Chapter 16
Chapter 16
tantance fuskoki,ganin batayi magana ba ta qura masa ido ya sanya yayi gyaran tsayuwa yace "Beauty sannu kinji?" murmushi ta sakar masa sannan hawayenta ya silalo da gudunshi tace " Thank you,thank you so very much uncle say,may Allah bless and reward u abundantly" hannunta ya riqe sannan yace yana fad'ad'a fara'arsa " Beauty nafiso inji kina fad'an Alhamdulillah shine ya baki lapiya Allah,soni nawa taimako yazone ta hanyarshi" murmushi tayi amma ta kasa tsaida hawayenta,hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan yace "Beauty kiji sauqi gaba d'aya da sauri so nakeyi na kaiki yawo,watannin da kikayi bakya gani duk sekin rama wannan kallon" murmushinta ta fad'ad'a har fararen haqoranta suka bayyana,sannan tace "Uncle say i so much like you,apart from my parents ur d only person nasan yana kulawa dani tamkar blood d'aya yake yawo ajikinmu,bana fatan abunda ze raba zumuncin mu har abada" murmushi kurun yayi haka kawai ya tsinci kanshi da matukar jin dad'in kalamanta "Ameen ya rab" ita kad'ace kalmar daya tsinci harshensa da furtawa,kan wani ya kuma yin magana har su Abba sun afko d'akin.. Da sauri Abba ya rungume hafsat jin ta kira sunan sa,suka yita kukan murna sam barka abinsu. *Bayan sati biyu* Hafsat gaba d'aya jikinta yayi saiqi har yawo sun zaga garin ba laifi,sabida har shirin komawa sukeyi,gaba daya qannen say mata suna matukar qaunar hafsat sun shaqu da ita itada khairii ba kadan ba,har roqa sukeyi wai su zauna dasu india suma suyi karatu dayake dukkansu sunajin hausa sabida babansu dabhausar yake musu magana mamansu kadai ke musu yaren india kan tarasu kuma itama tanajin hausar,koda Hafsat ta roqi Abba haris akan abarta anan tanasan tayi karatun low mmbe hana suba har khairii yace su zauna atake aka nema musu gurbin karatu inda dukkansu suke karatu a jami'a d'aya se dai hafsat low take karatu yayinda kharii ke karantar business admn..... *NIGERIA* Zaune ake a babban parlor ana hirar dawowar yan india daddy ba qaramun dad'i yakejiba ganin cewar hafsatunsa harta fara sabon karatu,sabida anan niger tamayi missing semester d'aya kowa se murna yake shi sam yaa shaam hankalinsa baya wurinsu sabida damuwarsa ma ta isheshi sam baya iya tab'uka komai a shinfid'ar matarsa sannnan kumanya kasa gane dalilin daya sanya komai zatayi baze iya yi mata magana ba,tazo tayita karb'ar kudade hannunsa amma baya iya cewa da ita kanzil,daddy ne yace " Shaammaz kaji qanwarka ta samu gurbin karatu a india,tana can mumbai tana sha'ani abinta banji ka sanya albarka ba" Dan tab'e baki yayi sannan yace "ni anawa tsarin banason banso yarinya taje wani qasar karatu,kawai dai ina mata fatan alkhairi,banza kowa ya masa aka ci gaba da hira,shi dama abba baya amsa koda gaisuwarsa ne...... Kwance hafsat take tana karatu Dr.say ya kirata, "Uncle say ina wuni" kwaikwayar maganarta yayi sannan yace "Duk wannan ladabun baze hanani zazzanekiba,an gayamun bakyashan magani mesa haka?" shagwab'ewa tayi "Allah ni uncle say ka yarda dani ina shan magani,sameera fa qarya takemun" "Naji amma mesa bakya shansa akan tsari,Allah idan kukayi hutu punishment dinki shine bazakizo Nigeria ba" kukan shagwaba ta saka masa dakyar ya hakura sannan sukayi sallama.... Mom Nu'aiym [1/25, 8:54 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* *wannan shafin nakine kyauta Ta ma'aiki,inajin dadin comment naki Allah yabar zumunci* 15 Tun bayanda su hafsat sukaji labarin auren uncle say sataji gaba d'aya duniyar ta mata qunci tayaya ma uncle say ze hanata zuwa hutu,ace bikinshi sukutum wai bada ita za'ayi yishiba,gaskia abu beyi ba kam wannan ya sanya taketa fushi dashi,shi