Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,266 words 0 views Progress saved
Download Book

yana sani ya miki haka,sabida yasan bashi bane yayi kisan so kekuma bakida wani hujjan dazaki iya cewa aa bayan an gama shari'ar,shawarata anan shine kije ki lallab'ashi" kallon dattijon tayi tace "Daddy dan Allah ka bashi hakuri akan ya janye wannan zancen nidai bana sansa,kuma idan su daddy sukaji nayi wannan shirmen bazanji da dad'i ba" kallon ta yayi shima yace "To hafat kije gobe zan sameshi da kaina,suna kokarin barin wurin kanwar sayyeed datazo hutu daga india ta shigo,se kallon shammaz takeyi,suna fita ta biyo bayansu da suruun ganin hafsat,a can tace da hafsat "T loojah waye wannan?" hafsa tayi sannan tace "Bros shaam my big bros kenan"murmushi tayi "hes handsome ina sansa kuwa?" zare ido hafsat tayi "Da gaske Baby?" "Ea mana da gaske wlhy" murmushi tamata tace "Idan zaki auresa shikenan sena gaya masa" dariya tayi tace "Zan aure sa mana ai yafiki kyau" haka dai suka rabu baby se matsawa take da zancen shaam,koda sukaje mota hafsat ta gaya masa dariya yayi yace "Ina ni ina ba indiya rufamun asiri" cike da zolaya tace "Kai yaa shaam banda boye boye fa,Allah ina ganinka se wani kallonta kake kana murmushi" dariya yayi yace "Ina wasa dake zan mareki wlhy" seda sukaje gidan sannan ya karbi numer din baby haka kawai yakejin yarinyar ta masa wannan zankadediyar yarinyar lolxx. Qememe muhammad ya kafe akan lallai baze janye qudirin saba kuma nanda sati daya zeyi auren danita,su daddy hankinsu ya tashi kowa gani yakeyi auren manufa ne na rama sunansa da aka nemi batawa zeyi. Waya kawai ya kira hafsat bayan magaribar ranar yace da ita ta sameshi a mota,tana zuwa ta shiga gefen me zaman banza ta gaidashi,fitilar motar ya kunna fiskarsa ba yabo ba fallasa yakai hannunshi ya daga hannunta dake ciwo,dan kara ta saki ya juyo ya kalleta itama d'in shi take kallo harta soma kwallah,dauke kanshi yayi sannan yace da ita "Har yanzu hannun nan be gama dawowa daidai bako?" batace dashi komai ba se hawaye,tausayin kanta takeji sabida sosai take tsoron muhammad,hannu ya saka ya share mata hawayen daya gangaro mata yace bayan ya dauke kanshi "Mesa kike kuka hafsa? Banasan ganin saukar tsadadden hawayenki yana zuba a banza kinji" sauke kwayar idonta tayi kasa batayi magana ba,ya sake cewa "Yanzu sanar dani me dame kike buqata,bazakiyi shagalin biki ba,ni zanyi dinner da reception sabida yanzu ne zanyi auren soyayya na kuma zab'ina" kallon shi tayi tana kuka tace "yaa muhammad dan Allah kayi hakuri" dagowa yayi a karo na farko "Hakurin me kike bani" kukan ta ne ya tsananta ta dukar da kanta taci gaba da yi,tafi minti talatin tana kuka amma bece da ita komai ba seda dan kanta tayi shiru,kanta ne ya soma sara mata ta bud'e mitar da nufin wucewa cikin gida yace cikin izzah "Nine nace dake na gaji dajin wannan zazzaqar waqar da kika sakani agaba kina reramun? Maza dawo kici gaba dayi harse ya isheni" kallonshi tayi cikeda mamaki idanta ya kad'a yayi jajir,yakuma cewa "Dawo mana nace ki rufe murfin" a hankali ta sako kafafunta ciki batare da tayi magana ba "Kalli idanki hafsat,duk yayi ja sabida bakyajin magana,nace dake kukan na menene amma kinki ji,kin zauna kina kuka sekace wacce ke rero waqa,idan ba so kike na sassab'a miki ba karna kuma ganin hawayenki wlhy,sanar dani yanzu tsakanin ki da Allah menene kikewa kukan?" sadda kanta tayi kasa tace "Auren ne bana so" kallonta yayi ya sakar mata murmushi "Banida maganin wannan gaskia,so kiyita kukan,shika d'aine damuwar kodai da wata bayan wannan?" sadda kanta tai a qasa tace "So nakeyi ka