Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,246 words 0 views Progress saved
Download Book

yanzu karfe nawa?" sadda kanta tayi kasa wani qututun bakin ciki ya tasoma mata ta kuma rasa dalilin daya sanya sam bata iya kuka idan yaci zarafinta sedai zuciyarta ta dinga wata suya me azababben rad'ad'i,da k'yar ta lalubo kalmar "kayi hakuri" tsaki yaja "Dama mana kullum kece ayi hakuri,idan kin isa gobema na sakaki aiki na baki lokaci ki wuce time d'in wlhy zaki d'and'ana kud'arki a hannu" batace kanzil ba taje ta dauko warmers d'in data zuba abinci aciki ta sakosu acikin wasu cute baskets guda biyu ta ajiye a gabanshi ta juya zuwa d'akinta cikeda qunci,tana zuwa tayi kiran umma akan zancen yarinyar dasukace zasu kawo mata me tayata aiki,sabida a yanda ta gaji yanzu bataji zata iya girka lunch and dinner kuma taga har haleemah tafara fita aiki tun jiya,bayani umman ta mata akan an kawo yar aikin khairiyya zatazo ta kawota anjima kadan...... *Bayan wata biyu* Rayuwa a haka taci gaba wa hafsat cikeda qunci da wahala,gashi duk k'wak'war mutum be isa yasan abunda ke damunta sabida dama batada jiki balanta na kace tayi rama,sannan kuma bazaka gane a fuskarta,tana zuwa school yanzu 200l suke kullum huda cikin bata shawarwari na kwarai take akan tayi hakuri kasancewar itace kadai aduniya tasan meyake damun hafsat,kuma har wannan lokacin shammaz baya kwana gidan hafsat indai abubuwan more rayuwane da kudade sedai ta baiwa wani amma sam ba magana me dadi a tsakaninsu wasu lokutan sam ko gayar dashi tayi baya amsawa,yau agajiye ta dawo daga skul tana fitowa wanka wayanta ya soma ringing,d'agawa tayi ganin sunanshi yace " Yanzunnan ki kawomun abinci yunwa nakeji" cikin takaici tamkar zatayi kuka tace "yaya yau ba abunda naci wlhy yanzunnan na dawo daga skul ko sallah banyiba dan Allah kace Aunty haleemah ta baka mana" wani mirmurshin mugunta yayi da har tana jiyo sautinsa yace " Ita d'inma yunwa takeji kuma yauma agajiye ta dawo ke muke jira ki bamu abinci kuma 1 hour kawai na baki" yana kaiwa nan ya ajiye wayar,cikeda takaici taje kitchen ta dafa musu sphagetty bolognese da orange juice tafita kaimu su haushi tamkar ta had'iye zuciya ta mutu,da sallama tashiga parlor din amma abun mamaki se numfarfashi take jiyowa juyawan dazatayi tagansu akwance suna kissing junansu shaam se shashafa leemah yakeyi yana mamatsa breast dinta kai abubuwan data gani sam bazasu fad'uba,wani takaicine ya taso ya tarnaqeta a wannan lokacin ji hafsat keyi tamkar ga kashe kanta har lahira,da kyar tayi karfin halin zuwa dininga tabajiye kayan ta juya,abunda yafi bqanta ranta shine yanda sukayi tammar basu ganta ba kuma sarai ta sani dukkaninsu ba wanda be sanda zuwanta ba wani abin ma har da gayya suke yinshi,wanda sosai ta kula Aunty haleema wannan surutun datakeyi danta gantane,a wannan ranar kuka hafsat ta kwanayi ko abunci bata iyaci,Allah sarki qaramar yarinya akace ana wata ga wata domin kuwa tun daga sanda hafsat ta gansu a haka se wani azababben sha'awa yake taso mata gashi wannan lokacin ne tashen balagarta seta rasa yanda zatayi a haka take danne zuciyarta tana adu'a Allah ya kawo mata d'auki... Ranar wata juma'a bayan sallan isha tashiga part din haleemah sabida tanasan ganin yaa shaam akan zancen bikin huda dayake wani satin za'ayi tana zuwa kofar d'kin tajuyosu suna iskancin nasu dasuke ihu sekace wasu maguna,juyowa tayi cikeda takaici anan taci karo da abinda tangamemen tv n dake parlor din ke haskawa wato BF,gabanta ne ya fad'i ganin me akeyi take taja baya se kuma wata zuciyar tace kindaiji ana labari amma yaune ganinki na farko,jeki ki kalla...da wannan ta tsaya ta kurawa tvn idon tana kalon masha'an da ake tafkawa rashin