Chapter 32
Chapter 32
lumshe ido yakeyi soft skin nata na daukar masa hankali sosai..... Da yamma yace da ita tazo su shiga bangaren zainab,ba musu ta caba ado suka wuce part din na zainab, suna zuwa parlor ya kalli wata yarinyar yace "Ki mata iso wurin zeezee" ya juya abinshi wani bangaren.....A zaune suka taddata ana mata gyaran kai,da alama wasune daga salon sukazo mata aiki a gida,har kafafuwanta ake wanke mata,kallo daya hafsat ta mta taji ta tsaneta,matar ma kallon sheqeqe tawa hafsat "Sannu" shine abunda tace dasu babu wanda ya koda kalleta acikinsu har masu aikin, duban su tayi tace Aunty zainab sannu" dagowa matar tayi cikeda isa tace "Kan mijin naki yakawoki gaidani be sanar dake ba'a gaidani a tsaye ba? Kuma ba'a saka ido acikin nawa sannan kuma ba'a kiran sunana hajiya zakice" kallonta hafsa tayi ta baki,ta juya abinta kawai aranta tace "qanin uwarki zanci ni kam wlhy,kajimun masifafgiyar mata,kinjawa kanki dani kuwa rashin mutun cine,gidan kika tarar... Kumun uzuri kaina ke ciwo [2/14, 9:00 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 28 A babban parlor na gidan hafsat ta had'u da muh'd kallanta yayi sosai ganin ranta duk a b'ace "Kaddai harkun gama gaisawar?" kallansa itama tayi "Ta dai gama wulakanta ni,Allah bazan qara zuwa wannan part d'in ba" tana gama fadar haka ta banki kofar tayi gaba abunta,binta yayi da kallo da kallo harta kurewa ganinsa,a ranshi yace lallai wannan yarinyar dama wai haka takeda fitina?....zuwa yayi kai tsaye d'akin da zainab take,Kallo daya yayiwa ma aikatan suka saketa suka watse,mutuqe fuskarnan yayi "Me kikawa hafsat ne?" kallon raini ta masa "Wacece hafsat kuma?" batare daya ce kala ba ya juya da nufin fita,ya gano raini zata kawo masa "Idan wannan shegiyar fitsararriyar yarinyar kakemun wannan kallon gwara ma ka dena,sanin kanka ne nan d'in gidanane kuma kowa dole ya girmama ni sabida nice babba" cak ya tsaya jin kalamanta sannan a hankali ya juyo ya kalleta "Gidan tane itama,ai auren mu aka daura bawai yar aiki na kawo miki ba,bakuma wai zama dadiro mukeyi da itaba,sannan da kike zancen girma aini ne me gidan idan baki girmama niba babu wanda ze girma maki wlhy,zaman lafiya nakeso kuyi da juna bawai shirmen kishi ba" miqewa tayi tazo har inda yake "J.A ni kake kallo kace dani wai kishi? Akanwa zanyi kishin kai? Danake sanka kokuma da aka gaya maka zaman jin dadi nake a gidan naka? Kaga wlhy idan ma mafarki kake ka farka,bazan tab'a kishin kaba sabida kasani sarai ba so araina" murmushi yayi dukda yaji zafin kalamanta sannan yace "Kamar yanda kikasan ni d'inma hakan take a wurina,nakuma auro matar so idan kin isa kem ki auro mujin so" Kallon mamaki ta masa sabida be taba cewa da ita baya santa ba se yau,qirjin tane ya doka lokaci d'aya taji ranta ya b'aci,kan tasamu bakin magana kuwa yayi gaba abinshi.... Koda ya dawo b'angaren hafsa kuwa a walk way ya sameta tanasham coffee,kallon shi tayi sosai "Mezaka ci dinner inaso zanyi girki?" kallonta yayi sosai "Bana cin abinda keda nauyi,so u think of something light" "Same here" tafad'a had'e da miqewa,sanda zuka parlor ya kalleta "Zan fita akwai wani abu?" matsowa tayi sosai kusa dashi ta hada jikinta da nasa,a kumatu tayi tsalle kadan ta manna masa kiss tace tana murmurshi cikeda rashin damuwa da abinda tayi "Ina maka fatan alkhairi,Allah ya sanya aje lafiya kuma a dawo lafiya" tana kaiwa nan ta juya abunta zuwa kitchn, yafi 3 mnts tsaye yana tunanin hafsat,tunda yake zeezee bata tab'a gwada yi masa adu'a ba akan wai ze fita