Chapter 18
Chapter 18
shanyeshi tas,danma su momy sun tashi tsaye da adu'a,danma bazaki fahimta bane amma da kunnena naji tana magana da qanwarta harira akan naqasashin dasukayi,ko kad'an fa baya sha'awar mace wai sabida karya tuna abunda suka aikata,in taqaice miki dai kud'ad'e take karba a hannunshi da kadarorinsa baji ba gani nan da kika ganshi yanzu bashi da komai se asibitinsa shi d'inma sabida daddy yana tsaye ne akan asibitinsa da takardun wurin gaba d'aya,sedai tayita yawon banza nabin maza,ni a ranar danaji suna zancen aunmai asiri a ranar na sanarwa momy nanne fa aka d'an samu sauqi domin adu'o i da magungunan tsari sukayita nemar masa,gashi baya kula da ibadunsa da addininsa seda daddy ya tashi tsaye yanzu dai yaji sauqin rashin jin sha'awa duk nice yar rahoto akwai lokuta da dama da idan naje gidan nikan tadfasu suna wasaninsu wasu time ma har kwanciyar aure nake fahimtar sunayi dukda ni ban yarda da matar ba,yanzu abu daya ya gagaremu shine rabashi da matar sabida tsananin santa yakeyi fa,gashi ita kuwa komai ya samo seta qwace shi tatas ni na rasa wane irin kaine sa yaa shaam,gashi kumansu daddy sun saka yana adu'o i kema dai ki tayashi gaskia,yana cikin wahalar mace" nisawa tayi sannan tace "Allah ya kyauta musu,Allah ya shiga tsakaninsa da ita" kallon tausayi mero ta mata ganin tana kwallah tace " Nasani hafsat har yanzu kina san shaammaz ina rokon Allah ya daidaita tsakaninku" kallonta takumayi tana me sharar kwallan daya zubo mata tace " Mero bana fatan sake zaman aure da shaam,ko a mafatki naganni matsayin matarshi lallai senayi adu'ar tsari daga mugun mafarki had'eda yin sadaka, har kwanan gobe ina san yaa shaam sedai a yanda na fahimta sam wannan bashi bane mafita agareni,so tari zakiga abubuwan damu y'an adam muke so basu suke zamtowa mafakar alkhairi agaremu,yaa shaam ko banda asiri ba sona yakeyiba kuma tsana ta zahiri,nidai wlhy kinji na rantse miki nidashi har gaban abada,ina dai masa fatan alkhairi" jinjina kai mero tayi "To Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki" "Ameen" ta fad'a ataqaice sannan ta kwanta ta runtse idonta...... *Bayan sati biyu* Shaam durqushe agaban daddy da abba haris dasu momy harma hafsat wacce dominta aka tara zaman,kasancewar wai shaam yace ze aureta kuma ze barta harseta qarasa karatunta a india,kowa yayi shiru yana kallon ta tsuniyar daddy domin kuwa ilahirin jama'ar wurin kallon me bada tatsuniya suke masa harya idar,hafsat dai batace qala ba kazalika bata koda girgiza da zancen ba tunda taga yana mata bata dagawa be dena kiranba ta tabbatar cewar lallai da wata aqasa..... Kallon su Abba yayi yayi wani malalacin murmushi sannan ya kalli hafsat yace "y'ata nasan bazaki tab'a watsan qasa a idoba,ina sauraronki menene naki ra'ayin ni duk abunda kikeso shi zan miki" kallon shi ta dago tayi ido cikin ido suna had'a ido abba ya gano ta shaqa,ta nisa sannan tace idonta a qanqance " Bazan sake fad'ar abunda zan fad'a a yanzu ba,abu d'aya nake san kusani shine,dukkanin abinda kukaji zan ambata yanzu babu wasa kokuma wani abu makamancin raini aciki,kuskurewa qa'idata d'aya ka iya janyo lalacewar komai musamman idan na aikata abinda zan aikata idan aka kuskuremun qa idar" shiru ta danyi kowama yayi tsit taci gab "Ni bazawarace ba budurwaba kuma a tsari na addinin musulunci nice dakaina nake da haqqin zab'awa kaina mijin aure a yanzu,bazan lamuncewa zab'in kowa ba tsarin addinina zanbi, kuma wlhy summa tallahi bazan tab'a komawa auren shammaz ba,ko gawata akayi kuskuren daurawa aure da shaam ban yafewa wanda yayi ba koda mahaifinane kuwa, idan aka qarabtayarmun da zancennan wlhy na sanya