Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
Download Book

haka "Da farko dai sunana kamilu,kuma ni dan area boy ne ina zamane a unguwar iraqi dake cikin garin sokoto,ina zama wani likita me suna shuraim yazo ya sameni akan yanaso in masa aiki akan wata mara lapiya me suna hafsat,ni kuwa dama ba ruwana aiki ko wane irine indai na kudine to kuwa zan yishi yabani details na komai da komai na dakin datake da time da babu yawaitar mutane awurin yakuma ce na danneta da pillow sabida gudun zargi ganin zan samu kudi ya sanya na amsa tayinsa naje nagama monitoring na wurin da komai,nashirya rana daya naje,shine qaddara ya fadowa wanda yazo tare fadan na kasheshi da wuqa ta,shine wayannan suka bi ta hanyar kotar danake hawa suka kamoni" jinjina kai kowa keyi yayinda hafsat ta rikice tabbas wannan shine mutumin data gani kuwa,dama sun buqaci ganin shuraim shi kuwa be karaji daga wurin wannan mutuminba so bezata hakan zata faru ba,koda aka buqaci yazo beyi gaddama yazo a rude ,tambayar sa akayi dalilin san kashe hafsat baiwar Allah yafara magana kamar haka "Na kasance ina matukar san yarinyar tun tana secondry schoool amma ta wulakantani,har kuka nake mata amma bata damu dani ba,ganin nayi nayi taqi kulani yasanya nashiga malamai na sanya duk wani namiji idan ya kalleta zeji yana matukar tsanarta idan kuwa me riqon addinine yafara santa semu saka masa mafarkai na tsoro akan zamu kashe duka su biyun harse yagaji ya kyaleta,kwatsam mukazo asirinmu damuke mata ya dena tasiri bincike ya nuna mata an mata magani kuma turarukan datake using ba wani aljanin daze iya rab'ar inda take ma, da wannan naji zuciyata tanamun zafi a yanda nakesan hafsat lallai na qudurta araina idan har ban sameta ba to kuwa bazan taba bari ta mori wata rayuwa da wani namiji ba,a wannan karon kuwa naga bazan iya kashe abokina ba kuma asirin yaqi cinsu shine nayi amfani da damar kwanciyar ta asibiti na aikata hakan,amma wlhy nayi nadama musamman rashi aminina na sosai sosai" shiru aka danyi kan mutane su fara mamakin dan wannan guntun laifin ze saka tsabar rashin imani ka kashe mace har lahira,hukuncin daya dace dashi aka yanka mai aka tarwatse karar aka kuma gargadi muhammad akan furucinsa daya janyo masa cin zarafi....... *Washe gari* Tsaf J.A ya shirya yaje gidan su hafsat a parlor akai masa masauki,sannan akaje kiran hafsat,jiki a mace ta sakko yana ganin ta ya miqe tsaye yazo suna fuskantar juna yace "Bakin rijiya poor barrister,the youngest one,nazone in sanar miki ki gayawa iyayen ki one week kawai na saka d'aurin auren mu,lokaci yakusa zuwa dazaki san waye muhammad,menene kuma matsayin wanda ya tozartar dashi yakuma bata masa suna a idan duniya" wasu miyau ta hadiya masu dacin gaske ta runtse idonta sosai ta bude su a hankali sannan tace "Kayi hakuri muhammad" bece komai ba ya miko mata waya kirar iphone 6 yace zan miki waya,idan buqatar hakan ya taso,yana gama fadar hakan ya juya a nan ta durqushe ta saka kuka me tsuma zuciya..... Mom nuaiym [2/11, 8:52 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 25 Da k'yar ta iya lallasr kanta tayi ciki,tarasa wazata tunkara da wannan maganar a duniya,ganin shirun baze amfaneta da komai ba ya sanya for the first time tun bayan rabuwarta da yaa shaam ta d'aga waya ta kirasa,mamakin ganin sunan ta yayi amma seya dauka da sauri ya kara a kunne tare da cewa "Hafst ya jikinki" amaimakon ta ansa shi se kawai ta saka masa kuka,mamakin jin kukan tane ya kamashi yace cikin