Chapter 12
Chapter 12
*'KUNGIYAR DASHEN🍃ALLAH* _'kungiyace tajajur tattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu_ *Dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, fad'akar daku, kuma ya nishad'antar daku* *AL'KALAMI✍🏻 YAFI TAKOBI🗡* ****************************** 🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍 _*WANNAN BOOK TUN DAGA FARKONSA HAR 'KARSHE SADAUKARWACE AGAREKI AUNTY ZAHRAH*_ _*FATIMA ZARAH*_ _*BLOODY NAH*_ _*🥰🤍🥰*_ *Episode* 2⃣1⃣⏩2⃣2⃣ _______Ranar wata juma'a tunda tawayi gari takejin ciwon mara tin tana jinsa kad'an ² harya zama babba tun tana dannewa har abun yata'azzara, aka fara ganewa. Nan akai shirin shiga da ita hospital inda cikin ikon Allah akasamu 'kwararrun likitoci suka fara bata gudun mawa sosai. Abu kamar wasa saida Hassana takai yamma amman bata haihuba, kuma na'kuda takeyi sosai... Anan likitan yayanke shawarar ayi mata C.S kawai dan kar ita ko baby'n su shiga wani hali. Hakan yasa suka yadda aka fara shirin yimata C.S, saida aka shirya komai anshiga da ita theater room d'akin operation kafun afara aiki, kan baby yafara futowa, kafun likitan yazo tahaifi yaranta guda biyu duk maza kyawawa dasu... Haka aka gyarata ita dasu aka kaisu nad'i namusamman Duk ilahirin wannan family murna sukeyi da wannan haihuwa sosai inda aka dunga bata kulawa ita da yaranta. Saida suka kwana biyu, aka 'kara tabbatar da lpyr su sannan aka sallamesu. Iyayensu sunzo ''kauyen JANIKI inda suka taho musu da shatara ta arzi'ki sosai.. Ranar suna Hassan aka saka masa ABDULLAHI inda usaini aka saka masa MANSUR, anci ansha babu wanda zaice yanada yunwa wannan ranar ko ''kauyen JANIKI yasan ana sunan d'an gata, dan wani 'kwarya 'kwaryan biki aka had'a inda "yan ''kauyen suka rin'ka bada kyaututtuka gawad'an nan jarirai. Saida tai wata 3 sannan suka koma burni sosai ake basu kulawa cikin ikon Allah yaranta suka taso abun sha'awa. Lokacin data yayaesu saida sukai sati 4 da yaye sannan tamaidasu wajen Usainar ta da zama inda anan ne suka 'kara wayau sosai, kome sukeso shi ake musu. Hassan ana kiransa Fawass Inda ake kiran Usaini da Farhan Sosai take basu kulawa har suka kai tsawon shekara 5 aka sakasu amakarantar boko duk da sun fara zuwa islamiyya tunda wuri kafin asasu bokon. Haka rayuwa taci gaba su Fawass suka kai tsawon shekara 11 amman mahaifiyarsu bata 'kara haihuwaba inda itama usainar ta bata ta6a haihuwaba. Batada damuwar komai dan tanada su Fawass sukad'ai ma suna d'ebe mata kewa... Haka tarin'ka rainonsu koda yaushe cikin kulawa suke. Akwana atashi babu wahala awajen Allah inda Fawass da Farhan suka kammala makarantar primary da kuma saukar Al'kur'ani mai girma kamar yadda iyayensu sukai. Fawass ne bai iya fad'an sunan Daddy mansur ba sai yace daddy manss, shikuma farhan yayta masa dariya yana cewa mans kuma hakadai suka taso kamar wasa har abokai da mutanen ''kauyen JANIKI suka koma kiransa da daddy mansur da daddy mans. Dan kullum sukaje 'kauyen cikin bada labarinsa suke. Ana cikin hakane kuma Allah ya'kara azurta Ammie Hassana da samun wani cikin inda cikin ikon Allah wannan cikin bai bata wahala ba. Sosai suke farin ciki inda kuma daddy mans ya'kajin dad'i ganin d'an uwansa zai 'kara haihuwa, baijin koda d'ar saboda matarsa bata haihuba tunda yanadasu Fawass baya damuwa itama kuma haka. Cikin ikon Allah haka sukaita rainon cikin nan babu wasa inda cikinta yagirma harya shiga watan haihuwa... Nan ma suka koma 'kauyen JANIKI dan Baba Jan namiji yace saita haife zata koma gida kamar haihuwar fari. Haka kuwa akayi dan basu barta takomaba saida ta haihu. Ranar litinin ta haihu inda tasamu mace kyakkyawa da ita kamar Mahaifiyarta, ranar