Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,256 words 0 views Progress saved
Download Book

nisawa yayi ya soma gano da babbar matsala sabida wlhy ko zainab seta fuskanci hukunci "Ke hasano sanar dani ina dayar madarar da sauran wacce suka sha jiya?" gyaran zama tayi. "Suna nan acikin fridge har sauran rabin ma" "Jeki kawon su yanzu,ke kuma karime karbo kizo muje wurin zeezee din" Da sauri sukayj yanda yace.... A tsaye suke ya miqa mata madarar yace k'arbi kisha wannan,saqon dana baki ki kaiwa hafsat ne,tasha kuma ya mata aiki sosai,inda kika taimaka ma har Ammy tasha kuma duk sun kamu da sharrin ki,se kema kisha yanzu in ga ko zeyi aiki a naki jikin" zaro danta tayi waje,cikin tsiwa tace "Wlhy bazan shaba,kuma Allah ya sanya cikin ya zube gaba daya" be fahimci kalamanta ba ya sanya hannu ya kwasheta da kyakyawan mari yace cikin qaraji "Shine zaki zomun da hauka,shine zakiyi poisoning matana? Meta miki zaki kashe tq? Yanzu gashi sabida wani gruges na banza zaki mun hauka ki hada har uwata,rashin hankakin naki har ya kaiki ga tunanin yin kisan kai?" zare idanta tayi jin ya ambaci kisa tace "Nashiga ukuna ni zainab wlhy ni ban saka maganin kisa anan ba,na zubewar ciki ne kawai na saka mata" wanketa yayi da wani marin "shine zasuna riqan fitar da kumfa a baki,shine likitoci zasu tabbatar cewar deadly poison ne? Kuma inna zubar da cikine ya akayi yayi affecting har Ammy? Idan na zubar da cikine kema karbi kisha muga yanda ze miki" kin sha tayi se kuka da take tana rantse rantse akan na zubar da cikine, a fusace yace "Zanje da madarar nan aduba wlhy sena hallaka ki idan hakanne" yana barin dakin ta janyo wayarta ta kira qawarta data kawo mata maganin datake iqirarin na zubar da cikine wato *HALEMAH SHAMMAZ*. Mom Nu'aiym [2/25, 9:03 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 36 Da madarar yaje asibitin,gwajin farko aka tabbatar itace,hafsa tasha baqar wahala sabi acikinta aka yayyakan yaron cikin kusan 6 month ya soma girma sosai, haka aka ciro mata shi,kuka kam tasha shi,muhammad kuwa be duba dan gantakar dake tsakaninsa da zee ba ya sanya aka damqeta zuwa police station daga ita har qawarta haleema kuwa...... Ammy taji sauqi ba laifi sedai kam ita nata yazo da gaddama sabida hawan jininta ya tashi sosai kuma yaqi sauka,sedai adua,a bangaren hafsat kuwa kwance take tana sharar kwallah,ba wai wahalan datasha ba mutuwar yaron cikinta, sosai ta qwallafa ranta akan wannan cikin, tana nan khairii nata mata sannu sega muhammad nan, ficewa sukai gaba daya suka bar musu dakin, da sauri ta miqe zaune,shi kuwa ya kama hannunta ya riqe tausayinta ya sanya ya kasa maganq,rungume shi tayi tace "Yaa muhammad nashiga uku nq" tsamm ya qara matse ta ajikinshi yanajin tsananin tausayinta da sabuwar kaunarta na ratsa ilahirin jikinshi "Noo plss hafsat stop saying that baki shiga komai ba se alkhairi inshaa Allah sharrin su ze koma musu ne ki barsu kawai" ita batasan meya faru ba ta dago kanta ta kalleshi "su waye yaa muhammad?" be damu ba ya bata amsa "Su zeezee mana itana da matar yayanki haleema,sune sukayi poisoning naku keda Ammy da madarar da kukasha,kuma wlhy tunda suka mun asarar baby na sesun gane shayi ma ruwane wlhy" kasa magana tayi tsabar mamaki poison kuma? Ta nanata a ranta,ga mamakinta kuka taga muhammad yanayi sosai kuma,kasa yin kukan tayi ta soma bashi baki "Hafsat tsabar zainab batada hankali zatayi kisa,kisan ma wai mahaifiyata data haifeni da kuma matana mafi soyuwa agareni da yaron danafiso tunkan zuwanshi duniya,yanzu gashi