Chapter 15
Chapter 15
dasuyi aurensu, acan aka haifeni kuma acan nayi karatu na gaba daya,bayan mahaifiyata ta rasune mahaifina ya dawo ainahin qasarsa wato nan Nigeria a kuma birnin sokoto,inada qanne na mata guda biyu suna gidansu mahaifiyata dake Babban birnin indiya wato Goa acan suke karatunsu,ni kadaine nabiyo mahaifina nayi aurena anan har Allah ya karb'i ran matata a wurin haihuwa......Dalilin daya sanya na baka tarihin rayuwata shine sabida inaso kaje kayi bincike kaji koda zaka da abinda zan fad'a maka yanzu,dukda yake dakai nakesan muyi tafiyar idan ma hakan ta kama" Dukda yake Dr.say yayi magana me harshe damo amma abba be katse shiba yace "Ina jinka sayyeed" "Mahaifina ya mallaki qatotuwar asibiti tashi ta kanshi a k'asar india inda kusan garuruwa hudu a fadin qasar zaka tarar akwai branches nata,zan baka komai sekayi browsing ka gani,akwai wani qwararren likita dake aiki a asibitin na mahaifina wanda shararre ne a b'angaren k'walwa shine nayi waya dashi sabida al'amarin hafsat yana damuna a bakin shi naji cewa inshaa Allah indai tanada rabon gani a duniya Allah ze bashi ikon mata aiki kuma fitowar farko ta warke sabida badashi aka haifeta ba, dama nikuma zanje india gun yan uwana dakuma kula da asibitin ta mahaifina shine nake sha'awar zuwa tare dakai da hafsat idan bakuda damuwa,nidai ayanda nake tausayin hafsat bana san ko sisin ku har jirgi ma nine nan zan dauki nauyi amincewarku kawai nake buqata dakuma uwa uba adu'arku" sosai Abba haris yaji dad'in wannan zancen yace "wannan ai babban ci gaba ne sayyeed,kuma zancen yadda tun yaushe aina yarda zancen kuma wai kyauta duk bata taso ba nine nan zan biya komai har zancen tafiyar ma,kuma wlhy na gode nagode maka sayyeed Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka ya sanya haske acikinta yakuma d'aukaka,Allah ya jib'anci lamuranka ya baka wata matar ta gari ya ilmantar da bayanka yakuma tallafi bayanka sayyewd" godiya sayyeed din tun kafin abba yabar asibitin yafara processing visa batare da sanin kowaba....... Ranar wata juma'a hafsat na kwance ta rufe idonta acewarta ba amfanin bud'asu wayanta ya soma ringing janyowa tayi ta kara a kunenta bayan ta d'aga,jin muryanshi kad'ai ya sanar mata waye me kiran cikin shagwaban dabata masan tana dashiba tace "Uncle say se yanzu,ni baran ma kula kaba Allah kuwan" murmushi yayi tamkar tana gabanshi " Beauty kefa rigimanki baya qarewa,wlhy Aikine yasha kaina matuqa kiyi hak'uri yanzu ya jikinki ina fatar kinji sauqi?" turo baki tayi "Ni bazan kulakaba" dariya sosai tabashi amma sabida bayasan ya b'ata ranta yace "Kiyi hakuri mana Beauty,aina sanar miki uzurina kuma fa yau zan siya miki pop corn da ice cream plus frozen coffee amor" murmushi tayi "Ni bazaka siye ni da wannan ba bazan ma shaba,nidai kawai ka kawomun qawata dan Allah itane take d'ebemunnkewa" "Naji zan kawo tan indai suhaila ce amma dai gaskiya se gobe,yau ina riqe sosai" murmushi tayi tace "Babu damuwa uncle say Allah ya kaimu goben" sallama sukayi sannan suka ajiye wayoyin su, hafsat se murmushi takeyi tun zuwan suhaila arayuwarta take jin sanyi abubuwa da dama suna canja mata ko yanzu tanata faman tunanin yanda zatayi idan tabar qasar,shiya sanya taso ayi auren uncle say da suhaila kafin tafiyarsu india dase su tafi tare da qawar tata me yawan d'ebe mata kewa...... Yauce ranar tafiyar su hafsat india,kowa se adu'a fatar samun nasara suke musu, tafiyar har da umma aciki, da abba......nima ina musu fatan alkhairi.. Don't forget to vote and comments...... [1/23, 9:57 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 13 *FLASH BACK* A ranar da yaa shaam yaji komai a ranar Haleemah taje wurin