suna yarinya taci sunan kakarta FATIMA ana kiranta da NASMA sosai suka run'ka bata kulawa. Wanda Nasma tasha banban dasu Fawass dan ita saida tai wata 5 sanan suka koma garin kano.. Sosai Ammie take bawa Nasma kulawa bata tasu Fawass ma dansu sam ba sa wani zumud'in Nasma. Haka Nasma takai shekara 4 amman indai su Fawass sukazo saisunci zalinta suke tafiya, hakan nema yasa Ammie tace karsu 'kara zuwar mata gida can suje suzauna agidansu suma suzauna anasu.. Wani lokacin idan suka had'u wani taron ma suka dakata kuka intana fad'a akan Nasma saikai zaton ba ita ta haifi su Fawass ba.. Itako mommy usaina taita mata dariya dan tasan ita Nasma bazata daina raina suba sukuma bazasu gaji dacin zalin taba. Lokacin dasu Fawass suka shiga SS 1 alokacin Allah ya azurta mom usaina da samun ciki wanda yasanya dukkan su farin ciki dajin dad'i. Sosai sukaita murna anata farin ciki da wannan ciki data samu, nanfa aka fara bata kulawa sosai, inda harda su Fawass amasu bata kulawar, dansu murna sukeyi zasuyi 'kanwa suma suna zuwa da ita makaranta. In kuwa suka had'u da Nasma suyita mata suna cewa zasu samu 'kanwa ita bata da kowa.. Suyita mata dariya. Haka zataje wajen Ammie tana kuka, tafad'a mata, nan zakaga fad'a. Mommy usaina taita musu dariya, tace idan anyi zuciya akawo mata 'kanwa itama... Haka rayuwa ta 'kara shiga cikin jin dad'i da farin ciki koda yaushe kansu had'uwa yake 'karayi suna 'kara 'kaunar junan su. Dan duk da wannan fad'an nasu dasun siyo abu zasu kaiwa Nasma.. Alokacin kuma arzi'kin su Abbie ya'kara bun'kasa inda suka gina manyan company har guda 8 acikin garin kano akwai 4, akaduna akwai 2 a abuja akwai 2 sosai kasuwanci ya'kara cigaba wanda har suka fara siyarda kayan sawa dangin su shadda lace atamfofi takalma dasauransu. Awannan lokacin ne kuma suka had'u da wani aboki wanda shine yay sanadiyyar ruguza musu rayuwarsu. Yazo musu da magana akan sufara siyasa inda suka nuna masa basu da ra'ayi wannan sam. Ashe Alhaji Mannir akwai wata a'kasa dayazo da ita wasu manyan hajiyoyine suka aikosa wajen su suma kuma manyan "yan siya sane.. Wanda sunyi² sushawo kansu MANSUR, ABDULLAHI akan su auresu suka nuna musu basa da ra'ayin zama da mata biyu. Shine suka turo musu Alhaji munir danya yau daresu da siyasa. Daddy mans da Abbie kullum tunanin su yanakan Mommy usaina wadda take da ciki wata 5 Mai aikinta Mamah Asabe itace tadawo kula da su Fawass dasauransu, dan tun kafin ahaifesu take aiki agidan, mommy usaina ita tai mata aure wanda mijinta yake gadi ita kuma take aiki agidan. Mommy usaina bata ban banta Asabe dasu Fawass komai tatashi tana yimusu iri d'ayane sosai take bawa yaranta kulawa harta haihu itama tafara haihuwar namiji sannan tahaifi mace, yaranta biyu wanda shekara ce tsakanin su sosai mommy usaina takula mata dasu inda sunakai asasu makaranta mama Asabe tace boarding zata kaisu inda tasamu 'kwarin gwiywa daga wajen mommy usaina aka kaisu makaranta suda sudawo saidai idan anyi musu hutu... Kuma dasun dawo ake kaisu makarantar islamiyya tun safe sai dare wadda su Fawass sukeyi. Wannan dalilin ne yasaka mamah Asabe take 'kara ganin kimar mommy usaina dakuma daddy mans dan shima ba bayaba yanada 'ko'kari wajen kyautata musu. Haka komai yakoma wajen mamah Asabe bata yiwa mommy usaina zagon 'kasa tana zama da ita da zuciya d'aya kamar yadda itama take zaune da ita. Ammie Hassana taso tazo itama takula da mommy usaina amman ganin yadda mama Asabe take kula da ita yasa bata dawo gidan dazama ba saidai tazo tawuni saita koma... Idan kaga su Fawass sunje gidanta to tabbass hutu akai musu.. Kuma shima sundun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40