Chapter 11
Chapter 11
so tamkar sune suka haifeka shine tsabar mugunta yarinya ko 17 bata hada ba zaka hadata da ciwon zuciya mugun banza" wurin hafsa suka koma dakyar sadiq ya tattaro nutsuwarsa ya shaidawa hafsat komai cikeda rarrashi da nuna mata hanyoyin dazatabi tunda abin beyi nisaba,sosai hafsat tayi kuka sannan ta nuna musu su rufa mata asiri karsu sanar wa kowa,hakan dai aka bata magunguna ta koma gida da damuwa me dinbin yawa wacce ta ninka tada,tundaga wannan lokacin hafsat ta dawo sukuku sam bata walwala gashi batada lapiya a haka har Haleemah ta haifi yaro namiji,wanda bataje wankan gidan ba kuma tanayin 40 days aka maidashi kwana wurin hafsat,komai wahalar khaleefa hafsat keyi baji ba gani, harma ya saba sedai yasha madara wasu lokutan idan ya tashi a bacci da dare ya saka kuka setayi ta rarshinsa idan yaqi itabdinma seta saka mar kuka suyitayi se me aikinta tazo ta karb'eshi.......a haka har khaleefa yayi wata hudu a duniya,san suniya shaam ya dauka ya daura akan yaronnan bama a san ranshi yake barinshi kwana acan ba,danma bayason bacin ran haleema na...... Ranar wata juma'a Cikin dare khaleefa ya tashi da wani irin ciwon da hafsat ta kasa gane na menene,kuka yake tayi tamkar me yana zabure zabure,hankalin hafsat ya tashi ta dauki wayarta tayita kiran shaam baya dagawa,takira haleemah akayi rejectin call din sannan kuma aka kashe ma wayar gaba daya,shaam yaga ta kuma kiranshi yace "Haleemah lafiya kuwa? Kodai in daga inji menene dalilin kiran naga bata taba yin hakan ba?" wani narkewa haleemah tayi tace "Boo me dan Allah manta da ita,nasan kuka khaleefa ke mata shiya sanya kaga ina ce maka akaishi acan kar ya hanamu walawa" biyeta yayi sukayita har kofar gidan tazo ta bubbuga suka mata banza,koda ta koma yaron baya motsi lokacin ma karfe biyar na asuba,da kukanta takira shi again be daga ba,ta aika masa message "Yaa shaam nayita kiranka inaga fa Khaleefa ya rasu" yana fitowa daga gun alwala yaji aran message yaje ya duba a rude ya gayawa haleema da salla be dameta ba tana baccinta aibhar ture juna sukeyi sabida tsabar gidi mewa,banka kofar sukayi suka sameta rungume da gawar tana uban kuka, "yaa shaam kunga illan rashin daga waya ko? Shine inata kiranku yaron nan se zabura yakeyi amma kuka qi dagawa wlhy kungani ya mutu" ta sake fashewa da kuka,ai shaam na dubawa yaga da gaske ya mutu ya soma jibgar hafsat "yanzu tsabar bakida mutunci shine kika kashemun yaro,dama wannan qiyayyar taki akanshi ta wuce tunani wlhy kema sena kasheki,jibgarta ya hauyi baji ba gani haleema se kuka takeyi ta dauki gawar se jijigawa takeyi,dakyar yadena dukanta yace dan ubanki kije na sakeki saki d'aya ki barmun gidana........yana kaiwa nan yabar dakin yana me karbar gawar yana kuka,wayanta ta janyo da kyar ta kira Abba haris,yana dagwa dak'yar tace "Abba kazo ka daukeni yaa shammaz ya sakeni kuma so yakeyi ya kasheni da duka,banama iya tashi"............. To jama'a kunjifa yanda ta kasance,anya kuwa shammaz yanada hankali? Anya kuwa wannan halin nashi asirine kawai kodai har da qiyayya da wulaknci? Yaya rayuwa zata juya masa? Mom Nu'aiym *Don't forget to vote and comment,ur votes and comments are more important to me than anything plsss do vote for me* [1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* Wattpad@ 68billygaladanchi 11 Sosai ran Abba haris yake a b'ace sanda yazo gidan,kai tsaye part d'in hafsat ya wuce ya tarar sabuwar yar aikinta dasuka saba sarai ta tasata agaba tanata kuka ko motsi batayi,da hancinta da bakinta duk jini,sosai ya tsorata bema wani damu shaam sabida