ko wani abu daya shafi nasarar sa,wani sanyi yaji yana ratsa shi tamkar ruwan sanyi ayayin daka kwaso rana kake tsananin jin qishirwa, juyawa yayi ya fita amma sam bayan ya fitan seya kasa zama waje,duk motsin dazeyi kuwa zuciyar sa azalzalar sa takeyi akan ya dawo gida haka nan..... Shaam kuwa da maryam tun daren jiya suka angwance,ya samu nutsuwa me tsananin yawa a tattare da aurenta,yarinya ga tsananin riqon addini,domin kuwa ganin lokacin sallan asuba yayi shaam na bacci koda ta tasheshi sanda tayita mai wa'azi akan hakan,haleema kuwa batada labarin miyan da ake sha a niger da mujinta lolx..... Waffles sandwich ta musu da pizza ,se creamy la bees,sosai gidan ke tashin kanshi,wanka ta tsala tayi sallan ta na isha,daci ado cikin wasu riga da wando qanana pink and white masu matukar kyau,zokaga yanda heeps nata suka kwanta sosai gwanin sha'awa,kunce gashinta tayi ta taje shi zuwa baya yasha gyara se sheqi yakeyi haka ta zuboshi tamkar wata india,light makeup tayi tana fitowa sukaci karo a parlor,sanda ya lumshe ido ganinta kawai yaja numfashi, kamshin dayaji gidan nayi kawai ya wadatar balantana qamshin dayaji na ratsashi sanda ta fito, da sauri taje ta rungumeshi sosai ta kwantar da kanta a saman faffad'an qirjinsa ta furta a hankali "Sannu da zuwa yaa muhammad,ina fatan ka dawo lafiya" qamshin sumar kanta ne ya ebe shi besan sanda ya daura hannunsa yashafi gashin kan nata ba,yama kasa magana dama gashi ba ma'aboci son magana ba se kace ba lauya ba,dagowa da kanta tayi jin tayi lamo itama tanaso ta manta da muhammad ne fa,a shagwab'e tace "Yaa muhammad sekuma ka barni ni kadai,tun yamma fa ka fita" murmushi ya sakar mata me sanyi yama rasa me zece seya tsinci kansa da furta mata "Kiyi hakuri hafsat,wani abune ya tsaidani nima banso hakan ba,amma na kawo miki chocolate" wara ido tayi "Allah yaa muhammad? Thank you so much" ta qara rungumeshi sannan ta sakeshi ta juya,kallon duwawunta yake harta shige da jakar hannunsa da leda data karba,shi yaushe ma yataba samun arziqin a wani riqe masa jaka? Hmm lallai wannan auren yana ganin shine ake kira auren gaske kuwa.....A bed room nashi ma koda yashiga kamshin turaren wutan da aka saka dana freshner gaba daya ya banbanta,be taba kamshin daya kwanta masa araiba irin wannan,kallonshi tayi sosai,zuciyarta na dokawa sabida abinda huda tace tayi ya mata nauyi,haka ta daure sabida yanzu kam ta shirya yin wining wannan,taje kusa dashi botiran shirt nashi ta soma b'alle masa sororo yayi kuwa ita kam se murmushi take "Wanka ne ya dace dakai,a baho na had'a maka ruwan wanka da turaren wanka me tsananin kamshi,bayan kayi wanka se dinner kuma ko?" kallonshi tayi dasanjin amsar tambayarsa "murmushi ya sakar mata ya gyad'a kai alamar e,haka ta cire masa har wandon cikeda dauriya,ya dawo iya boxers de singlet ne a jikinshi, towel ta miqa masa tace "To zan jira kafito semu tafi tare" harta juya ya riqo hannunta yace "Sauran kayan fa hafsat? Su bazaki tayani ragewa ba?" murmushi tayi tace bayan ta kawar da kanta gefe d'aya "Yaa muhammad wannan ma aiya isa,dan Allah ka barni haka?" juyawa yayi zuwa toilet ba tare dayayi magana sarai ya gano nauyin sa takeji,wannan auren yana ganin shine mutu ka raba,shibesan ana wa maza gata ba har haka ai,a gurguje yayi wankan yana mamakin wannan kamshin da ruwan wankan keyi,haka yafito dagashi se towel halittarsa ta faffadan kirji ta kala,gaba daya jikinta ya mace sanda ta lumshe ido tana mafarkin ganin kanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44