Chapter 12
Chapter 12
ze riqa baiwa hafsat renon yaro cikin dare yashige da tsohuwar matar daya ajiye suna holewa,kuma sabida Allah ya karbi ranshi rana daya ya ce wai hafsat ce ta kasheshi kuma ya mata dan banzan duka harta suma,bayan sakinta dayayi duk wannan be isaba se sanin ya dasa mata ciwon zuciya ba wanda ya sani harma da hawan jini,yanda ga wayannan kuma gashi likita ya tabbatar mun cewar wai hafsat kanta ya tabu sabida dukan daya mata aka,wlhy Yaya Abu bazan tab'a yafewa Shammaz ba,na yafewa duniya shi kuma bazance masa komai ba yaje duniya ce,daga rana me kama da ta yau kar naji kona qara ganin yace nine nan na haifeshi ko mutuwa nayi wlhy banda shammaz a gadona kuma ko'a lahira se an mana hisabi dashi,yaci mutuncina yaci mutuncin dan uwana,yaci mutuncin matarshi yaci mutuncin aure,kuma be ragawa Allah ba,na kuma tabbatar Alkah bazenraga masa ba" Da sauri Daddy ya rufewa Haris baki tare da zaunar dashi dukkuwa danyake yaji maganganun tamkar saukar aradu,wai kan kulelen sa ya tab'u kuma a dalilin dukan da shaam ya mata,sa'annan kuma wai tanada ciwon zuciya adalilin mene wannan? Dakyar ya saisaita kansa ya kalli shaam "shammaz kaji abubuwan da harisu ya fada hakane??" sadda kanshi yayi qasa sannan yace "Daddy niba abunda nake mata,kuma wlhy bansan da zancen ciwon zuciyaba,da ina mata wani abin aidanta fada tuni,zancen khaleefa kuma itace da kanta taroqi Haleemah akan yana kwana gunta kuma jiyan ma wlhy banso ya kwana candin ba,dukan dana mata kuma ba'a san raina bane harma sakin dana mata duk acikin b'acin raine da gigicewar rasuwa khaleefan" Shiru daddy ya kasa magana kowama yayi shiru se momy dake kuka lokaci lokaci tana jan hanci kasancewar kukan nata bame sauti bane,yafi mintuna biyar kafin yace " Harisu dan Allah markayiwa d'anka baki,ka janye wayannan kalaman daka masa kuma ka nutsu wannan maganarbta gida ce ba abun tashin hankali bane" miqewa Abba yayi "wato yaya ba kadan ba ka ke sakarwa shammaz dama yana durun uwarsa san ransa,ni za'a gayawa wai harkar gida wlhy tallahi sena maka wannan yaron kotu senaji dalilin wannan ha'incin kuma koban masa bakiba haqqin yata seya kamashi rasa kunya kawai b'eran tanka,dana sani shine babban amininka koba yanzu sekun kulla babbar abota dashi wlhy" yana kaiwa nan yayi waje,yayinda momy tayi kiran mero suka nufi asibitin uduth daddy ma da shaam din suka bi bayansu kasancewar haleemah tana gidansu..... Acikin d'akin kowa yayi zugum zugum an qurawa hafsat dake wance ido, A hankali ta bud'e manya manyan dara daran idonta,sunanan dai a lumshe tamkar mejin bacci a kowane lokaci,d'aya bayan d'aya take bin kowa da kallo,har shaam wanda taqurawa ido bata ko k'iftawa,a hankali kuma ta rufe idon tamkar me bacci can kuma bayan yan mintuna tamkar wacce aka tsira kuma seta fara fizge fizge kan kace me wannan ta soma zabga sambatu "Dan Allah karka dakeni wlhy ba abunda nawa khaleefa,yaa shaam ka dena dukana zaka kasheni,wayyo Allah daddy kazo ze kasheni,Abba yaa shaam ze kasheni" dak'yar suka rirriqeta shaam yaje yayi kiran nurse dake kusa akan ya akira doctor sannan ya koma kanta, koda dortor yazo seta fara kuka sekuma ta saka dariya kowa a d'akin kuka yakeyi yayinda lokaci d'aya kunya,danasani,nadama da bak'in ciki suka qara taruwa suka lullub'e shaam yama rasa me yake ciki a yanzu,Dr.sayyeed ne yazo dubatan ya kalli shaam ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yane kai tsaye wurin hafsat,cewa yayi kowa ya saketa sannan ya sauke mata lallausan murmushi bayan ya riqe hannunta na dama,qura masa ido tayi dukda acikin rashin lapiya take