Chapter 2
Chapter 2
taron murnar dawowanshi dayayi shekaru kusan 8 baya kasar yace aranshi "kaddai har yanzu su daddy basu dena shagwab'a hafsat ba,inko hakane da matsala a tarbiyar yarinyar,ko yanzu ya fahimci ba wanda ta gayar a duk yawan mutanen dake wurin.....A parlor ma ba wanda tawa magana se Aunty surayyah wacce ita kadaice take masifar tsoro indai har tana wuri tofa iskancin hafsat qasa qasa yakeyi,kallon ta surayya tayi tace " ke Hafsat ni kadai kika gani anan sauran fa? ,d'an turo baki tayi sannan ta juya ta kalli jama'ar parlor din a wahalce tamkar wacce zatayi kuka tace "Ina wuninku" amsawa sukayi daganan suma saka mata dariya ganin irin shirmen datakeyi mafiya akasarinsu kuwa sun dauki hakan datayi amatsayin kuruciya,wasunsu kuwa sunsani sarai iskancine sundai kama bakinsu ne sabida suna samun alkhairi a wurin uwarta Haj Nasara wacce bata had'a kowa da ita ba,tana sharar k'wallah tayi sama a hanya ta hadu da mairo kalllanta tayi tace "Kulele momy ya akai?? Waye ya tabamun babbar 'yata" wurgi tayi da jakar ta tace "Bayan Aunty surayyane tace wai dole sena gayar da mutane bayan kuma arayuwa ni natsani gayar da kowa ma wlhy" rungu mota tayi jikinta "Haba babyn dady kiyi hakuri kinji ba wanda ze kuma tilastaki gayar da mutane amma fa ki sani ita gaisuwar wajibice idan ba hakaba yanzu zakiji ana cewa bakida kirki" wucewa kurin tayi bayan ga qwace jikinta ba tare da tayi magana ba,bayan like an hour se gatanan tafito sanye da vest da gajeren wando iya gwiwa tana tsotsa alawar lollipop,mutane sund'an ragu se yan uwa na dole batare data kalli kowa ba tayi dining serving warmers tagani tuma tuma awurin tsayawa tayi daga inda take ta kwallah ihun kiran mero "mero!!" wanda ya mayarda hankalin akasarin mutanen dake parlor akanta,da sauri mero tazo tace "Lele ya akai?" zumburo baki tayi tace "Dayake kinfison mutanen nan dani shine kika barni da yunwa tun dawona nake jiran abincina,ni ki zubamun to" kallon ta mero tayi tace "Dady ne ya sakani aiki kiyi hakuri mezan saka miki?" duk abinnan dasuke a gaban idon shammaz ne, ko kallonta batayi ba ta saka alawar datakesha a baki ta hau tsotsa sannan ta hard'e hannayenta gu daya,ganin haka mero ta gano rigima takeji yasanya ta dauki plate ta saka mata snacks da papaer chicken ta juyo ta miqa mata, karb'a tayi sannan ta kifar da abincin a wurin cikeda raini da shagwaba tace "ni wannan nace dake ina so? Shreded chicken zanci" batayi auneba taji saukar lapiyayyen mari wanda ya kusan zautar da ita,dafe wurin tayi ta saka kuka kowa a parlor din ya taso ana baiwa Shammaz haquri ita kuwa mero tazo da sauri ta riqe hafsat tana rarrashinta,wani kallo shammaz ya wurgawa mero, cikin fada ya furta " Maryam zan mareki wlhy kema,maza ki saketa ta clearing wannan mess datayi" jikinta har rawa yakeyi ta duqa ta soma tattare wurin tana sharar k'wallah tana gamawa yace " se kinci wannan din yar rainin hankali da zaki wani zo tana tambayarki kina iya shege sannan yanzu an zuba miki ki kifar an gaya miki a qasa ake haqowa" juyawa tayi zata haura sama da plate a hannu tana kuka yace cikin daga murya "Maza zo nan zaki zauna ki cinyeshi a gabana" dawowa tayi ta janyo kujerar dining daya tana kuka tanaci harta cinye tatas,momy dai batace komai ba amma harga Allah bataji dadin abinda shammaz yayiwa Hafsat ba agaban mutane,kumama tsabar rashin tunani daga dawowarshi duk wanda yaga yayiwa qanwarshi wannan abin aiseyaga tamkar baya san tane.......... Mom Nuaiym ce [1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin. wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 02 Hawa saman tayi bayan ta kammalawa cinyewa taje rufe kofar d'akinta tasaka wani uban kuka tanata faman shura qafa,duk abinda ta samu seta fasa ita adole zuciya,su momy sunzo juyin duniya sunyi akan ta bude kofar d'akin amma fir taqi se dad'a sautin kukanta takeyi Aunty surayya ma datazo tayita fadan amma yau ko gezau,surayyace takira Yaa shammaz yazo bakin k'ofar yace cikin daga murya "Hafsat Allah idan har kika kuskura na sameki a d'akin batare da kin budeshiba ranki ne zeyi matukar b'aci anan" cikeda fargaba ta bude kofar d'akin ta qura masa ido jan hannunta yayi sukayi waje sannan yakaita b'angarensa,zaunar da ita yayi suna fuskantar juna yace "ke har yanzu Hafsat girma da hankali basu wadace kiba? Mero sa'an kice sannan yanzu wannan uban borin dakikeyi a daki ke kadai wa kikewa shi? Sarai kinsan halina tsaf zan zaneki karkiga kamar yanzu na dawo zaneki zanyi sosai,kuma idan na kuma ganin kina wannan kukan ko hawaye daya na gani a idonki sena zaneki yanzumma kece da kanki zaki gyara barnar dakikayi a dakinki,sakaryar yarinya kawa,kuma daga yau duk bayan kwana biyu kece zaki riqa zuwa kina gyaramun wannan bangaren nawa,ki share ki goge da komai kina jina?" da sauri ta daga masa kai a ranta tace "Ina kammala exam zan gudu gidan Abba wlhy bazan zauna wannan mugun ya kashe niba" a fili kuma godiya ta masa sannan ta fita daga dakin..... *Washe gari* Yaa shaam na zaune a a daya daga cikin gujerun da aka qawata ht dake farfajiyan gidan dasu yana karatun news paper hannunsa daya na riqe da cup na hot meantleaf coffee yana kurba a hankali,ganin Hafsat ta fito ya sanya da sauri kuma cikeda mamaki ya mayarda dubanshi zuwaga wrist warch dake hannunshi,dagowa ya kumayi yaga driver yazo ya bude mata tashiga gidan baya ta zauna,driver din ya kwallawa kira yazo ya da sauri ya durqusa yana jiran cewar sa,kamar baya sanyin magana yace " Ina zakujene k'arfe tara da rabi na safe?" kanshi a qasa yace "Yallab'ai Haj qarama zankai makaranta?" Haj k'arama ya nanata a ransa sannan a sarari yace "yaushe yakamata ace kana fitowa kaita makaranta?" "yallab'ai dama da safene kullum k'arfe bakwai anan gidan yakemun,hajiyar ne bata fitowa se sanda taga dama" cikin mamaki yace "Ita hafsat ne setaga daman zuwa skul zataje? Maza jekamun kiranta" koda friver ya sanar mata tana fitowa mota kuka ta saka ta kwasa ciki aguje,miqewa shima yayi a fusace yabi bayanta,daddy da mommy na zaune a dining taruga ta fada jikin dady,kan wani cikinsu yayi magana sega yaa shaam ya shigo a fusace,momy ce tayi saurin magana "shaam lapiyanka kuwa meya sameka kaida qanwarka haka taketa kuka" daddy ya kalla yace "Amma daddy sabida Allah kuna kallo se yanzu hafsat zataje makaranta qarfe goma saura fa?? Wannan wane irin tarbiya aka mata ba kwab'a ba komai ace yarinya se sanda taga dama zataje skul wannan ai ba soyayya aciki" shiru daddy yayi saboda yasan gaskia shaam ya fada momy ce tace cikin quluwa "Kaga shammaz nafa kula tun dawowarka jiyannan ka takura yarinyarnan,hafsat baccin safe ne da ita kamar me ya kakeso muyi? " kallon momy yayi rai a b'ace yace "wannan ai rashin sone idan naga zatayi rashin hankali na barta,wannan ba takura aciki tsantsar soyayya ce nake mata,kuma ita jakar inace bata ma tsoron duka irin wannan mugun lattin ai dole setasha duka kullum" "makarantar mahaifinku take zuwa,se abinda taga dama takeyi ba wanda yake takura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44