Chapter 10
Chapter 10
dake a hannuna sekace da yunwa take kwana a gidan" batare datace komai ba tayi ciki aranta tace "Nice ma bankai mace ba,nice ma ban isa yasoni ba,nice banida banbanci da tsinken tsintsiya" ko wannan daren hafsat kasa bacci tayi kuma se zazzab'i me zafi ya rufeta Allah ya taimaketa ta kammala exams nata gaba d'aya........washe gari yayi kiranta wai tasan haleemah nada juna biyu bata iyacin abinda ta girka ta kawo mata abunci,tace dashi "yaa shaam nima a kwance nake ko bacci banyiba wlhy banida lapiya" tsaki yaja yace wai mintuna talatin yabata ta kawo kalacin.... Mom Nu'aiym [1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* *Wannan shafin nakine maryam Abdullahi gumel,nagode da qaunarki agareni* 10 Tunda hafsat tashiga gida take rusar uban kuka daganan tayi alqawarin ficewa sha'anin yaa shaam koda kuwa soyayyar sa zata hallakar da ita har abada.....da wannan ta mayarda hankalinta akan karatunta matsalar fa d'aya tsananin sha'awar dake damunta kullum ba dare ba rana,ta rasa yanda zatayi da kanta kuma tayi alqawarin koda huda bazata sake sanarwa da duk wata matsala tata ba zata qalubalanci rayuwarta ita daya, amma fa sam bata acikin walwala.....yau dai shirin zuwa gidan momy tayi sabida sunday ne ba school,harta shiga mota yaa shaam ya tsaidata "Kije ki dafa mana abinci sabida Babyn shaam bata da lapiya kin kuma sani sarai tanada juna biyu bata iya cin abinda ta girka" tamkar zata yi kuka haka ta ji amma seta daure batace komai ba tafito zuwa cikin gidan,a bangarenta ta girka komai sannan ta shirya ta dauka takai bangaren haleemah,tana zuwa ta ajiye a dining ta sanar musu,seda haleemah ta kalleta sannan tace,cikeda sigar rarrashi "Dan Allah hafsat kiyi hakuri wlhy bazan iya cin komai ba se indomie,ki daure ki taimaka ki girkamun" kallon mamaki tabita dashi sannan batare datace komai ba ta juya zuwa ktchn din a gurguje gani karfe uku ta gota momy se waya take mata akan bata zoba ta dafa ta kawo mata,har takai kofar barin parlor din tajiyo karar daya bata mamaki "Nashiga ukuna ni haleemah,wlhy boo me baran iya ciba yaji ne aciki sosai ga kuma magi yamun yawa" wani mugun kallo shaam ya wurgawa hafsat "muguwar yarinya dawo nan ai kinsan muguntar da kika kullah me baqar zuciya,dan ubanki da dakikasan bazaki iyaba meya hanaki kanki tsaye kice bazakiyiba,wato wannan cikin na jikinta shi kikeso ki kashe ko? Muguwar banza muguwar wofi wlhy yau bama inda zaki,kin dinga girka mata indomie kenan se sanda kika girka mata kalan wanda tace ya mata" kan tayi magana kuka ya kwace mata se kuma wayanta ya soma ringing,dagawa tayi tana me hadiye kukan lokaci daya ta qaqalo murmushin daya baiwa shaam mamaki takuma saisaita muryanta "Momy dan Allah kiyi hakuri,wlhy Aunty Haleema ne batada lapiya inaga kamar bazan samu damar shigowa ba yau,kinga ita kadaice bazan barta haka ba" murmushi momyn tayi tace "Eyyah Allah sarki Allah ya bata lapiya ki gaida ta kinji,yanzu se yaushe??" "gobe sha biyu nake qare lectures inshaa Allah daga school se gidanki momy karki damu" "To Allah ya kaimu hafsat Allah ya miki albarka kinji" Ameen kawai tace ta ajiye wayan sannan ta juya zuwa kitchn din,dafa wani tayi bata saka yaji ba ta kawo,ai loman farko ta zubar aqasa ta kalli yaa shaam fuskar nan harta soma kawo ruwa "Yaa shaam kaci kaji wlhy ba taste yanzu fa ko d'an green pepper ta saka man amma haka tayishi,Allah ni bazan ciba kuma" Tsaki hafsat taja bada shirinta,dama fa hafsat gwanar rashin kunya ce kurin tsoron yaa shaam