qafa nashiga duniya nida gida har abada,idan dame tantama kuma ya gwada tada zancen kuga ikon Allah, ku tambayeshi kuji dalilansa naqin zama dani idan dai basankai kuke sanyi ba ai bazaku qara cutar saba kamar yanda kukayi abaya,da bakinsabyace dani ya tsaneni!! An cuceshi da aka had'ashi aure dani,da bakinsa gashinan zaune ya kalli tsabar idona yace dani Babu tabinda ze zauna da mace bushashiya ni menakedashi,mena ajiye ajikina ina fama da qasusuwa,da bakinsa ya kalli tsabar idona yace dani na dena mafarki ze tab'a had'a shimfud'a da banza irina bushashiya,ashe nidin nan icce ce a idonku,ashe bajini a jikina,ashe qarfeceni bansan dadin mijiba,idan har baku sani ba toku sani yau nasha baqar wahala rayuwa da miji fanko,ina da aure an kawar dani sabida gudun wannan yaso ya cillani gayinta banda a litttafan hausa da fina finai ina kuka tab'ajin anyi aure shekara daya amma namiji be taba koda riqe hannun matarsa ba duk sanda kuka ga jikina da nashi ya hadu tofa duka ne,kuma da bakin sa ya sanar mun cewar bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine ina makauniya zan dauki kaina inkai daidai bakin rijiya,sabida bana tsoron afkawa aciki,toku sani ina tsoro!! Na rantse da Allah kona rasa mujin aure bazan auri yaa shaam,ninan ni kadaice na san baqar wahalar danash a hannunsa,a ranar dana samu matsala dakaina na roqeshi akan waze aureni idan yasaken ya taimaka ya maidani gidansa,bud'ar bakinsa se cewa yayi dani be soni sanda nake da lapiya ba se yanzu dana dawo nakashashiya,bayan shine silar lalacewar rayuwata da quruciyana kowa namun kallon bazawara!! Kullum zancensa d'aya ya tsananeni yana tunasar dani bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine yanzu ze bazamo kome ya gani ajikina oho!!! Ko kuwa dai yanzu zan iya wasa a bakin rijiyar tunda naqasa ta tafi oho!!! D'aukacin mutanen parlor dinnan ku shaideni ranar dazaku qara zuwamun da zancen komawa gidan shaam kun rasani kenan har abada!!!!"" Jikin kowa yayi sanyi yayinda abba haris ya zabgeta da albarka,shaam kuwa ya saka kuka wiwi wai ta taimaka masa....to phaaaa.. Zaune suke idata Uncle say a babban parlor na gidan daddy se shagwab'a takeyi wai bazata koma india ba,shi biyeta yakeyi ya saba haka sukeyi da qannenshi sesu sakashi gaba abu beje yazo ba su saka masa kuka "Haba dan Allah uncle say,idan kuma na tafi bazan qara ganin kaba fa" murmushi yayi yace "Dan Allah hafsat ki dena rigimarnan,bakya ganin khairi batayi haka ba? Ke komai se kace jin jira,komai rigima komai kuka,na sanar miki akwai wani coirse dazanyi a india na shekara daya kuma nxt montj zanzo,tunda kunfara school seki koma kafin nazo" turo bakinta tayi waje " Ni dai jiranka zanyi bazan iya juran rashin ganin kaba na tsawon wata ni yanzu im used to you over,i just cnt imagine my self with out you around" Murmushi ya sakar mata "Nima haka beauty amma ya zamuyi yanzu idan namiki aure ya zakiyi? Sekice dani zaki tafi" B'ata fuska tayi "Ni nace dakai zanyi wani aurene,ni bazan taba aureba aje ana dukana,maza basuda kirki wlhy" janyo hannunta yayi shi yarigada ya saba da al'adar indiyawa yace "Beauty banasan wannan mummunan tunanin dakika sakawa kanki,sam be dace kina cewa bazaki qara aure ba,adu'a zakinayi Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki tsakani da Allah" kallonshi tayi ido cikin ido tace "Ni koba wannan ba bazanyi aureba,idan nayi aure mijin baze bari ina ganinka kullum ba,nikuwa that will be d worst thing that will happen to me ever,i just cnt imagine my self living a day with out u" murmushi ya sakar mata yana nazarin kalamanta sannan yace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44