Chapter 35
Chapter 35
cikin bogi yayi wata 9 anan nace masa zanje gidan marayu dan akwai wani makirci damuka 'kulla nida wadda ta kar6i haihuwar Imhal a Hospital.... Dan a lokacin yara 3 mahaifiyar Imhal ta haifa amman sai muka had'a baki akan akaisu gidan marayu guda biyun mace da namiji, haka muka kwashe mata yara guda biyu muka gudu dasu, muna zuwa muka bawa wata mata akan idan nayi aure zanzo saita canjamun da yara maza guda biyu sai in biyata 'kud'in rainonta, haka akai kuwa , dan ta yadda kuwa inda ta amshi yara takai d'akin da ake ajiye yara agidan marayu... Haka kuwa akai bayan nayi aure sai nazo bana haihuwa, dan haka saina 6ullo da wannan tunanin ina cikin wannan yanayin kuwa naje kai musu ziyara dan na shiga watan haihuwa aikuwa ina zuwa bayan nagama raba musu wasu daga cikin kayan dana zo dasu, sainabar sauran dana kawo wanda ban rababa, dan abasu nazame jiki nagudu d'akin jariran nan nida wannnan matar, dan munshirya komai dama tun kan inzo... Hankalin mutane yayi kan sauran kayan dana kawo anacan anan rabo nafara na'kudar 'karya nan akace mutafi Hospital nace a'a bazaniba samm na'ki yadda nakafe, aikuwa aka ce za'a kaini wani d'akin manyan wajen nace a'a abarni anan d'akin jariran nan da wannan matar dana bawa yara biyu, kowa yafuta, haka kuwa akai kowa yafuta.... Bayan sun fita haka muka zubar da jinin dana siyo sannan kuma muka d'auko yaro d'aya mukace shine nahaifa bayan ta'kara masa wanka ta saka sa acikin sabon zani.... Dama kafun nazo munyi waya akan cewa an kawo wani yaro da aka tsinta jariri ko cibiya ba'a yanke masa ba dan haka washe gari nazo nayi wannan drama d'in... Komai damuka zuba masa jini 'kin bari mukai awanke, mukace zan tafi dashi gida, haka ma akace akawo mahaifa abunne anan mukace abarta ma bunne agidana... Haka akai aka bani yaro nataho dashi gida babu wani binbini, ko bin kwakw kwafi, dan lokacin da aka tsinci yaron aka bata, bata gayawa kowaba , wanda yabata tabawa kud'i kawai yatafi, tashiga dashi d'akin jariran ta ajiye... Shiyasa muka samu sau'kin mutane, dan dasai aairinmu yatonu... Koda nadawo gida yaro 'kememe ya'ki amsar nono na dan har maganin dazai kawo ruwan nono nasha amman yaro ya'ki sha... Dan haka nafara bashi madara, sbd in samu sau'kin abun.... Haka nai rainon khalil ita kuma Nafisat bayan khalil da shekara na'karayin laulayin 'karya har ciki yakai lokacin daya fara futowa. Lokacin ina zuwa asibiti kuwa nasha mamaki dan anamun test akace inda ciki na gaske, aikam murna babu irin wadda banyiba, dan dana fara laulayin 'karya, saina gaskiya yabayyana..... Haka naita rainon cikina abu kamar wasa ciki yagirma yashiga watan haihuwa nan naje Hospital akace saura sati biyu in haihu, aiko murna babu kama hannun yaro, nan nadawo gida. Randa sati biyu yacika kuwa ban haihuba saidai na'kuda kawai danakeyi tazo ta tafi.... Saida na'kara kwana biyu ina wahala amman ban haihuba, wasa Β² saida nai sati ban haihuba saidai wahala kawai danake sha, da abu ya'ki 'karewa sai aka ce aimun CS nan mukai shirin komai muka koma Hospital, ranar akaimun SC, Allah yatai makeni suka ciromun yarinyata mace aka saka mata Nafisat sosai nad'auki sanduniya nad'aura mata Bana manta lokacin data rasu, lokacin da kuka tafi bikin 'kawarku Abuja keda Ikilima, alokacin ne Allah yayiwa yarinyar rasuwa Allah yatai makeni Daddy man's baya nan aikuwa na'ki fad'awa kowa ta mutu nakira wannan matar dana bawa 'kannen Imhal guda biyu, nace mata tasan duk yadda zatai takawomun jaririya wadda take da sati 3-4 nan aka shiga fafutuka aka satomun wata aka kawomun, sukuma aka kai musu gawar Nafisat, nasakawa yarinyar itama Nafisat, abu kamar wasa yarinya ta'ki amsar Nono na kamar yadda Khalil ya'ki ansa shima, madara aka fara basa yarinya ta amsa kuwa tana sha........ Kowa yazo yakansha mamaki idan yaga wannan yarinyar,, sai ace ta canja kama sosai, haka naita basarwa nabar zancen ahaka.... Shekarar Nafisat 3 nasamu cikin Aisha nan nadage da addu'a dashan rubutu kuma, dan har 'kauyen mu nakoma lokacin ke kuma kina BUK kina karatu, acan nahaifi Aisha a'kauyenmu... Saida akai mata hud'uba, mukai kwana 4 sanan nace zan koma gidana, haka aka had'ani da addu'oin dazanna sha dana yarinyar kuma.. Anan gidana akai komai da komai na suna da wani budi'a, dan ankashe kud'i sosai, bayan suna naci gaba da zamana agidana inaci gaba da kula da yarana, amman kusan ko yaushe inashan tsegumun mutane dan sautari akan ce Nafisat da Khalil kamar tagwayene, kuma basa kama daku, hakadai nake basarwa dan banasan asan kan komai.... Wannan zancen dana gaya miki bandani da matar nan sai Allah daya haliccemu babu wanda yasan dashi, dan ko Yayah ban yadda tasaniba, koda yaushe ina nan ina 6oye sirrina.... Koni nasha mamaki ganin yadda yaran suke juyamun baya, kamar sun san bani na haifesuba, amman kuma nawatsar, dan ni badan komai nake zaune dasuba saidan dukiyar Mansur... Da da farko har tsoro nakeji kar asirina yatonu,dan ganin yadda kamar su dajuna ta 6aci kuma basa sona ko kad'an, sun fisan Imhal... Amman daga baya kuma na maze na watsar da "yan banza..... Lokacin danaje gidan marayu awannan lokacin naga yadda 'kannen mace da Namijin nan sukai girma suka zama manya kamar ba'a gidan marayu sukeba, kuma suna kama da ita sosai,kamar antsaga kara, idan kagansu atare bazaka ta6a cewa ba cikin d'aya bane dan kamar su ta 6aci sosai, dan kamar macen da Imhal ta 6aci sosai, saboda har farin Imhal da yanayin tsarin halittarsu iri d'aya ne... Amman tafi Imhal wayewama, sbd ita tayi makaranta Boko da islamiyya, sannan kuma sukan d'an futa yawon bud'e ido wani lokacin, har BUK take zuwa, sbd tanada baaira kamar Imhal, ita kuma ana ce mata YUSRA SHIKUNA ANA CE MASA YASIR 'kaninta, komai da komai tare sukeyi ita da 'kaninta ko makarantar BUK ma atare suke zuwa... Dan haka hankalina yatashi sbd makaranta dasuke zuwa kar su had'u da Imhal, sbd itama Mansur yaso sakata BUK na'ki yadda, nakasa na tsare nahanata zuwa makarantar..... Suna kuma nasaka LADII.... Mai kula da jariran gidam marayu akan tasa musu taka tsan-tsan ita da d'an uwanta dan Banason asirina yatonu..... Kallonta kausar tai da mamaki akan fuskarta tace "Lalle Biri yayi kama da mutum kice shiyasa suke wannan iskancin.... Kuma shiyasa basajinki duk lokacin da kike musu fad'a akan Imhal.. Allah mom kiyiwa yaran nan magana dan idan ba hakaba Imhal zata 6ata miki su.... Daddy man's e yashigo da mamakin furta wannan........ Najiya ba dai dai bane sorry π π please π my fan's*π€π€ Wayata tasamu matsala ne shiyasa amman yanzu kam alhmdllh komai normal.. π€ *_πΎ"DAN SHAYE SHAYE NEπΎ_* *{DRUNKARD}* *NA* *Sβ’Aβ’U* *πΉOMH teemerhπΉ* *βπ»MARUBUCIYARβπ»* *1-KADDARAH KOSAN ZUCIYAH* *2-"DAN HAKIN DAKA RAINA* *3-MATAR SOJAH* *And now typing* *πΎ"DAN SHAYE SHAYEπΎNE* *AND* *ππ»AM 16 YEARS OLD ππ»* *AND* *πSANADII...!!!π* ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ» ```For those Interested in yummy dishes, mouthwatering snacks, moist nd soft cakes.. don't worry cuties Delight have got you covered.. we specialize in snacks, dishes, drinks, festive cakes and small chop``` ```We also supply the above mentioned items for booking or order for Wedding, Naming, Birthday, Gifts,door to door, Restaurant & shops e-t-c``` _*π₯³ π₯³π₯³ do follow us
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40