Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,257 words 0 views Progress saved
Download Book

karan tsana ya d'aura mata kullum acikin bautawa gidanshi take ita kuwa yi hawai takeyi domin ta faranta masa,momy kuwa komai akan idonta take tafiya yanda ake takurawa yarta ba karamun damunta yakeba,duk kuma sanda tayi magana sekaga fuskar daddy ta sauya akan hakan. Hafsat da huda sun samu admsn a Usman d'an fodiyo university dake sokoto,inda dukkansu suke karantar English,dabadan hafsat tanada kokari ba dabazata gane komai ba a makaranta kasancewar gaba daya hankalinta yana kan yaa shaam kullum kwanann duniya da begensa take kwana kuma take tashi,shekarunta goma sha shida yanzu yakamata ace ta qara girma irinna tashen balagan nan amma sam damuwa ya hana ta,tanaso ta yakice wa kanta soyayyar yaa shaam amma ta kasa,ganin rayuwar gidan yamata k'unci ya sanya tabar sama road gaba daya ta tattare kayanta tace gidan Abba haris zataje gun khairiyyah dayake itace tsarar haihuwarta,momy bata hanataba kasancewar tasani sarai 'yar tata tana cikin damuwa,gwara ma tane candin kota samu sassaucin abinda yayan nata kemata wannan kenan. Tunda hafsat takoma gidan Abba haris se kewar shaam ya taso mata,shaam seyayi sati biyu bezo wurinsu abba haris ba,dukkuwa dayake sune iyayensa na ainahi,sabida kawaici,lokacin da yayan abban haris yayi aure wato mahaifin hafsat yajima be haihuba kai har haris yayi aure suka haifi shaam,shine fa suka baiwa yayanshi shi na har abada ganin yana matukar san y'ay'a amma Allah be kawo masa ba shiya sanya hafsat datazo sanda ba'a zataba bata gane cewar ba mahaifansu daya ba na haihuwa se daga bisani,domin kuwa an cire rai kamar daga sama Allah ya kawowa haj nasara cikinta samun hafsat be sauya komai ba na dangane dankaunar dasu momy da daddy kewa shaam ba......duk tabi ta qara yamutsewa batada kiza kiza,har Abba haris ya fahimci haka,kuma yayi juyin duniyarnan amma sam tace ita ba abunda ike damunta,da wannan yayi kiran khairiyya yace lallai tabi yar uwarta taji meke damunta cikin hikima domin ya kula ko wannan dawowan da tayi da dalili. Da dare hafsat ta tashi kukan data sama na rashin yayanta,wayanta ta dauko ta qurawa hotonsa ido a sarari kuwa tana kuka tace "yaa Allah ina rokonka,ya ubangijin sammai da kassai,ya Allah ka ceceni Allah ka cire mun san yaa shaam a zuciyana,Allah ka rabani da kaunarshi,Allah ka ceci rayuwata karna mutu"" kuka me tsanani ya kwace mata khairiyya da ke kwance tana kallonta tana kuma saurarenta da mamaki tazo ta dafa tace "Hafsat yaa shaam kuma? So? So naji kina ambata,shine zaki bari san dan uwanki ya hallakaki har haka? Kinga kuwa yanda kika dawo sekace ba poojah kulelen daddy ba? Meyasa zakiyi shiru kibar abu aranki bayan kuma kinada gatan da za'a miki abinda kikeso?" tana kuka ta kasa magana dakyar khairrii ta rarrasheta tayi shiru sannan ta kalleta tace "Anya khairiyyah yaa shaam ze tab'a sona kuwa? Baze taba sona ba shekaru biyu kenan da yasan i a sanshi amma banda tsana ba abunda yake qara nunamun kullum,ina kyautata zaton a duk fadin duniyarnan a zuciyar yaa shaam wanda ya tsana ni kebin shedan,nikuwa bansan mesaba nayi rashin sa'an zuwana duniya wlhy inaga san yaa shaam ne zeyi ajalina amma dan Allah karki sanarwa kowa kinji?" hannunta ta kama tace "Wlhy bazan barki cikin azaba bayan inada maganinta,wlhy sena gayawa Abba gobe da safe tayaya poojah?? Tayaya san dan uwanki ze illataki bayan kinada gatanki? Ni gaskiya sena fad'a" kwanciya tayi ajikin khairiyya tama kasa magana......washe gari khairii ko breakfast batayiba taje ta kwashe komai ta sanarwa Abba,aikam