kunya iri iri,dakyar ta dakatar ta juya zuwa part d'inta jikinta har rawa yakeyi wasu abubuwa takeji suna mata yawo kasa haqura tayi da tambayoyin da zuciyar ta ta gaya mata ta zari key na motarta zuwa gidansu huda......kallon huda tayi bayan sun zauna a d'akinta tace bayan ta tattare nutsuwarta zuwaga hudan " friend mene ne sha'awa? Yaya kakeji idan kanajin sha'awa?" kallon mamaki hudan ta mata tace "Ban fahimcekiba?" sosa kanta tayi ta labarto mata tun farkon ganinta dasu shaam dakuma abu da ta gani ayau,ta qara da cewar "Huda wasu lokutan sena kasa bacci kinga har kuka nakeyi sena ringajin ina matukar sanjin abinda Aunty leemah keji tana sambatu idan yaa shaam yana mata wannan abun,kuma kinga yau danaga turawannan suna wannan abun sena ringa jin dadi sosai nima inaso kuma naji na rage yawan sha'awa shine nakesan siya nakuma ana yawan cewa haramun ne kallon wayannan abubuwan kuma yana saurin kashe ido?" cikeda tsoro huda tace "kinga hafsat wlhy ki kama kanki,inake ina kallon wannan abun?? Masu siyarwa ma karuwai kad'ai suka san inda suke masu browsing a waya kuma wlhy duniya tana kallonsu sosai da sosai,sa'annan na kula kinada karfin sha'awa sabida haka wlhy kine ki samu mijinki kice dashi kina buqatarsa inba haka ba wahala tana ganinji,kuma wlhy idan nakuma jin wai zaki siya wayannan mugayen films senaje na fadawa momy,ki barsu yaa shaam matarshi batada maraba da karuwa wlhy ni sunaso su b'atamun ke,wainikam ma tukunna tsaya sanar dani kina yawan adu'a da tsayuwar dare?? Kuma kina azkhar?" dan sosa kanta tayi tace "Gaskia bana,wani yi ina dai adu'a" "Toki riqayi akan mijinki da duk wata damuwarki kinji huda,adua yana da kyau da kyautata ibadu yawan yin azumin nafila da sallar nafila dakuma azkhar,kina yiwa qananan yara sadaka tunda baki rasa ba kinji,ki cire ranki da wannan mugun kallon indai ba wuta tsundum kikeso kije ba,kuma masu san kalllon wannan ma idan suka saba basa iya denawa,sekiga idan ba namiji a tare dasu suna yiwa kansu abubuwa da hannu kuma wlhy masifa ne Allah ma yayi alkawari. Azabtar da masu irin wannan mugun aikin,seki kiyaye kinji qawata" gyada kanta tayi alamar gamsuwa sannan tamata sallama tabar gidan,huda se tausayinta takeji matuka.......hafsat se tunanin rayuwarta takeyi da abubuwan ban mamaki datake ta faman gani arayuwa,a haka ta isa gidan cikeda damuwa,a harabar ajiye motocin gidan taci karo da yaa shaam tamkar bashiba,bashida niyyan koda kallonta ne balantana yamata magana,da sauri ta qarasa gunshi "yaa shaam ina wuni?" "Lapiya" ya amsa a taqaice yana shirin shigewa motarsa takuma kallonshi tace " yaa shaam magana nakeso muyi" batare daya kalletaba yace "Enhmm" "Dama nikam wai yaya banida wani haqqi a gidannan ne koda na kwana a part dinane yanzu kusan watannina biyar agidannan amma koso daya baka taba kwana bangarena ba atare dani" wani kallo ya wurgo mata ya murtuke fuska sannan yace "Idan tunanin kike kinada wani haqqi a kaina to kuwa kinyi babban kuskure domin nidai,ni shaam wlhy nafi kardinki sam *Bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane* bakida wani abu ajikinki ko a fuska daze gayyaceni kwana sashen ki,sa annan kuma bakida wani diri na ya mace dage gayyaceni zuwa shimfidarki,wlhy Hafsat bakida banbanci da namiji awurina,iyayenki sun cuceki domin nidai bazan taba iya furta kalmar saki agarekiba kamar yanda bazan taba iya makwanci dakeba sabida haka idan ma mafarki toki farka samni kam bana san mace sekace tsinken stintsiya se dare kamar wani daren yunwa,kuma me harma kinyi girman dazaki tareni da wani haqqinki wlhy kika kuma mun irin wannan maganar sena tattaki mara kunya fitsararriya haqqin uban wahe

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44