Chapter 26
Chapter 26
komai ba" sanda yaja numfashi sannan yace "Hafsat lallai kin dakkowa kanki abunda bazaki iya karasawa ina so ki sani bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ni dinnan nafi karfin tunanin ki wlhy"Murmushi tayi har haqwaranta suka bayyana sannan tace "Tabbas zancenka dutse ne Br. J.A,Amma ina san ka sani wlhy bazan saurara maka ba harse naga bayanka" cup dinshi ya dire akan table yace cikin nutsuwa batare daya kalli inda take ba "Miss poojah courage dinki yana burgeni sosai,abinda nakeso dake shine wannan fafatwar tamu ta zama deal" kallonshi tayi ta kauda kanta gefe batayi magana ba yace "Idan har kikayi wining case dinnan zan karbi hukuncin kisa kuma zan mallakamiki daukacin dukiyar dana mallaka fiye da rabinta zan baki,dukkanin abubuwan dana gada awurin mahaifina kuwa kashi uku zan masa in baki kashi biyu in yarona daya tilo dayan kashin,idan kuwa har nine nayi wining wannan case to kuwa ko kina so ko bakyaso sekin aureni" da sauri ta dago ta kalleshi taga shidin ba ita yake kallo ba,sai saita kanta tayi ganin deal din ba wani babba bane kasancewar tanada yaqinin shi yayi kisan kuma zata diddigo abun,tace "Na amince da wannan kuma zanyi" ta miqe kallonta yayi yace "Bakida wayo,shiyasanya nace dake bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane ai,an tab'a deal ba'a rubuceba idan na cuceki fa? Zama zakiyi mu rubuta muyi sighning inada photocophy machine se nabaki copy daya nima na ajiye dayan kuma ke zan baiwa orijinal ma" yafada yana murmushi kauda kanta gefe tayi sannan ta zauna amma sam bata karayaba,sanda suka gama komai sannan ya miqa mata hannu yace "Deal?" murmushin yaqe ta masa tace "Deal" daganan ta karba ta juya yace "Semun hadu a court poor poojah" juyowa tayi ta washe masa baki sannan tayi gaba abunta ta shige mota sukayi gaba,ya koma ya zauna yace "Smart poojah". Toophaaa jama'a wasa farin girki yanzu ake book kam,yanzu race ya fara. Idan kaji dadin wannan page dan Allah comment and vote..... [2/10, 10:05 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 24 Tunda hafsat ta koma gida take nazarin abubuwan da suka shiga tsakaninta da J.A sam bata ankare da wautar data aikata ba se yanzu,idan ya kasance shi yayi wining na case din fa? Ko kuma ya kasance ba shi bane yayi kisan fa?" wani tsoro ne ya shigeta lokaci d'aya qirjinta ya soma wani irin dokawa,dafe kanta tayi ta shiga rero adu'o i kala kala na tsari..... Brr. J.A kuwa bayan fitar hafsat a fusace shima ya fita,be tsaya ko ina ba se asibitin uduth kai tsaye wurin masu bada katin shiga wurin ya nufa bayan sun gaisa ya nuna musu ID card d'insa sannan yace "Nazo bincike ne akan wani case na murder da aka samu anan asibitin kwanakin baya,ina matukar buqatar had'in kanku domin tallafawa family d'in wannan babban rashin ba bisa haqqi ba,nima kuma da ake zargi ku taimakamun matsayin na na baban lauya me matsayi ace ana zargina da kisan kai" sosai suka fahimce shi dama mutane da dama sun dad'e da qaryata zancen zargin da ake masa kasancewar mutane da dama sunsan halinsa na nagarta, babban cikinsu yace "Wane taimakao kakeso mu maka yallab'ai?" gyaran zaman madubinsa yayi sannan yace "Record nakeso na dukkanin motocin dasuka shigo asibitin nan aranar 11/11/2016 tunda shabiyun daren shigar ranar har zuwa shabiyun daren wucewar ranar,na kuma san kunada cctv camera anan so idan ba damuwa ina buqatar video d'in" gyaran zama ogan nasu yayi sannan yace dashi "Dama plate number ne muke d'auka mubaka