ya hau bambami yace "Amma shine kulelen tayi shiru,shekaru biyu tun lokacin aurenshi fa kenan,lallai wannan yarinyar tasha wahala wlhy bazata sab'uba dole dan ubanshi seya aureta shi kuwa kodan halaccin ubanta akanshi,maza tashi kije anjima zan nemeku" tana barin wurin ya daga waya ya kira yayanshi da shaam akan zezo gidan ya samesu akwai magana,da khairii da Hafsat dakuma umman su khairri aka je.....bayan an gaggaisa ya kalki yayan nashi yace "Yaya wannan ramar da damuwar da hafsat ke kici duk akan tanasan yayanta ne shaam aurenshi take sanyi ni kuwa na yanke hukuncin ayi auren tunda yanada halin yin hakan" tamkar saukar aradu haka yaa shaam yaji wani maganar da sauri ya d'ago ya kalli abba haris,daddy ne yace "Haris ai ita kace tana sanshi shifa bamuji ta bakinsa ba,kai shammaz menene ra'ayinka?" k'asa yayi da kanshi kan yace "Daddy ni bawai bana san hafsat bane ba amma dama tun farko ita na fara aura amma sam ni ba tsarin mata biyu a ra'ayina tayi hakuri kawai ta nemi wani" umma ce ta yanka masa wani mari dabesan da zuwansa ba "Kai mara hankalin inane dazaka taramu anan ka gaya mana wani tsari to bari kaji wallahil azeem ko yanzu na mutu indai ba hafsat ce tace bata sankaba bazata aure kaba kaine kaqi wlhy Allah ya isa ban yafe maka ba indai kaine ka kuma cewa bazaka auretaba" se huci take abba haris ma yace "Lallai wannan anyi dan banzan yaro,toka sani ninan na yanke hukunci kuma wlhy koda wasa kakuma furta bakaso na sallamawa duniya kai aure kuma nanda sati biyu masu zuwa zan daura idan muka kaima ita ka dawo mana da gawarta washe gari tsabar rashin san rugura tsari" shidai bece komai ba yayinda hafsat se kuka takeyi daddy yace "haris ina darai zaka yankewa shaam hukunci? Ina nine ubansa? To baza ai masa auren dole ba indai ina numfashi" ran abba haris ya baci ya kalli yayanshi yace "yaya iya tsawon zamana dakai ban taba maka musu ba amma wlhy wannan karon bazan lamunta a cutar mun da 'ya ba,wlhy indai har ina numfashi nanda sati biyu zan daura aurensu sannan kuma idan yace yafasa Allah ya isa tsakanina dashi" jikin daddy ne yayi sanyi kuma harga Allah shima yanasan auren,momy ma dadi fal aranta sabida tasani hafsat nasan shaam sosai......bayan sun watse hafsat na d'akinta yayinda kahirri ke toilet shaam ya shigo tamkar wani mayunwacin zaki,tana ganin ta mike a tsorace,Da baya da baya take tafiya har suka isa bango,ya sanya hannunshi ya matse hannunta sosai yace "Kika zab'i aurena bayan kinsan na tsaneki ko? Kika zab'i aurena bayan kinsan zakisha uquba a hannuna? Kika zab'i had'ani da iyayena sabida tsabar san zuciya ko?? Wlhy ki sani se kin gwammace kid'a da karatu indai muddin kika yarda kika shigo hannuna,sekin gwammace da bakizo duniyaba sekin kasa tantance nine kuwa kobani bane,shawara nake baki ki janye inba haka ba ko hmmm wlhy senci qaniyarki da mai da yaji,k'aramar yarinya se iskanci banza tambad'addi'ya....yana kaiwa nan ya saketa ya juya,ita yauma ta kasa koda kukanne sabida bakin ciki,gashi sam bazata fasa aurenshiba koda ze yanakatane gida biyu idan anyi auren......hmmm hafsat kenan anya baki daukowa kanki masifa ba kuwa??.... Mon Nua'iym [1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* Wannan shafin nakine kyauta Aunty me jiddah musa,Allahu ya wadata ki da hasken rayuwa ya sanyaki a aljannarsa madaukakiya 08 Mamakine ya kama hafsat sanda ta farka taga har qarfe tara ta gota sauqinta daya tana fashin sallah,jiki ba kwari ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta sanya rigarta mara nauyi pink color doguwace har qasa

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44