rud'u "Subhanallah hafsat meya faru? Bakida lapiyane ko kuma shari'an ne be miki ba mu d'aukaka qara?" cikin sheshekar kuka tace "Dan Allah idan baka komai mu hadu a season 7 park,inaso muyi wata magana dakai ne" batare da bata lokaci ba yace "Babu damuwa in the nxt 25 mnts zan isa wurin" "To yaa shaam nima a haka" da kanta tayi tuqi tana isa wurin ta tarar ya rigata aranta ta ayyana wata qila yana kusa da gun dama,motarshi ta nufa kai tsaye ta bud'e gidan gaba ta zauna,gaidashi tayi sannan ta miqa masa takarda,cikeda mamakin takardar meye ya karb'a ya bud'e zare ido yayi bayan kammala karatun takardar sannan yace yana kallonta "Hafsat se yaushe zakiyi hankali ne wai e? Mesa komai naki bakya san ki saka tunanin mezeje ya dawo aranki? Yanzu gashi kin janyowa kanki sabida babu wani wanda ya isa ya watse wannan maganar yanzu,kuma sanin kanki ne j.A babban lauya ne wanda ya shahara a fannin iya shari'a,ni bawai auren sa bane banso kiyi sabi kowa ya masa shaidar halayya ta kwarai kuma sosai reputation dinsa ya girgiza da faruwar wannan abun waya sani koda wata manufar ze aureki ta cutar wa? Babban burina shine ki samu nutsuwa a gidan mijinki wannan shine dalilin daya sanya sam kikaga na janye zancen aurenki da zanyi sabida na tabbatar wa kaina bazaki tab'a samun nutsuwa dani ba musamman akan halima,yanzu sanar dani yaya kikeso muyi kuma yazo miki da wata maganar ne?" Kallonshi tayi tama kasa kukan yanzu kam tace "Yazo da yamman nan,yake cewa dani wai nagaya wa su daddy aure nan da sati daya yakeso kuma zan fahimci ba'a cin zarafinsa a zauna lapiya,har ya bani wannan wayar akan zemun waya idan buqatar hakan ya taso" nisawa yayi yace "Hafsat gaskia kinyi kuskure da kika aikata wannan shirmen,babu abinda zakiyi illah kije ki gayawansu daddy ayi masa yanda yakeso kije kiyita hakuri,danni nan matsalolin dakike fuskanta suna daukarmun hankali bamu sani ba ko wannan auren dazakuyi dashi ya zamo sanadiyar jin dadin na har abada ta yiyu ma adu'ar iyayen mu ne Allah ya karba zakiji dadi" kallonshi tayi qirjinta na dokawa tace "Baka tunanin cewar wani zargi ze iya shiga tsakani na da mutane? Baka ganin wasu ma zasu iya cewa hadin bakine kisan da aka yiwa sayyeed nida muhammad? Baka ganin kuma idan sun fada haka basuyi karya ba,muhammad so yake ya batan suna nima so yakeyi gaba daya nima duniya ta zageni,idan har na yadda da zancen aurennan tofa wlhy kowa zega tamkar ban damu da mutuwar sayyeed bane musamman lokacin nan daya diba kadan,dama ace nanda watanni hudu yace ko biyar" "Hafsat kije ki lallab'asa da dabarunku na mata cikeda hikima sabida ya yarda abar auren har nan da koda watanni uku ne,kuma kije gidansu sayyeed na nan garin ki nunawa mahaifinsa wannan takardar ta yar jejeniya ,shima mahaifin na say kizo masa da hikima ta hanyar rokarsa akan ya nema miki alfarmar muhammad ya janye wannan agrement din ya hakura da auren ki,ta wannan hanyar kadai zaki tsira da mutuncin ki a wurin iyayen sayyeed koda kuwa an daura auren nanda sati daya" jinjina kanta tayi cikeda gamsuwa da bayaninsa "Yaa shaam dan Allah mana muje gida na ajiye motana muyi sallan magrib in yaso ka rakani gun baban sayyeed ni tsoron wannan muhammad din nakeyi wataqil idan ya aureni ma mutuwa kawai zanyi" murmushi yayi yace "Kece mutuwan ai,sekace wani dodo"....... Bayan ta gama yiwa mahaifin sayyeed bayani yakuma ga takardar murmushi ya sake yace "'yata wannan muhammad din

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44