Chapter 14
Chapter 14
karkuce zakumun dole kalar na farko kundai ga ba aci nasara ba,ba alkhairi a tare da wannan auren,inshaa Allah zataji sauqi ku aura mata wani,kuma ni ba qinta nakeyiba kurun dai ina gudun gurbacewar zumuncine sabida kunga bawai san aure nake mata ba,kuma ma koba itaba banasan auren zumunci" Sosai da sosai maganganun shi suka girgiza rayukan ilahirin mutanen wurin,lallai shaam baze rasa yin shaye shaye ba,Abba haris miqewa yayi yace " Bazan maka baki ba Shammaz amma kaje duniyace,inshaa Allah kana darai hafsat zataci gaba kaikuwa kana bayan yan baya" yana kaiwa nan yayi waje,daddy ma waje yayi batare da yayi magana ranshi a b'ace momy ce tace "kaima danane shaam amma dan Allah inaso ka dubi girman zumunci ka taimaki qanwarka,waye ze aureta tana makauniya yarinya ga qarancin shekaru ko haihuwa batayiba" budar nakinshi se cewa yayi "momy dan Allah kiyi hakuri wlhy bazan iyaba" aikam momy kuka ta saka cikeda takaici shikuwa ko a jikinshi yayi waje abunshi.... Mom Nu'aiym [1/22, 7:56 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 13 Yaukam rayuwar daddy tayi matuqar b'aci da wulakncin shaam akan hafsat,lallai wannan yaron yazo da salo na raini iri iri,banda haka tayaya ma agaban su kaikoma ba agabansuba zece wai baze auri hafsat ba haryana iqirarin be sota tana da lapiyaba se yanzu data zama nakashashiya,ba abunda zece dashi koya nuna masa zega iya gudun ruwanshi tare da jiran matakin da Haris ze dauka....... Hafsat zaune tanaso taci abuncin dake gabanta amma bata saka cokalin wurin daya kamata,har ranta takejin wani tuquqi,wannan ya sanya ta ajiye cokalin ta laluba ta gincira,duk wannan abun datakeyi khairri na kallonta tana hawayen tsananin tausayinta,zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Sister ya bakici abuncin da yawa ba kaddai harkin koshi?" Murmushin yake tayi tace " Na qoshi ne wlhy" "Nasani baki koshiba hafsat,kawai sabida bakya saka spoon din inda ya dace ne,kiyi hakuri na baki kanki saba kuma inshaa Allah zaki warke ai haka doctor yace zakiji sauqi kinji" hawayen da dukkaninsu ke qoqarin tarewa ya silalo musu hafsat tace "Khairiyya haryaufa yaa shaam bezo ya duba niba,da gaske manufarshi kenan ya rabu dani har abada?" kukane ya kwace mata ta toshe bakinta,khairiyya tama rasa me zatace mata "kiyi hakuri hafsat,amma barin kira miki shi awaya" batace komai ba wannan ya sanya khairiyya taje waje tayi kiran shammaz akan dan Allah yazo hafsat ta damu da rashin zuwansa,beyi musu ba yace yana nan zuwa da dare..... A parlor zaune hafsat take a kujera me mazaunin mutum biyu,se shaam dake zaune a me mazaunin mutum d'aya,dak'yar ya iya bud'e bakinshi yace "Hafsat ya jikinki" "Naji sauqi Alhamdulillah" "Akace kina nemana?" sadda kanta tayi qasa "Yaya dama zancen komawa nane gidanka,dan Allah kayi hakuri abubuwan dasuka faru wlhy ko mutuwan khaleefa ba laifina bane lokacin sa ne yayi" murmushi yayi yace "Haba hafsat,kewai bakya fahimtar abubuwane? Ban soki nakuma zauna dakeba sanda kike mutum me lapiya,se yanzu dakika zama nakashashiya,na dade da fad'a miki sam bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane saura miki yaushe ki gama iddah,idan ma banyi kuskure ba aiba idda a kanki,saboda haka kiyi hakuri ki kalli dahir ni bazan taba dawo dake gidana ba,ina miki ao irinna yan uwantaka matsayinki na kanwata amma bawai zancen aure ba" dukda bata gani amma hakan be hanata duban inda take jiyo sautin muryanshiba tace tana kuka "Yanzu yaa shaam idan kai dakake dan uwana ka gujeni akan inada matsala waye aduniya ze aureni? Kaine sanadin lalacewar rayuwata,ka b'atamun duk wani abu danake taqama dashi,bani ga karatuna babu labarin future na,banida d'a ko d'aya a duniya da wanne kakeso