bashida abun ce masa ya sakata a mota itada sarai suka nufi asibiti.....waya yayiwa matarshi da dama ya barota hankali a tashe tana salallami akan driver yazo dasu Uduth suna can,Dr. Sayyeed hamid Ali shine dr d'in da ya duba Hafsat sunkai kusan awanni hud'u akanta kafin ta farfad'o,zuwa yayi ya kira Abba haris a office d'inshi ya kalleshi sosai sannan yace "Sir wannan yarinyar shekarunta nawa ne?" dubanshi abban yayi yace cikin damuwa "shekarunta sha shida inaga nanda watanni biyar zata cike sha bakwai" jinjina kanshi yayi sannan yace "Amma yallab'ai kuna zaune da qanqanuwar yarinyabhar ciwon zuciyata da hawan jini su mata yawa haka,ni fa a gaskiya nasan is very rare kagan yara masu qananun shekaru irin nata suna fama da wannan cutar,sa'annan wannan uban dukan da kuka ce mijinta ya mata kyautuwa ma yayi ku kaishi gun hukuma sabida kuwa ya tab'a wa yarinyar kai, yanzu haka idan ta farfad'o gaba daya bamusan a wanne halin zata tashiba,sabida jini ya taru mata a k'walwarta,rayuwar yarinyar abar tausayi" dafe kai abba haris yayi tare da zare ido waje cikeda kad'uwa yace "wane irin ciwon zuciya da hawan jini kuma likita? Anya hafsat tamu kake magana kuwa?" nisawa Dr. Sayyeed yayi cikeda tausayawa yace 'Alhj wlhy itan kuwa,kana nufi kenan bakusan tana fama da wayannan cututtukan ba? Bincike ya nunar mana cewa har magungunan take sha" A zuciye ya miqe yace "wannan azzalumin mijin nata ya sani sabida kuwa shikeda asibitin zuciya sukutum wacce itace k'wallin k'wal agarinnan,kuma shine babban likitan zuciya" kallonshi sayyeed yayi cikeda mamaki yace "Alhj Karkace dani Dr. Shammaz kake nufi sabida a iya sanina shikad'aine ya mallaki asibitin zuciya me zaman kanta,bazan amince ba idan har kace dani wai shine da kanshi yayiwa matarshi irin wannan dukan" kallonshi Abba yayi cikeda takaici sannan cikin d'acin zuciya ya furta "Amma zaka iya yadda cewar nine mahaifinsa na asali na haihuwa,yayinda mahaifin wannan yarinyar da yayiwa wannan dukan shine mariqinshi shine ya zamto gata agareshi harya kai wannan matsayin dayake kai a yanzu,amma shine tsabar yana butulu ya aikata wa yarshi wannan mummunan ta'adin" sosai wannan maganar ta girgiza Dr.sayyeed ya zare madubin idonshi ya dawo kujerar dake kusa data Abba ya zauna sannan yayi abba nuni da daya kujerar akan shima ya zauna ya ce "Amma nayi mamakin jin wannan maganar,sabida da badan kai bane mahaifinshi wlhy da bazan yarda ace wai Dr. Shaam ne yayi wannan aikin ba,sabida sanin dana masa mutumin Kirkine kuma kamili,Allah yamana tsari da sharri shaidan,yanzu dai bazamu sanar daku komaiba se yanda bincike ya nuna mana,sabida haka ku bamu nanda yamma seka dawo nan muji koma meye" Godiya Abba haris ya masa sannan ya fice kai tsaye gidan Daddy ya wuce ya tarar ana jajen mutuwar khaleefa,a fusace ya kalli jama'ar dake parlor kasancewar duk yan gidane se daddy da shaam,idonshi yayi jajir tamkar gaushin wuta "waye acikinku ya nemi sanin inda Hafsat take da baku ganta ba" mero ce tayi saurin cewa "Abba mun tambayeta amma yaa shaam ya sanar mana wai tana makaranta" wani kukan kura Abba haris yayi ya shaqi wuyan shaam ya miqar dashi tsaye ya surfafa masa lapiyayyen mari har guda uku a jere a jere,cikin mamaki d'aukacin mutanen dake parlor din suka miqe daddyy ne ya riqeshi "Harisu lapiyan ka kuwa meya faru?,yaro yana cikin zillar rashin yaronshi zakazo kana surfafa masa marika haka,meya maka" cikin huci yace "Sabida yaronshi ya mutu seya nemi kashe yar mutane,wai har shammaz dan bashida imani ba Allah a ranshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44