Chapter 6
Chapter 6
kanta yay yace "good girl, yana futa daga d'akin... ***************** Awajen daddy mans kuwa yana kashe kiran yafara tunanin menene amman yasaka basu gaya masa Imhal bata gidaba kuma ma bayauba tun jiya, a hospital ma takwana.... Abunne yad'aure masa kai sosai dan bai ta6a tunanin hakan daga gare suba, shida yatambayesu sukace tana bacci, yau kuma sukace tana makarantah... Shidai yasan Imhal d'insa bata dad'ewa haka bata nemesaba, koda zai mata fad'a, sannan bazata ta6a tafiya makarantaba batare data gansaba.... **************************** Wani makeken gidane wanda daka gansa kasan na manyan mutanene wanda suka ji'ku da arzi'ki. Gidan Alhaji Mansur kenan, wanda aka fu sani da Alhaji mans komai da ruwanka... Yasamo wannan inkiyarne daga bakin (Fawass) Komai daruwankan kuwa yasamu asaline daga jajir cewarsa wajen kasuwanci komai ana bugawa a company sa, babu abunda bayayi indai fannin kayan abuncine da sutura da furniture da kayan electronic.... Get din gidan nad'an bud'e nashiga ai sainaga bakomai nagani ba awajen gidan, subhanallahi, gidan yatsaru iya tsaruwa sosai kamar yadda kaga gidan turawan America haka tsarin gidan yake babu hayaniya, saidai kana gani kasan ankashe masa kud'i sosai.... Makeken gine ginene acikin gidan da tan'kama²ⁿ part² yadda kasan estate guda.... Ahankali natura 'kofar danake tunanin itace ta phalon gidan shiga nai ina waleee ido dan jiyo wani sautin masifa danakeyi daga upstairs yana tasowa.... Wata murya naji tana fad'in, yau idan Imhal tazo kashetane kawai bazanyiba dan saina yi mata dukan dasaita gwammace dama mutuwa tai da wannan tashin hankalin dazatazo tasamu yau acikin gidan nan..... "Yar iskar yarinya 'karamar "yar bariki kawai, tasan dad'in maza shine zata dinga guduwa idan na aiketa tana tafiya wajen su. Harni zata kunyata dan uwarta, ince mata tatafi tasiyowa ba'kina fruit wanda zasuzo da daddare domun yin dinner 🍽 shine zata tafi wajen kwartayenta takwana ko wlh saina sa6a mata kamanni wlh.... Wata murya ce tace mom kibarni da ita haka jameel zaizo nace tadawo dawuri tai masa girki dan zaizo yau 8:30pm shine wannan shegiyar yarinyar tasa yazo amman batai masa girkin ba gashi yace yafuson abuncinta tafi iyawa.. "Wlh saina kusa kasheta yau d'in nan bari tadawo, wata shirgegiyar mata nagani tana sakkowa daga sama, rai Amatu'kar 6ace tana ta huci Kamar tsohon kumurcin daya fusata, duka duka matar bazata wuce shekara 33 ba dan kawai tasamu dukiyane tai wannan muguwar 'kibar, sannan kuma da rashin gyara kanta da batayi saitazama kamar wadda takai shekara 40-45,duk takashe kanta da 'kazanta..... Kan 3 sitter tazo tazauna tana kwalawa Asabe mai aiki kira. "Asabeee.... Asabeee..... Asabeeeee... Kina inane dan ubankiiii....!!!!!! "Na'am hjy ganinan zuwa... Dagudu gudu sauri sauri matar da aka kira da Asabe ta'karasoo tazube agabanta, kanta na 'kasa tace gani hjy... Matar takai wajen shekara, 40-44 nidanaji tana mata wannan kiran ma zatona yarinyace 'karama, sai naga matarma tagirmeta sosai, tayi sa'ar mahaifiyarta ma... "Dan ubanki mekikeyi aciki ne tun d'azu ina kiranki.... "Hajiya tahowa nakeyine, inawa hjy KAUSAR girkine banasan ya'kone shine narage wutar kafun natahoo... Wuta kuma ta uban me, murhu kika kunna mun acikin, gida nan gidan yamiki kamane da jejin 'kauyenku... A'a hajiya mantawa nai wutar gass d'in narage kafun nafuto... Ohhhh, dakinbar aiki gidan nan yauu Ai baza'ai hakaba hajiya, amun afwa.... Ba wannan na tambaye kiba kinganekooo kifad'amun gaskiya banasan muna furcinki na tsofaffi.. "Dan ubanku ina kuka had'a baki keda Imhal ta tafiii...? "Cikin rawar murya bakinta na 6ari tace, "wlll......h h.j..y ba...b..u inda muuuuu......kaaaaa.... had'a baki taaa.... taaaa.....fi, danni ma tun jiya da rana da kika aiketa siyan kayan fruits dataimun sallama ban sake sakataba a idona ba..... "Idan nai buncike nagane bakinku d'aya wlh saima kusa kasheki, kuma saina koreki daga aikin da kike ta nacin zama... "Wlh hjy babu