inji?" murmushi ya kuma yi "Hafsat wlhy kinji na rantse bazan tab'a iya zaman aure dakeba,ke ni idan ma kinamun wannan maganar haushi kike bani wlhy,kimun magana kanki tsaye indai zaki bani matsayin yayanki to zakiga gata na haduwa,amma zancen aurennan yarabu kenan har abada,idn bakida wani abun fada zan wuce"......sanda ta d'anyi shiru sannan tace " Nayi dana sanin saninka arayuwa,nayi danasanin kasancewarka d'an uwa na jini agareni,nayi danasanin aurenka,nakuma yi danasanin aurenka,nayi danasanin kasantuwar zuciyata tawa ina ma ace canje aka mun bisa kuskure dana roqa a sauyamun da tawan sabida na kaucewa wannan wahalalliyar soyayyar,daga rana me kama da yau inaso ka nemo biro da takarda kakuma rubuta ka ajiye cewar ni hafsat nakashashiya nafita arayuwarka na har abada,na yanke duk wata alaqa dake tsakanina dakai, harta zamanka d'an uwana,ko a hanya ka ganni karka nuna sanayya tsakanina dake,bana buqatarka arayuwata ka sani ayau d'innan wlhy na tsaneka tsana mafi munin tunani,bazan hana zuciyana haukanta na sanka ba amma zan iya haramtawa rayuwata koda gaisawa dakai koda hakan yana nufin zan rasa ilahirin rayuwata kuwa tunda ai ka gama nak'asani meya ragemun,nice nan yaa shaam zan tabbatar maka da cewar bakin rijiya sam ba wurin wasan makaho bane" Yad'anyi mintuna biyu bece komai ba secan ya nisa yace "Hafsat me kuma ya kawo maganar tsana anan nifa d'an uwankine" miqewa tayi ta soma doddogara sandarta tana neman hanyar waje,kasancrwar tasan tsarin gida. Yasanya tayi amfani da basirar ta ta nufi cikin gidan zuwa dakinsu.....duk wannan zantutuukan nasu akan kunnen abba haris tausayinta me tsananin gaske ya rufe shi,daganan ya qudiri niyyar nemawa hafsat lapiya kota halin qaqa koda kuwa dukkanin abinda ya mallaka ze qare..... Hafsat tama kasa kuka,gaba d'aya wani mummunan yanayi takeji a zuciyarta game da shaam,tabbas yau tafara jin yana fice mata arai cikin qanqanin lokaci,wayantane ya soma ringing tashiga lalubarta tana kamowa dama wurin sazata amsa kira baze mata wuyaba ya sanya ta d'aga ta kara a kunne "Assalamu Alaikum" shine tajiyo am fad'a a d'ayan b'angaren tun kafin tayi magana,cikin sanyin murya tace "Amun wa Alaikassalam,barka da wuni" "Hafsat ya gida ya kuma jikinki?" "Da sauqi Alhamdulillah" ta bashi amsa "Sunana Dr.sayyeed Hameed Ali uncle d'inki" Murmushitayi tamkar yana gabanta sannan tace "Ayya Uncle say ya aiki yakuma kwana biyu?" "Alhamdulillah hafsat,dama Number din abban ki damuke da afile nayi tankira baya zuwa gashi kuma emagency case ne ya taso,shiya sanya nace barin nemeki ko zaki had'ani dashi" "Babu damuwa uncle say barin je ingaya mishi seya duba last call nawa ya kiraka,amma sekayi hakuri ni kadaice adakin khairii batanan,idan tashigo seta rakani gun abban" sosai ta bashi tausayi yace "Babu damuwa hafsat,nagode sosai" "nima nagode sosau uncle say Allah ya saka ma da alkhairi" har ranshi yaji dadin adu'arta lokaci d'aya ya tuna da matarsa margayiya data tafi ta barshi da tsananin kewa,itace take yawan masa adu'a irin wannan tun bayan mutuwar mahaifiyarsa...... Office Abba yaje ya sameshi,bayan sunyi magana awaya,da suka gaisa Dr.sayyeed ya tattara nutsuwarsa gun Abba sannan ya gyara zaman gilashin idonsa yace da Abba "yallab'ai Allah shine ya dasamun tsananin tausayin hafsat wanda tunda nake ban taba jin tausayin patient kwatankwacin yanda naji akan hafsat ba,musamman yanda na kula da karacin shekarunta, da farko dai ni haifaffen qasar India ne amma kuma d'an asalin Nigeria,mahaifina likitane kwararre wanda gaba d'aya acn yake aiki acanne ya had'u da mahaifiyata datake Ba'indiya kasancewarta musulma gaba da baya ya sanya basusha wahala iyayensu suka aminta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44