainted da ruwan tea.. Dakinta ta koma tayi kwanciyarta.. Se wajejan goma taji motsin fitowar su..dan haka itama se ta fito dan suyi break... A saman dining din ta gansu har Halima ta fara zuzuba abinci ,,ranta ya soso kwarai kenan da bata fito ba su bazasu kirata ba..ta tab'e baki ta iso tare da gaishe su duk da Rid kad'e ta gaida..... Halima ta galla mata harara ,,itama ko ta rama.. Rid yace ke baki da tarbiya ne da bazaki gaida my love ba. Ta ya mutsa fuska tare da turo baki haba yaya nicefa Baban tunda nice uwar gida aii ita ya kamata ta gaisheni .ai se kasa ta rainani...aman bari na gaisheta ..tana qara ya mutsa fuska tace da fatan kin tashi lafiya amaryar mu?bata jira ansar suba ta fara cin break dinta duk da ruwan tea da plainted kawai take sha'awar ci.. Galala suka saki baki suna kallonta har ta dasa aya ba kamar Rid bama da tayi mugun bashi mamaki ..har ze fara fada Halima ta tari numfashin shi da fadin haba my sweet love kyaleta ci break dinka kada ka qware... tab'e baki tayi dan ko kallo basu isheta ba taci gaba da abunda take.. D'aga idon da zatayi taga Rid na bawa Halima a baki itako se wani shagwab'e midhi take tana wani kashe murya , dan takaici Manane bata san sanda taja dogon tsaki ba mtssss ta bar wurin se yanzu take nadamar fitowarta. Ta koma palo ta kunna TV.. Suko tab'e baki sukayi sukaci gaba da cin break din su ..daga nan ma daki suka koma sukaci gaba da soyewar su..dan daren jiya sun gurji armacin su dukda tasha wahala amman burdurcin nata yana rauni a matsayin shi gynécologis.. Kan kace mi gidan har ya fara cika dan yan uwa Halima da Manane d'in .. sosai Manane tayi musu tarba cike da fara'a ,.. Duk sun yaba da hankalinta ... hayaniyar su cema ta fito dasu daga dakin su duka wata narkye kiyar shadda ce a jikin su da alama ma anko ne sukayi dan kalar iri dayace.... Bayan sun fito ya tsaya suka gaisa da yan uwan sannan yyi ficewar shi.. Fitarshi keda wuya Halima ta daka tsale da ihu Tana fadin anty Kadidja wai kinga kyatattatu kan da my sweetyna ya ban...kafin su bata amsa ta fiddo wata shegiyar sarqa ta gwal tare da makullin motar ''LAGUNA ..sun tayata murna amman basuso ta fiddoshi gaban kishiyarta da yan uwanta saboda dukda al'adace bada kyautar aman akwai kunya .. Itama tasan bedace ba amman dan taba Manane haushi tayi shi kuma ko tayi nasara tunda ranta ya sosu... Allah ya taimake ta su yesmine da Muhsana suna gidan dan su suka kama mata tayi lunch.. Haka tayi ta musu abinci. break da lunch hana tsawan kwana ukun ..... Yau ta kama litinin Manane amakare ta tashi dan ko break bata dafa ba ta shiryawar ta ta fice ..suko se bakwai da minti arba'in da biyar(7H45) suka fito da shirin su na zuwa school because school d'in akwai su da tsanani ba'a fashi in har bakada kwakwara raison. .shima yanada lecture a can..koda suka iso dining din se suka ga wayam duda haka suka zauna zaman jiran Manane ta kawo musu break dan ji suke tana kitchen....after 10 minutes shiru ..Halima ta fara qorafin ita yunwa take ji gashi kuma mun yi late amman yarinyar nan bata gama break ba.....Rid ya tashi yana fadi bari na dubo ta ...koda ya shiga se yaga wayam...ranshi ya b'ace. Ya fice dakinta nan ma de bata ciki ..ranshi ya qara b'aci ..ya dawo yace tashi mutafi dan yarinyar nan bata gidan nan da alama ta tafi school ma....what??amman yarinyar nan ta ..se kuma tayi shiru.. .yace muta fi gidan Umma muyi break din se mu fice... .sakaka take kallonshi sannan tace Umma fa?bama Mom ba..?e jinake Umma surikar kace ,,ya b'ata fuska sekuma

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41