Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,255 words 0 views Progress saved
Download Book

tata me aika jini me makon saqonnin fahimta akanta aikinta ze janyo wani matsalar,kodai lalacewar ido,kokuma ta kunne sabida haka sekun saka haquri a lamuranku" kuka shaam ya saka tamkar wani qaramun yaro sabida shi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak,tayaya ze kalli su abbba da daddy da wannan zancen? Ina courage din? Menene ma mafita agareshi?" A yanda ran Abba haris ya baci idan wani abun ya samu hafsa agarin aikinnan ai tsaf ze tsine masa wlhy kowa ya huta,dak'yar Dr.sayyed ya rarrasheshi yabar asibitin.... *Ur vote is important also ur comment fan's,inasanjin ra'ayoyinku,i hope ur enjoying this story* Mom Nu'aiym[1/21, 9:43 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 12 Dr.sayyed tunda yaje gida yake tunanin yanda zasu b'ullowa lamarin hafsat,haka kawai ya tsinci kansa da tsananin tausayin yarinyar,indai har acikin halin hauka bata manta muguntar da yake mata tokuwa lallai abun ba qaramun abu bane yana cutar da ita over,sam bayaso wani abu ya tab'u a jikinta kuma yasani sarai chancess na rashin samun hakan ba qaramun abu bane, yanaso ayi aikin as soon as possible amma fa sam bayaso ayi garaje a samu matsala....... Shaam kuwa koda yaje gida masa bacci yayi,bangaren zuciyar sa na masa zafi akan abinda yaji da kunnensa haleemah na fad'a itada uwarta,yayinda dayan bangaren na zuciyarsa ke masa rad'ad'i akan abunda abbansa yace dashi akan hafsat,wani dogon tsaki yaja yace a asarari "Gaba d'aya wannan hafsat d'in ta jamun masifa wlhy,dabadan ta maqale akan seta aureniba wlhy daban shiga wannan mugun yanayinba,ita kuma haleema yaya zatamun haka?? Ina sanki sosai haleema ko baki sani bane" a haka ya dinga sambatu shi kadai harna shirme....... Dr. Sayyeed da kanshi yayiwa su Abba bayanin rashin lapiyan hafsat da kuma da kuma abinda yake hange idan har aka mata wannan aiki,fatanshi d'aya ayi aikin lapiya kuma adu'arsu itace abun nema" Babu yanda suka iya dole su yarda da akan ayi aikin dukkuwa dayake Abba haris yaso a fita da ita waje daddy ne yace duk inda akayi aikin nasara a wurin Allah take,da wannan aka tsaida ranar aikin nan da sati d'aya...... Hafsat dai tana nan jiya iyau,ba abinda ya ragu har yau ba hankali akanta,yaa shaam tunda suka yaji wannan zancen nasu haleema seya kirata yace ta zauna gidansu se bayan sati biyu zuwa lokacin hankalinta ya kwanta dama kuma hakan takeso ya sanya ta kwantar da hankalinta tayi gidan bokan ta.... Sati ya zago Aka shirya shiga da hafsat tiyata yaa shaam har kuka yayi abubuwa sun taru sun masa yawa yanzu ya tabbatar wa kansa cewar abinda yaji gaskiyane,coz kwana kusan uku baya samun number wayan haleema kuma koyaje gidansu se a ce masa wai batanan sunfita da momy........Aiki dai anyishi cikeda nutsuwa da kuma na sara an samu damar kwashe duk wani jini daya taruwa hafsat a kai, yanzu jira kawai akeyi ta farfad'o, a ga yanda zata tashi...... Umma da momy sunyi jigum jigum suna adu'ar farfado war hafsat lapiya,se suka jiyo maganarta sama sama "Saro kunna mun fitilar d'akin nan kuma ki bani ruwa" kallon juna su umma sukayi sabida su sam basusan da wani zancen wai za'a iya samun matsala ba,da sauri suka miqe atare sukayi kanta,umma ta riqe hannunta tace "Sannu hafsat ai ranane aikin da'aka mikine akai,inaga lallai alluran nan ne be sakeki ba shiyasanya kike ganin duhu,sannu kinji" Shiru tayi tafara tunano abubuwan da suka faru da ita ita dai bata jin wani jiri gashi ta tabbatar wa kanta cewar idonta abude yake yama za'ayi