kuwa ya kafe akan bazata zoba wanda wannan umarni ne na abba haris,bayaso ya hanata da kanshi amma sam bayaso tazo ta sake tada hankalinta akan shammaz gashi ance su kula sabida matsalar ta na heart,haka akayi bikin tanata qunci batazo ba,gashi su sumayya da suhaila duk sun tafi itada da khairii ne kawai shekara d'aya kenan rabonsu da gidan....... *Bayan shekara Biyu* *Takun saqa* Ba kad'an ba hafsat kejin dad'i zatazo hutu Nigeria bayan shekaru biyu cur datayi harma da yan watanni bata Nigeria,tsakanin itada khairii bazakace wa yafi wani zumud'i ba,koda jirginsu ya sauka hafsat ji takeyi tamkar ta bangaje dukkanin mutanen dake tafiyar yangarnan ta sauko,sabida ba qaramun missing gida tayiba, A yangace yangar dabata san sanda ta koyeshiba take tafiya,ba shakka wanda yasan waccen siririyar hafsat kamar ka busata ta fadi baze yarda cewar wannan data tara mula mulan abun zama da iyayen heeps tare da doka dokan breast cewa itace hafsat d'in daba,sanye take da straight skirt na roba light blue da top red wacce ta d'ameta takuma bayya no ainahin surar da Allah ya mata,ga wani tsukakken flat tommy da bazaka tab'a yadda cewar mamallakiyar wannan booties ne dashiba,tamkar arayuwa ba'a saka masa komai aciki,sanye a idonta dan qareren qaton shade ne me kyau,a saman kanta sirirn fayafine ta yane kanta dashi,tun daga kan goshinta har girar idonta gargasa ne baqae wuluk se sheqi sukeyi,lallai hafsat tayi kyau, takuma qara girma side bag ce me kyau kalar ja rataye a kafad'arta yayinda a k'afarta take sanye da wages blue masu kayu matuqa, khairii ma irin shiga d'aya sukayi kalace kawai ta banbata domin kuwa ita pink and white tayi,sunyi kyau matuka,Abba haris suka fara hangowa inda basuyi qasa a gwiba suka zarce wurinsu suka rungume shi suna murna, "Abba kai kad'ai kazo ina su momy?" hafsat ta tambaya cikeda k'osawa,murmushi yayi yace "Nine nace kowa ya zauna ba wanda zw biyoni duk suna gidana ku kadai ake jira yau daddy ma na gayyata can sabida yara nema zasu dawo" murmushi tayi sukayi gaba abunsu zuwa mota.......murna sosai akayi domin zuwansu anyi girke girke na masifa masu matukar qayatarwa da dai hafsat nak tayi kasancewar ta jima rabon dataci abuncin gida,su momy suka wuce ita kuwa tace bazata ba se gobe,da dare bayan sun huta wayanta ya soma ya ringing tana dubawa taga sunan uncle say,qin d'agawa tayi gaba d'aya ta turo baki tamkar zatayi kuka kuma kamar yana ganinta,kallonta khaiirii tayi "Uncle say nefa ki d'aga mana" harara ta wurgo mata sannannta tsiyayar da hawayen datake ta faman tarewa "Bazan d'agaba ai cewa yayi dani shine ze dakkomu daga airport shine be zoba kuma na kirasa yama kashe wayan" murmushi kawai khairi tayi indai fad'ane dama tasaba ganin sunayi batanan sanda suke shiryawa abunsu.... Washe gari yamma liqis hafsat tace da driver ya ajiyeta gunsu momynta,haka ta shirya ta wuce yauma kalar dressing na jiya tayi sedai wannan karon lemon green and orange tayi ga alama wannan dressing shine d'abi'ar ta yanzu,a baking katafaren gate d'in gidan tace driver ya ajiyeta yayi tafiyarsa,ba komai a hannunta se wayarta kirar iphone 7 da side bag lemon green dake rataye a kafad'arta,koda ta shigo gate d'in gidan wayarta take dannawa,acikin qatoton madubin idon dake idonta,murmushi takeyi har fararen haqoranta suka bayyana ganin khairii na mata iya shege kan whatssapp akan tafiyanta gida, jitayi ance "Hafsat ce" D'agowa tayi fuska a had'e jin muryar me mata magana tana taunar cingam dake bakinta,batace dashi kanzil ba ta wuce taci gaba da tafiya abunta,mamakinta ne ya kama shaam ganin abunda ta masa,se
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44