tamun asaran shi wlhy sena hukuntata sena gane cewar doka tana aiki har cikin gida" Itadai bata iya magana ba sam. Bincike ya nuna cewar ita zainab batasan guban na kisa bane,haleema ne takawo mata a zuwan na zubar da cikine kawai,sannan batasan cewar tare da Ammy za'a shaba,ita kuwa haleema tasan na kisa acewarta tunda take da shaam hafsat ce take takura ta,yanzu dan taga ita bazata sameshiba shine ta hadashi da wata can ake wulakntata ita, tunda ta gane mijin Qawarta ne hafsat ta aura se kawai ta dinga zugata akan su hallaka hafsat,ganin bazata yadda da kisa ba ya sanya ta bullo ta hanyar a zubar mata cikin ashe fa dama kisan ne.......hafsat sun dawo gida duk sun samu lapiya,anan kuwa aka soma zana court inda atake sanida duk sunyi confessing aka yankewa zee zaman gidan kaso na wata uku ko tarar kudi naira dubu dari biyar yayinda aka yankewa haleemah zaman gidan kaso shekaru ashirin, tun a cotun ta haukace ta soma sambatu kuwa iri da iri, kamar wata zautacciya duk wani mugun aiki datakeyi haka ta dinga fada kuma tunkan ajata zuwa gidan kason Allah ya amshi ranta acikin dubannan mutane,wannan abin ya daga hankalin zeezee yayinda mahaifiyar haleema ta haukace a take ta wurgar da zani tayi waje,shammaz kam beso hakan ba sam yaso yaga tuban haleema ta koma ga Allah amna yazeyi haka Allah ya tsara tata kalar rayuwar,yayi kukan abubuwan data masa musamman daya kasance tana bin maza wanda ya dade yana zargin hakan, Zeezee kuwa ba irin hakuri daba ta baiwa muhammad ba amma yace sam baze hakuraba ya saketa saki daya...... Sosai hafsat ta tsorata da abubuwan dasuka faru, kallonta muhammad yayi sosai yagano tun fitar sa tana wurin daya barta,zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta yace cikeda kulawa "Hafsat dan Allah ki mayarda komai ba komai ba,inshaa Allah zaki samu wani cikin,kuma ire iren su haleemah bazasu sake samun galaba akanki ba,Allah baze bari ba kinji" kwantar da kanta tayi saman qirjinsa tace "Ba wannan araina yaa muhammad tsoron duniya kawai nakeyi wlhy,ni a rayuwa mena yiwa haleemah dazata bini da wannan sharrin ban tab'ajin banji zafin mutuwar koda kiyashi ba kamar yanda sam banji zafin mutuwar haleemah ba, abubuwan data aikata sun firgitar dani ace arayuwa mutum ba Allah a ranshi? Baya tsoron mutuwa baya tsoron had'uwarsa da Allah sam,baka gudun cin hakkin mutane ka mayarda neman maza kamar shan pure water da aurenka,sata sekaje beran masallaci, yaudara ba komai bane,ni naji tsoro wlhy" kallon sosai ya mata "Nagodewa Allah daya bani ke a matsayin mata,yanzu zan qara da wani mamakin akan halayyar dan adam, zainab da kika gani yar aminin mahaifinane tana soyayya da wani saurayi aka ce seta aureni suna matuqar san juna kamar me,nima kuma inada budurwata sunanta khaleesat, kinsan yan siyasa suna dasan auren hadi tsakanin yayan masu kudi haka mahaifina ya dage akan sena auri zee, nasha zagi a wurin zeezee ba iyaka azatanta santa nake amma duk bana kulata,sabida mahaifina daya bani amanarta,saura kwana biyu daurin aurena da ita taje gun wannan saurayinta,ina zaune khamal yamun waya akan ya ganta hotel ita dashi sun shiga daki,mukazo nida shi a mota muka kwana haka kuwa se 10 na safe suka fito atare daga dakin ita bata ganni ba amma nina ganta sarai, haka na roki kamal akan ya bar maganar iya mu, aka daura aurena da zeee, har mukayi wata daya da sati biyu ban taba kwanciyar aure da ita ba,bansan meya sanya zee ta kawomun kanta ba sedaga baya,bayan ta haihu na fahimci

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44