ne ke durqusar da ita,yau kam ta cika fam "Gaskiya Aunty haleema bansan ya kikeso na miki ba na dafa wancan kince bazakiciba na dafa wannan indomie kince yaji,na kuma dafa wani kince ba yaji ni kije ki dafa da kanki,ko aikin bauta nazo na muku wlhy ko zaku kasheni bazan dafa muku wani ba" kallon mamaki shaam ya mata domin shi har tasoma bashi tausayi ya matso kusa da ita yace "Jeki kitchen ki dafa mata me abunda takeso" tsayuwa tayi a wurin taqi koda motsi,saukar wani kyakyawan mari taji seda ta ga wasu taurari na musamman,yace "ina wasa dakene? Nace kije ki dafa mata wani" kamar yanda batayi magana ba haka bata koda motsa ba da wannan ya shaam ya soma dukanta tamkar wani mahaukaci baji ba gani seda haleemah taga tayi lilis sannan ta saka kukan muna furci tazo tana qwatar hafsat "shaam dan Allah kayi hak'uri,idan ka illatar da qanwarka ni za'aga laifina kuma kaga ai tama gaji ni dama ba ina nufin ta dafa wani bane,nama ji na qoshi tea ma ya isheni,miqewa tayi tsaye ita kuwa tayi hanyar waje har wannan lokacin bakinta be mutuba tana kaiwa kofa tace "kuma wlhy ko zaku kasheni na dena muku girki kenan har abada" bebi ta kanta ba ya dawo wurin haleemh da rarrashi...... Bayan magrib tana d'akinta tana rusar uban kuka abinta shaam ya shigo,zama yayi kusa da ita da yace "Hafsat ni kikewa baqar magana??" bata kulashiba yace "Kinaso na ci gaba da lallasaki kenan?" budar bakinta se cewa tayi "ka lallasanin ai akwai Allah,kuma wlhy duk wanda yaci zalina Allah ya isa" mamakin kalamanta yakeyi "waye yake koyar dake rashin kunya hafsat?" nurguda bakinta tayi sannan tace "Wanda suke cin zalina kullum kuma Allah ya isa" miqewa yayi yace "hafsat kin janyowa kanki zaman bakar uquba a gidannan sabida kinga ina miki wasa shine kikemun wulaknci san ranki ko? Wato ke kin isa lallai kuwa zakisha baqar wuya a hannuna" bata kulashiba taci gaba da kukanta yayi ficewarshi yana mejin tsananin tsanar hafsat,tundaga wannan ranar kuwa shaam komai qanqantar laifi idan hafsat ta masa se duka har yakasance daga dazan ya sanyata abu jikinta ze soma rawa,kuma da sauri takeyi,sedai kwanakinnan batada lapiya ko kadan, da wannan ta sameshi tace dashi "Yaa shaam kwanakinnan da zazzab'i sosai nake kwana ko zakaje dani clinic dinka a dubani" kallon ta yayi ya rufe jaridar dake hannunshi " A matsayinki nawa zakijemun clinic? Kinga nawa clinic ma na masu matsalar zuciyane,sabida haka kije wani asibitin kawai" batace masa komai ba taje gun huda daganan suka wuce wurin mijin ta dayake shima likitane,binciken farko ya fito da tambarin heart problem ajiki,sosai sadeeq ya shiga cikin shock,huda ya fara kira a gefe yace "Baby wai anya qawarki ba kashe kanta takeso tayi akarin banza ba @kan soyayya kinsan kuwa ciwon zuciyane da ita,fisa bilillah @her age gaskiya bance ba'a samun irin wayannan cases dinba sabida yanzu irin wayannan cutukan sun yi yawa a wurin yarama harda hawan jini,amma ni tausayi take bani gaskiya me take sakawa a zuci har haka,jininta mafa hawa yakeyi" dafe kai huda tayi tace dashi "Hubby kasanme har fa dukanta yakeyi sannan ko kwanciyar aure bayayi da ita,ga school ga problem dinshi girki mafa ita kewa matarshi ko sau daya betaba kwana a bangarentaba,ga hafsat da zurfin ciki tacika barwa kanta abubuwa ni wlhy har naji kaina yana ciwo ma,yanzu meye solution?" dafe kanshi yayi yace "Amma gaskiya shaam ya bani kunya wane irin sakarai ne qanwarka guda daya matar da iyayenta suka nuna maka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44