bokanta,kallonsu yayi itada uwarta yace "Kunyi sakaci dukkannin aikinku ya lalace,kuma mijin yarinyarnan yaji komai ciki kuwa hadda kashe masa gudan jininsa,kunsan cewar wannan abun ba qaramun b'ata ran shi yayi ba,sabida haka wannan aikin dazakuyi bashida wani amfani,idan kuwa kunaso amasa sabon aiki daze rufe masa baki tokuwa ke Haleemah sekin baiwa Aljani kyautar mahaifarki sukutum,tareda sha'awar mijinki ma'ana zamu cire dukkanin wata sha'awa dayake da ita a 'ya mace" zabura haleemah tayi tace "Nashiga uku boka,shikenan ni bazan qara haihuwaba? Kuma shi mijin nawa baze qara samun wata sha'awa akaina ba to meye amfanin auren??" Tsawa ya daka mata "ke!!!! Karki kawowa mutane raini kinji ko,kune da kanku kuka fada masa kuma yaji,aljani meramo yaso taimakonki ne idan bakyaso kije can,amma kin san na sanar miki asirin ze karye kuma ke zaki haukace,idan kin fisan haukar kije da mahaifar keda hankali sedai ki gani ga wari" zaro ido tayi tace "Kayi hakuri boka ba haka nake nufi,abunda ya kadar dani zancen qwace masa sha'awa" zbura yayi " K'wace masa sha'awa tare yake tafiya da sanya ya manta daduk wani abun da ya faru kuma yana ji yana gani yankasa magana koda be samu mantawar duka ba,shida sha'awar wata mace bama keba har gaban abada,kuma kece da kanki kikace dukiyarsa kadai zaki kwashe kiyi gaba to meye naki da sha'awarsa" haka dai dole suka yarda atake awurin aka hanawa zuciyar shammaz daukar wani mataki yaji a rayuwa baze iya mata koda tsawa ba,mahaifiyar haleemah ta kalli bokan tace "Aiki yayi kyau ya saki kishiyarta sedai yan gidansu nasan zasuce ya dawo da ita bama san hakan shifa ya za'ayi?" "Dama kin dena wahalar da kanki,sabida wannan yaron basan yarinyar yakeba,bana tunanin ze maidata kudinku da jikinku su huta hakanan" Godiya sukayi sannan suka wuce masaukinsu inda zasu qarashe tambad'ewa Allah ya shiryar damu ya kare muna imaninmu..... Hafsat Ajikin umma tayi baccinta jirgi,gaba d'aya Dr. Sayyeed duk wani motsi da zatayi idonshi na kanta masifar tausayinta yake ji, gashi yarasa dalilin daya sanya a wuni idan dai har ko kiranta beyiba seyaji wani uban zazzab'i na shirin rufeshi gaba daya,yakuma kasa fahimtar meyake damunshi arayuwa...... *INDIA* Kwanan su biyu a can agidan su maman Dr.sayyed suka sauka dukansu kasancewar gidan babban gidane ga kuma family d'in sananne ne a mumbai, Abba haris shikad'aine ya sauka a masauki sabida ganin rashin dacewar tarewarsa gidansu alhalin shi namijine....Ranar da aka shiga tiyata da hafsat har Dr.sayyeed dashi aka shiga tunkan amata allurar da za'a shemar dabita take kuka,sosai Dr.sayyeed yaji tausayinta ya kama ta ajikinsa shi dinma sanda yayi kuka da adu'a d'auke a bakinshi aka soma aikin.......... *Bayan kwanaki biyu* Cikeda fad'uwar gaba ake jiran sakamakon idon hafsat,wanda tsabar fad'uwan gaba ya sany Dr.sayyeed gaba daya ya kasa cin komai ranar,Kasa shiga yayi wurinta sedai a waje ya zauna wurin su Abba haris, sunfi 3 hours zaune zugum zugum kafin fitowar Dr . Din yana zuwa ya miqawa Dr. Say hannu da murmushi d'auke a fuskarsa sannan yace "Congratulations brother, we've succeeded" Miqewa yayi lokaci d'aya " Are you sure my Dr.?" murmushi ya kuma sakar masa "Sure bros" Rungumeshi yayi sannan yaja hannunshi zuwa d'akin da hafsat take a kwance,takasa banbance tsakanin farin ciki da bak'in ciki wanne takeji,Matsawa yayi kusa da ita yace "Sannu Hafsat,Alhamdulillah komai yayi normal yanzu" kallonshi tayi ta gane muryanshi amma bata taba zata haka kyawunsa yake ba sekace wani haihuwar larabawa,lokacin datake ganinsa bata cikin hankalinta batama iya tuno waye a kanta bare ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44