tausayawa rayuwa ta ka agazamun ka bar aurennan har nan da wata biyu na roqe ka yaa muhammad dan Allah" kura mata ido yayi na yan dakiku kan yace "sekin mun alqawari guda biyu,tsakaninki da Allah" kallonshi tayi amma batace dashi komai ba yace "Na farko sekinmun alqawarin bazaki taba kawo matsala me kamada kin fasa auren ba idan na qara miki lokaci,na biyu kuma sekin mun alqawarin bazaki sakeyin kukannan agaba naba sabida gaskia banaso yana batan rai" yawu ta had'iya tace "Abba haris ya sanar dani muhimmancin Alqwari sabida haka bazan taba fasa auren kaba,sedai idan kaine kace ka fasa,kukan ma zan kwatanta" gyada kanshi yayi yace "Nima ai alqawarin auren ki nayi,idan ko bazaki karya ba ni mezesa na karya, nasan muhimmancin alqawari ai,kije na yadda nanda watanni uku idan munada rayuwa se ayi auren" godiya ta masa ya tsare ta akan setayi dariya seda tayi dariyar kuwa sannan suka rabu,se dadi takeji...... Shaam ba kad'an ba yake jin yana san baby,sedai be sanar da kowa zancen ba se daddy kasance war shi abba haris har wannan lokacin fushi yake dashi,sedama hafsa ta saka baki yake dan sake masa kadan,cikin sirri kuwa aka shirya auren sa da baby tare da nasu hafsa,sam haleemah batasan wainar da ake toyawa ba,tunda taji hafsa zata auri wani shikenan hankalinta ya kwanta...... Hafsa gabaki daya ta rame tayi baqi,sam wani jarababben tsoron muhammad takeyi gashi abu mafi ban mamaki shine tunda ya tafi akan ya dage zancen aurensu be qara zuwa wurin taba kuma gabki daya ya dena kiranta,ita kuma duk sanda tayi yunqurin kiransa se gabanta ya fad'i, huda ce ta fad'o mata arai ta d'auki wayar ta kirata,komai da ake ciki ta sanar mata,hudan kuwa ta bata shawaran akan lallai ta kirasa,kuma ta basa kulawa as if tana matukar sanshi,wasan da yake so su buga idan ba ta wannan hanyarr ta biyo masa ba lallai akwai matsala,sabida ya shirya daukar fan sane,sosai tayi wa huda godiya koda sun dade basu hadu ba amma sosai suke hurda,huda yanzu tana germany itada mijinta. Cikin sanyin jiki kuwa tayi kiransa a waya,kamar baze daga bama,se can taji muryarsa me saukar mata da fad'uwar gaba yace "Hello" sanda ta d'anyi jimm sannan tace "Yaa muhammad Barka da yamma" gyaran murya yayi yace "Barka dai" a ta k'aice,jikinta ne ya qarayin sanyi tace "Dafatar kana lafiya" "Ina lafiya" itace amsar daya bata,runtse idonta tayi sannan ta kara budewa tace "Yaa muhammad ka gane me magana kuwa" kamar baze amsata ba yace "Na gane mana ba hafsa bace?" "Ea nice ya kwana biyu?" tafad'a cikeda jin zafin wulakancin data janyowa kanta "Lafiya lau,ya akayi ne?" dafe kanta tayi dayake barazanar rabe wa gida biyu tace "Dama naga kusan watanni biyu ban jika ba,shine nace Allah ya sanya lafiya" "Lafiya lau mana,me zan miki to? Ina auren Agreement ne zamuyi,sekace wata soyayya ke tsakaninmu dazanta damunki,kokuma daze kasance komai nawa sekin sani?" kasa hakuri tayi tace "Koda na kirak bakaji na ambaci soyayya ba ai,danni a wannan zamanin banajin ma akwai soyayya,kurin dai kamata ya sanya nayi kiranka sabida ni nasanta" sarai ya sani magana ta gaya masa,amma seya dake yace "Ni ai tun farko na sanar dake yanzu ne zanyi auren soyayah, kuma zab'ina bakijiba ne,kece bakya sona so meye zesanya na nanuqe miki?" jan dogon numfashi tayi sannan ta furzar da wani iska me zafi tace cikin wata rikitacciyar murya "Yaa muhammad" shiru ya mata tace "Why?" cikin dakakkiyar murya yace "Hafsatu manga yar sarki wacce maza ke rarrashi,koba haka taken yake ba?" ganin ze raina mata hankali ya sanya tankashe wayar ta ajiye,be kuma kiraba se

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44