card na shiga,se kuma sunan motar da color dinta da model number na motar,cctv kuwa yana daukar shiga da fice na kowa a asibitin nan,sabida haka yallab'ai komai daya dace zamu baka inshaa Allah" godiya ya masa sannan yashiga tattare muhimman informations da aka lokaci daya ya harbo bakin zaren......... Shammaz kuwa tunda abun yafaru yakejin wani tausayin hafsat,a qasan zuciyarsa kuwa yanajin wani iri tamkar laifin sane komai,zuwa yayi ya samu haj Innah ya sanar mata yafasa auren hafsat baya santa kuma ta janye qudirinta,dama ita tunda taji cewar sabida auren sa da aka ambata hafsat ta gigice harta samu hatsari ta kudurta aranta bazata qara wannan furucinba kuma idan ma hafsat taji sauqi zatace abata zab'inta,shi kenan kuwa ta amince wa shaam akan ya gayawa iyayensu...... *Court* Hafsat ce a zaune tare da lauyan me kare J.A se wasu lauyoyin guda biyu,acikin babban court dake jihar sokoto,Justice d'inne ya rero bayanin zargin da akewa Brr. J.A tare da baiwa masu qara damar bayyana hujjojinsu daya sanya suke zarkin sa da kashe likitan,batare da bata lokaci ba hafsat ta zayyane komai daya faru agabanta ta qara da cewar "Furucin sa kad'ai ya isa ya nuna mana cewar shine yayi kisannan" dayan lauya din me kare wanda ake qara ne ya miqe yace "Objection my load" kallon sa justice din yayi shikuwa yaci gaba "my load be kamata lauyan wanda suke qara ya riqa alaqanta laifin kisan kai kacokam ga wanda ake zargi ba,tunda ai zargin sa ake bawai an tabbatar ba" justice ya kalli hafsat yace "A kiyaye" ya sake kallon Brr. Khaleed yace " yallab'ai zamu so akara mana lokaci kadan domin gabatar da shedunmu kuma zasu so a gayyato mana babban Abokin marigayin anan wato Dr. Shuraim" dama aka basu daganan aka d'age zaman sena da sati d'aya. *Bayan sati d'aya* Lauyan wanda ake qara ne yace fara magana kamar haka "My load wannan gabaki d'aya record ne na motocin dasuka shiga asibitin ranar da abun ya faru,acikin mun samu mota iri daya kirar honda civic kalar ja wacce aranar tashiga asibitin kusan 7 times a wannan ranar cctv camera ta main gate data ward din da akayi kisan duk sun tabbatar mana da shigar mamalakin motar so bakwai a wunin ranar, kuma duk shigar sa kai tsaye ward d'in yake nufa wato inda sin din ya faru kuma mayannin dayayi duka ba face mask a fuskarsa se ziyartarsa ta karshe inda har yayi nasarar hallakar da sayyeed,sannan kuma a binciken da muka gabatar,makashin yaje kashe hafsat ne ita kadai bawai da sayyeed,sabida sayyeed ba asibiti bane gidansa,kuma idan ma kasheshi zeyi sedai yaje gidansa ya kashesa acan,abinda muka sani shine sayyeed taimako yaje a yanda muka gani a camera shine harya fito ya ganshi ya shiga seya bisa a baya,abinda camera ta kasa nuna mana shine menene ya soma faruwa acikin dakin kasancewar babu wadatuwar haske ya sanya se bayan yayi kisan ya juya ze fita haske ya wadata kuma har fuskarsa mun gani,abunda masu qara sukace wanda yaje kisan hafsat itace wacce yafara dosawa pillow a fuska kafin sayyeed ya cece ta,idan ko har hakane furucin da muhammad yayi sam bashida alaqa da wannan kisan na sayyeed" shiru yayi hafsat gaba daya kanta ya daure sabida batayi wannan tunanin ba shi kuwa yaci gaba "Munyi nasarar cafke wanda yayi kisan,kuma munaso yazo nan da bakin sa yayi bayanin wanda ya sakashi kisan idan har kotu ta bamu damar yin hakan" izini. Aka basu akan su gabatar da mutumin......koda alqali ya tambayi mutumin seya fara bayani kamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44