Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,268 words 0 views Progress saved
Download Book

wani yanga takeyi yayinda duk taku d'aya se yalwataccen qugunta yayi magana,ko kallon inda yake bata qara yiba tayi gaba,sosai tabashi mamaki ya had'iye wani yawu me d'aci a rayuwarshi yace "Lallai idan kika zomun da raini sekin gane kuskurenki" ... A parlor ta tsaya suna gaggai sawa dasu momy da daddy,daddy kallonta yayi "Lallai kulelen daddy girma yazo miki kinga yanda kika dawo kuwa,kuma yanzu naga ba rigima" murmushi kawai tayi batace komai ba, shine ya kuma cewa "Banga jakar kayankiba na zata zakizo gidane ai" sosai kanta tayi tace "Daddy nan gidan ba kowa ni gobe zan koma Allah kuwan" "Ni bazan takurakiba kulele so karki damu kinji" Miqewa da zummar zuwa kitchen ta hadaw onion samosa da ta zame mata jiki,kullum setaci ko a can dama abuncin suce,kan taje ko ina sega yaa shaam ya shigo ko kallonshi batayi kuma kowa ya kula da hakan shi kuwa ya qurawa yalwataccen gashinta ido harta b'acewa ganinsa,zama yayi kusa da daddy cikeda fusata yace "Daddy kagan kuwa hafsat wulakancin datamun ko gaisawa mafa batayi daniba ko kallona ma batayiba" murmushi daddy yayi yace "kayi hakuri zan mata magana,wataqil fushi takeyi dakai har yanzu" bece kanzil ba harta dawo d'auke da plate dinta na onions samasas ta zauna kusa da momy "Mommy zakiji samosar albasa zallah,da dad'i wlhy" kallonta momy tayi ta d'an b'ata fuska "Hafsat mesa baki gaida yayan kiba,ko baki ganshi bane?" cikeda rashin kulawa tace "A a momy waye kuma yayan nawa naban gaidaba,nina gaisa da duk wani jinina dama wanda ba jinina ba a gidannan kumafa kina kallo" "yayanki shammaz nake magana,hafsat" d'an tab'e baki tayi ta yamutsa fuska "Hmmm lallai ma mommy,bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ina nayi matsayin dazan gayarda d'anku,kuma ni wlhy Allah ya kiyaye ya zama yayana" mamakin kalamanta kowa keyi daddy yace cikin fushi "Hafsat kinad hankali kuwa,a gabanmu kike fad'ar wai shammaz ba yayanki bane" turo baki tayi ta soma hawaye sannan ta miqe ta tattare mayafinta ta yane kanta ta wurga wayarta ajaka ta shuri takalminta,wlhy indai kukace zakuna takurani akan gaida wannan wlhy bazan qara zuwa muku ba,ku tambayeshi mana yaya mukayi dashi,ai mun raba duk wata alaqa tsakanina dashi to meye kuwa ruwansa dani" tana kaiwa nan tafito daga main parlor d'n tana kuka, Ganin Uncle say a tsaye jikin motarshi ya sanya ta qara turo baki takuma qara sautin kukan datake har tana doka kafarta a qasa,da sauri yazo kusa da ita "subhanallah Beaty,.eya sameki kike kuka?" sauke hannunta tayi tace "Bayan su daddy da mommy ne wai sena gayar da shammaz,ni kuwa alqawarin nayi har abada bazan kuma masa magana ba,ni Allah bazanma kwana musu ba" hannunta ya janyo "Hafsat ur 19 fa,why are u still behaving so childish? Gaskia banaso kuma zamuyi fad'a,meye idan kin gayar da yayanki?" turo baki tayi tace "Uncle say bazaka ganeba banaso ina tunaninshi kuma banso ina ganinshi,tsanar kaina nakeyi kuma wlhy zuciyana yanamun zafi ko tunasa nayi,uncle say plss karkace na gaidashi kaji" tausayinta yaji ya sani sarai har gobe hafsat tanasan shammaz,kuma yasani zuciyarta a cunkushe yake da tsanar abubuwan da ya mata,kan yace wani abin daddy da shammaz sun fito,gaisawa yayi dasu yayinda hafsat tayi kici kicin,bayani daddy ya masa akan fushi zata gida,lokaci daya ya hade fuska yace "Hafsat kinsan shiyasanya na hanaki zuwa hutunnan Allah idan baki nutsuba nida kene,kina girma amma bakya wayau maza ki koma ciki" turo baki tayi tana hawaye "Uncle say bamu mafa gaisa