amma setake masa kallon rashin sani yace yana ci gaba da fad'ad'a murmushinsa "Hafsat sannu kinji meye ne yake damunki? Cikeda wowta tamkar wata yar shekaru biyar tace "Bayan yaa shaam kullum yake dukana na ganeshi so yakeyi ya kasheni,ni ku fita dashi a d'akinnan inba haka duka na zeyi kuma banasan ganinshi" K'ara riqe hannunta yayi yace "Ai indai ni Uncle sayyeed ina nan wancan shaam din baze dakeki ba idan ma yazo dukanki nine zan mar d'an banzan duka yanzu sanar dani ina ne yake miki ciwo?" amaimakon ta bashi amsa se kawai ta matso ta qamqameshi tana kuka da sambatu alamun ba hankali atattare da ita "Uncle sayyeed karka bari yazo kusa dani dan Allah,daddy idan bazakuce ya wuce ba ni bana sanku"k'wallah Abba ya share cikin hikima yayi waje a haka a haka kowa ya watse ya kama gabanshi cikin k'unan rai,Dr.sayyeed be ajiyetaba seda tayi bacci shida kanshi yarinyar ta bashi tausayi over,be tab'a ganin case maka mancin wannan ba awurin yara dai...... Shaam na fitowa yakira Haleemah suka gaisa se kukan munafurci takeyi dak'yar ya rarrasheta ya sanar mata halin da ake ciki,cikeda kirsa tace "Amma ai yaa shaam na sanar maka karka daketa ba laifin ta bane ba inaga kaddara ne kawai" sallama dai ya mata ta ajiye wayar ashe sam shi be ajiyeba yana jiran yaji tace I love you boo me,yanda suka saba se kawai yaji an tafa hannu ana sowa "Wlhy umma gabad'aya jin wannan labarin senaji gwarama da khaleefa din ya mace,dama kinsan ance seka haifi wanda zeyi silar arziqinka to zuwan khaleefa kenan a duniya,nifa da farko dakikace boka yace rayuwar khaleefa fansa har naji bakya sona,ashe kinfini kaifin hankali tunda ko yanzu nakeso zan iya qara haihuwa,amma fa wannan aikin da tsauri yake umma ji nayi kince bokan yace sena kwana biyar a gidanshi yana saduwa dani kuma kince wai idan har mijina yasan zanje konan dacan aikin bazeyiba sannan kuma idan har yayi koda tunanin muna masa asiri bare ma ya gane to aikin ya karye,ni kuwa ai bazanso hakan ba yanzu ya kenan??" "Kinga hali dubu yar mama,barni da shegen yaronnan maganinsa zamuyi ai,yanzu ki hau bori zaki tsaya anan,kinga gobe seki je,duk ya kira akan zezo ki hanashi harse mungama aikinmu,kuma kinji boka yace daga zaran kin sadu dashi na karshe karki bari awuce awa ashirin da hudu ba tare da kin sadu da mijinki ba,kina yin hakan gaba daya ze kwashe mana dukiyar sa ya bamu,daga nan idan munso mu kasheshi ko kuma mubar masa gidansa inyaso mu koma lalubo wani me kudin,karfa ki manta khaleefa kika bayar akan kinasan yin arziki gudan jininki sabida ki nutsu kar a samu kuskure kuma ki tabbatar yaji wannan ganyen a abinci sabida shine ze gusar mas d hankali yakwashe mana dukiya a arha" dariya tayi suka tafa wanda shaam yaji komai zufa se keto masa takeyi ya kasa sauke wayar a kunnenshi yana saurarensu sunata shirya makirci,shi gaba daya ma ya rikice musamman jinda yayi suna zancen sun dasa masa qiyayyar hafsat,lokaci daya ma yaji ya tsani kansa kuma soyayyar dayake mata ta yaya da kanwa kai tsaye ta dawo da gudun fanfalaqi,amma fa har yau bawai yaji yana santa na soyayyaba......... Dr. Sayyeed ne ya kalli shaam bayan sun zauna,yace raunin na kanta ya taba mata kwalwa harma yana neman zautar da ita,sannan kuma ga zuciyarta ta tsananta abinda na fuskanta duk sanda kazo wurinta se hawan jininta ya tashi ga bugun zuciyarta dake qaruwa,sabida haka kadan daga mata qafa,zancen gaskiya kuma aikin manta bame wahala bane sedai zeci kudi,abu mafi muhimmanci danakeso ka sani matsayinka na likita shine,lallai wannan jijiyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44