ruwana.. KAUSAR ce ta banka mata kiraa... "Asabeeeee....... Asabeee..., kin manta wannan pepper soup d'in dakika d'aurane da kuma chips din nan saiya 'kone dan uwarki...... "Ganinan zuwa hajiya, Kallon hjy maimuna tai wadda tahad'e rai kamar an mata aiken mutuwar uwarta, tace "in tafi hajiya.....! "Toda uban me zaki mun, tunda bazaki fad'amun gaskiya ba..... "Tashi kiban waje, shegiya muna fuka kawai....! Idan nabinciko gaskiya kuma nagane da hannunki wlh saina wula'kantaki.... Tashi tai tana sauri tabar gurin kitchen d'in, cikin sauri tashiga tafara duba chips d'in, taga bai kamaba kad'anne yad'an Kama kums shiga jaaa yayi baiyi ba'kibaa... Cikin sauri tafara kwashewa tana tsabesu ad'an basket d'in tsane soye²ⁿ su.. Zuba wani tai sannan ta gyara masa zama. Juyowa tai da zummar duba pepper soup d'in data d'aura shima danta ga koyayi. Wasu mugayen harara taga Kausar tana binta dasu... 'Dan kaucewa tai sbd tanasan taduba karya kama.. Wani waaawaannn mari taji Kausar tad'auketa dashi, saida taga taurari, gashi matar takai sa'ar kakarta... "Wannan wane irin rashin mutunci ne Asabeeeee, dan wula'kanci insaki kiyiwa mijina girki saiki tafi kibarsa ya'kone.... Itakam Mama Asabe kuncinta tari'ke tana cewa Kiyi hkr hajiya, wlh Hajiya babbace tai kirana, shine naje kafun nadawo yayi jaaa, amman ba 'konewa yayiba..... "Nuna ta tai da yatsa tace "Wlh yace abuncin nan baiyi dad'i ba saikin bar aikin nan wlh, banzar mata marar mutunci kawai.... Juyawa tai tana futa tace "Nanda 40m zai iso kiyi² kigama kafun yazoooo. " To hajiya, Mama Asabe tace tana bud'e tukunyar pepper soup d'in, dan indai wannan cin mutum cin ne tasaba dashi ita.... *********************** A asibiti kuwa FAWASS futa yayi duk abunda zai gama, saiya je yad'auki motarsa yay waje danya siyowa Imhal kayan dazata saka dakuma abunda zata bu'kata sosai yayo mata shopping sannan yabiya ta gida danya d'auko Nasma sbd ta taimaka mata takimtsa kanta dan bazata iyaba ita kad'ai... ********************** Alhaji mans kuwa cikin tsananin fushi da 6acin rai yafuto daga office d'in sa yayi space danya d'auki motarsa yau ko driver baya so, dakansa zai ja kansa..... Direct...... ✍🏻✍🏻✍🏻 *Keep waiting my fan's....* 🤗🤗😍 *Mrs Hallsad ce....💖* *Omh teemerh_🌹* *Gamasu san sufara biya da wuri saiku tun tu6i wannan number 08032762588* *_Idan kuma ta account ne_* *_Acc 0110015052_* *_SADIYA ABDULLAHI UMAR_* *_ECOBANK_* ```Idan kuma katin wayane na #400 ne kachal``` ```Comment section kuma #200 ne kachal wannan sau'kine agareku My special group kuma Da``` *'Dan shaye shaye ne* 🍾 *Am 16 years old* 💃🏻 *Sanadi* 😭 ```Duka #400 ne zaku biya wannan kyautar girmamawatace agareku saboda comment d'inku mai sharhi yana burgeni, yana sani nishad'i wlh, Idan banga comment dinku ba harjina nake wani iri, inayinku wlh🥰🥰. ``` [01/10, 8:51 PM] Omh Teemerh 🥰😘🥰: _*📲 TYPING📲*_ _*"🍾DAN SHAYE SHAYE NE🍾*_ _*paid book #300 only*_ _*By*_ _*OMH TEEMERH*_ _*👑THE QUEEN OF THE WRITER'S👑*_ 🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍 _*DASHEN🌲ALLAH*_ _*WRITER'S 📖 ASSOCIATION*_ ****************************** *'KUNGIYAR DASHEN🍃ALLAH* _'kungiyace tajajur tattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu_ *Dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, fad'akar daku, kuma ya nishad'antar daku* *AL'KALAMI✍🏻 YAFI TAKOBI🗡* ****************************** 🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍 _*WANNAN BOOK TUN DAGA FARKONSA HAR 'KARSHE SADAUKARWACE AGAREKI AUNTY ZAHRAH*_ _*FATIMA ZARAH*_ _*BLOODY NAH*_ _*🥰🤍🥰*_ *Episode* 1⃣1⃣⏩1⃣2⃣ ............Direct gida yatunkara, driving yakeyi amman gaba d'aya yafuta daga hayyacinsa harshi za'a yaudara, ayiwa 'karya akan 'yarsa guda d'aya takk.. Banda sun raina masa wayau tayaya zasuce jiya tayi bacci yau kuma tana makaranta.. Wani mahaukatan horn yadinga saki a'kofar gidan yana yinsa da 'karfi... Bud'ewa isa mai gadi yayi yana mamakin dayaga motar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40