kuma its been long,dama ba wurina kazo ba?" "Gunki nazo amma yanzu ammun waya yayarki tana labor so zanje gunta" matsowa tayi kusa dashi ta soma doddoka k'afa "Allah ni Uncle say sena bika dama tunda nazo banga Aunty ba" girgiza kanshi yayi a gefe d'aya kuma yana jinjina girman da hafsat tayi da kyau,se d'an karen wawta data qaro,kuka kuwa ya saba kullum ne ko a waya se an masashi akan zuwa gida..... Mom Nu'aiym *Babu tabbacin cewar gobe zaku samu,se yanda Allah yayi ina busy ne sosai kwanakinnan* [1/28, 8:22 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* * A shafin daya gabata,munyi kuskuren number,amaimakon 14 se muka saka 15,idan muka ce zamu dawo baya da matsala wasu zasu rikice sabida haka zamu ci gaba da 16 inshaa Allah,nagode.* 16 A asibiti kuwa uncle say gaba daya hankalinsa ya tashi jin za'a shiga da suhail cs sabida ta kasa haihuwa,sosai hankalinsa yaqi kwanciya,yakasa zaune ya kasa tsaye shi kuma ba b'angarnsa bane gefen haihuwa,Ganin Dr. Hafiz ya fito daga thereter room ranshi a b'ace ya sanya qirjin say ya doka da k'arfin gaske,yana fatar ba abunda ya faru kenan ba, Gwiwa a sace Dr. Hafiz yazo kusa dashi kallanshi yayi sannan ya d'ora hannunshi a kafad'arshi ya kura masa ido,hannun nashi Dr. Say yabi da kallo sannan a hankali ya mayarda dubansa zuwaga Dr. Hafiz amma beyi magana,cikin dakiya hafiZ yace dashi "Im so sorry to say we lost both the mother and the child,tunka mufara thereter d'in Allah yayi ikonsa akansu kayi hakuri abokinaHaka Allah ya tsara"Kasa koda motsi yayi idonshi sun qeqeshe sunyi jajir amma ba alamun ruwa acikinsu,ihun da hafsat ta kwallah ne ya dawo dashi duniyar tunanin dayaje,da sauri sukayi kanta se gunjin kuka take wayyo ita Allah Aunty suhaila, bata taba ganinta ba se a hoto kasancewar wancen lokacin dasukayi shiri sosai ita bata gani kuma tunda ta warke bata zoba amma sunyi wata irin shaquwa mara misaltuwa kullum se sunyi waya yafi a irga,ko jiya sanda sukayi waya,yauma da safe haka, sosai hafsat ta gigice dajin zancen Dr.Hafi,say shi yama rasa me zeyi Dr.bafiz ne ya lallashinta azatansa qanwar marigayiyar ce, A haka ya lallaba yayiwa mahaifinshi waya da kuma nata mahaifin kasancewar dama basusan ankawota asibiti ba,mutuwar suhaila ta rikitar da Dr. Say sabida yana matukar qaunar matar tasa,sannan be tab'a kawo mata mutuwa ba ko kan yafita da safe lapiya lau ya barta kuka yake tayi tamkar wani qaramun yaro har akayi sadakar uku,hafsat ma gaba d'aya ji take duniyar ta mata duhu,batajin dad'in komai,haka dai dole kowa ya haqura wanda ya fisu san baiwarsa ya dauke abarsa gaba daya....... *Bayan sati uku* Yaa shaam zaune a parlor din gidansa kusa dashi haleema ce take ta faman taunar cingam sekace abun dole, shi kuwa gaba daki daya hankalinsa baya kan kallon dasukeyi yana gun wannan hafsat da gaba d'aya tun zuwanta ta sauya masa tunani,be tab'a zata akwai ranar da tunanin hafsat ze hanashi sakat ba,anya kuwa bazece da abba yayi nadama ze maida itaba,kai idan yaje gun abba baze saurareshiba wataqil gwara ma yaje gun daddy,da wannan tunanin yaje ya kwanta.... Niko nace hmm ubanka zakaci d'anye wlhy.. "Mero ni kuwa wai in tambayeki?" kallon hafsat meron tayi "Ina jinki mana Allah yasa na sani" gyaran zamanta tayi ta tattare nutsuwarta gun mero tace "meyake damun yaa shaam? Naga duk yabi yayi baqi ya rame,kuma ya rage kiza kiza" kura mata ido mero tayi na yan dak'k'u kan daga nisani bayan ta gama nazarinta ta nisa tace " kaidin mace ke d'awainiya da shaam hafsat,wlhy haleema tagama da yaa shaam ta

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44