ace wai allurace,amma seta kama bakinta tayi shiru kawai tana me mamakin har meyake damunta daza'ace wai ammata aiki akai,wasa wasa hafsat haka ta wuni ta kwana bata gani zuwa wannan lokacin har su momy sunsan halinda ake ciki kowa ya sakata agaba har Shaam tana bacci tana farkawa tace "momy zansha ruwa?" ruwan momy ta bata tasha sannan ta kwantar da ita gyaran kwanciya tayi tace "Momy dan Allah wai se yaushe gari ze waye ne,ni nagaji da ganin duhu idan ma garin be waye ba ku kunna mun fitila" D'aukacin mutanen d'akin suka saka kuka sabida tsabar tausayi daddy ne ya qarasa gunta yace "Hafsat nasani maganar dazan fad'a miki zaki jita wani iri kuma tabbas zata tayar miki da hankali,amma inaso kiyi hakuri ki yarda da khaddarar Allah ya d'aura miki,khaddarace ta sameki sakamakon dukan da yayanki yayi miki wannan ne ya sanya kanki ya samu matsala na tab'in hankali, to agarin yi miki aikine kuma wata khaddarar ta sake samuwa gashi dai munyi nasara hankalinki ya dawo jikinki amma an tab'a miki wata jijiya aka wacce tayi sana diyar lalacewar idonki yasanya kika dawo makauniya bakya gani" shiru tayi kamar yanda kowa yayi shiru tamkar bataji meyace ba secan hawaye ya fara gangara daga cikin idonta da suke abude bazaka taba cewa basuda lapiyaba ,batayi magana ba wannan ya sanya kowa ya sanya bakinshi ana bata baki seda taji kowa yayi shiru sannan ta sanya daya hannunta dabashida ruwa ta dafe qirjinta tace cikin d'aga murya "meya sanya a rayuwa nayi rashin sa'an zuwana aduniya? Meya sanya wannan baqar zuciyar tawa takesan mutumin da yafi qaunar mutuwarsa akan ya d'aura idonshi koda akan me ita,meya sanya a rayuwa sam na zab'i bak'in cikina akan farin cikina,meya sanya zuciyata keson wanda bashida buri illah yaga qarshenta,lallai ina cikin tashin hankali ba adadi,lallai yaa shaam da inada ikon raba wannan wahalalliyar zuciyar tawa da k'aunarka wlhy da nayi a yanzu,inama ace inada ikon raba raba rayuwata da ruhina ko zan huta da wannan baqar soyayyar da batada ci gaba ko kad'an seci baya,ina ma ace zan iya sanya hannu in lalubo inda rad'ad'in sanka yake inyi wurgi dashi,kaico na dana zab'i abu mafi muni arayuwata,kaicona dana zab'i mummunan k'haddara da hannuna khaicona dana siyo makancewar idona da hannuna kaicona ni hafsatu,kaicona ni lelen daddy da Abba" wani razanannen kuka ta saka me tsuma zuciya wanda baya misaltuwa duk kuwa cikin d'akin aka rasa me rrrashinta.......Dr.sayyeed ya tabbatar musu da cewar matsalar bame yawa bace idonta ze iya bud'ewa yanzu,ko gobe ko anjima ko wata ran ko wata shekara kokuma har abada,Allah shine yabarwa kansa sani,haka hafsat tayi wata daya a asibiti gashi sam ya kasa yiwa halima komai sabida san dayake mata kurin dai ya qaurace mata kuma sannan be nuna mata komai ba,har aka sallami hafsat ta koma gidan Abba haris. A gida Abba haris yayi kiran shammaz agabdan daddy da momy ya kalleshi cikeda nutsuwa yace "shammaz abinda yasanya nayi kiranka ba komai bane illah zancen komawan hafsat d'akinka wato gidan auren ta" Da sauri ya d'ago ya kalli abba yace dashi "Abba nifa na rigada na saki hafsat kuma bance zan maida ita ba wane komawa kuma zatayi,kurin dai Allah ya bata wani mijin ta aura" cikeda mamaki kowa ya kalleshi wannan karon har daddy abba yayi karfin halin cewa " Ai wlhy tunda ka nakasa ta seka zauna da ita,so kakeyi ka gama lahanta mata rayuwa" cikin bacin rai yace " Haba abba nifa ba qaramun yaro bane,sa annan kuma zakuce zakumun dole,yarinyar ban sota tanada lafiyaba se yanzu,dan Allah na rokeku

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44