Chapter 33
Chapter 33
a cikin wannan kirjin nasa,haka ya janyo man shafawa ze shafa,ita ta karb'i karamun towel ta goge masa jikinshi sannan ta shafa masa mai d'in,kayan baccin data ciro masa ta bashi ya karba yana murmushin da sam,yakasa daukewa a fuskarsa,da sauri ta bashi wuri tayi waje,a parlor ya taddata koda yaga pizza kallonta yayi "Daga ina kikayi ordering pizza,na season 7n kawai nakeci" kallonshi tayi ordering kuma sekace banida kayan had'in pizza d'in? Ni na hadashi ba dadewa fa" kallon mamaki ya mata "A ina kika koyi girki?" ya wurgo mata tambayar "A wurin mama na,kuma a india naje ctring classes yafi a irga,wasu zubin idan muna hutu ban dawo ba senayi joining,i so much like cooking ai" jinjina kanshi yayi yana me jin dadin yanda yake cin girkin matar daya ajiye a matsayin tashi,tunda yake so daya tak zainab ta dafa masa spag ita dinma san beci ba sabida ba taste kowa abincin cook yake ci,a parlor suka zauna kallo bayan sin ida,matashin kai tayi da cinyarsa anan bacci ya dauketa, se wuraren 11 ya dagata cak zuwa bed room nashi, sosai ya rungumeta ya kwanta shima....... Haleemah kuwa kwana bakwai da auren shaam ta dira niger,kuma a gidansu tafara sauka anan takejin mugin labari,aikam qungiya guda sukayi zuwa gidan amarya domin ciwo kan ubanta danye lolxxxz. Yau satin hafsa daya kenan a gidan muhammad sukan ci atare susha atare kuma a haka zasu kwana wuri daya,amma fa sam ba wani mu'amalar aure dake shiga tsakaninsu,sedai kullim kwanan duniya tana qara samun wani babban matsayi a zuciyar muhammad har yakeji baya iya daukar a wanni biyar batre daya ganta ba,yauta shirya zataje gidan shaam da gidan Abba haris,izini yamata akan ta karbo key na motarsa Avensus wurin zeezee sabida duka keys suna bangarenta taje da kanta tunda tace tare dasu momy zasuje gidan shaam din harsu khairii ma,koda ta aika wai bazata badaba,kai tsaye taje da kanta ,a zaune ta tadda ana matsa mata kafafu ta kalle ta sama da kasa tace ."Zainab key na Avensus fara zaki bani zanje unguwa" "shi me gidan naki be sanar miki cewar ni ce nakeda ikon komai da kowa ba agidannan,kice hajiya kuma ki durqusa ki rokeni key sannan zan baki" wata dariya hafsat tayi ta juya abinta zuwa waje,kallon driver na gidan tayi tace dashi "A waccen benz da key ke hannunka akwai mai ne?" kallonta yayi ya gyada kai,miqa masa hannu tayi kawai ta karba tayi gaba,tana tashin motar ta saisaita kanta sega zee tafito tana masifa ko kallonta batayi ba,tazo tasha gabanta aikam hafsa tayi cikin ta seda ta fadi sannan ta kauce tayi gaba abunta....... Topha koya zata kaya,su haleema sunyi qungiyar zuwa gidan shaam gakuma su hafsat zasuje koya zata kaya ohoo Vote and comment [2/16, 9:28 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 29 Bayan ta d'auki su momy kai tsaye gidan shaam suka wuce,mota biyu sukayi kuwa,mamakin ganin motar gidansu haleema sukayi,kallo d'aya momy ta musu ta tabbatarwa kanta cewar ba lafiya,umartar kowa tayi dasu fito da sauri aikam a take suka fad'a gidan, mamakin ganin da sukayi su haleema sun saka maryam a gaba ta zuqa zuqan durina da kuma sanduna wannan ya mareta tanan wannan kuma ya mareta tacan,ita kuwa bakinta be mutu ba,se tambaya take su waye,da sauri momy tashige tsakiyar parlor d'in ta d'agata,mahaifiyar haleema ce ta wanke momy da mari kai tsaye,cikin fusata ta furta "Tsohuwar banza la'ananniya banda iskanci tayaya danki ze qara aure matarsa ta farko bata sani ba sannan ku baku nuna masa kuskuren saba? Aikam hafsa kukan kurciya tayi ta yanke uwar haleema da mari,daganan kuwa dambe ya kaure mahaifiyar shaam ta asali dayake tare ake da ita tashiga rabawa amma uwar haleema ta sharara mata marin gaske itama me kyau kuwa,aikam su khairi ma suka shiga damben,karamar su ce yar Aunty dinsu sumayya tayi wayon fita ta kira yaa shamm,dama yana hanya ya kusa karasowa,koda yazo kuwa se dukan iyayenshi akeyi agaban idanshi haleema batare data ganshi ba ta yanke momy da mari,babu yanda beyiba amma dangin haleema se dukansu suke da itace da dorina,kai tsaye dpo yayiwa waya akazo da motar police gida uku, kai tsaye aka wuce masa police station dasu haleemah da mamansu, su hafsa kuwa ansha duka jiki duk yayi tsami,dama mana dambe da yan tasha kai kuwa bawai saba wa kayi ba lolxxx... A station kuwa mamaki Shammaz ya baiwa halima domin bayaninsa cewa yayi wai sata take masa not knowing that takardunsa gaba daya na kadarorinsa original ones din suna bank,wayanda ke gida kuwa dukta sace tayi garkuwa da su,azatanta wai sune manyan sannan sunje har gidansa domin su kashe masa mata da iyayan sa,inta qaice muku qememe yace kotu zasu shiga..... Hafsat kuwa koda ta dawo gida a gaban gidan ta, ta tarar da Zainab ana mata matsar k'afa,sosai ta tamke fuskarnan tamau sannan tazo ta rab'a ta gefensu zata wuce,janyo hannunta zeezee tayi ta dawo gabanta "Ke baki iya gaisuwa bane? Ko bakya ganin mutane?" dan murmushi hafsat tayi sannan tace cikeda kasala "Zainab dan Allah kinga nifa bawai a makarantar karnuka aka haife niba,bakya gajiya da backing ne wai kekam? Irin wannan haushin dakike karnuka ne suke yinshi,kuma idan kin kula da kyau zakiga cewar su d'in dabbobine bawai mutane ba ni kuma mutum ce,sedai banida tabbacin koke kinada maraba dasu at all" miqewa zainab tayi ta d'aga hannunta da niyyar sharara mata lafiyayyen mari,se kawai hafsat ta riqe hannun nata ita ta wanka mara marin sannan ta cillar da hannun "Idan agidanku ba'a koyar dake gir mama d'an adam ba ni agidanmu an koyar dani,idan ke a gidanku ba'a koya miki zaman lapiya ni anamun bansan ma meye tashin hankali ba,wlhy zainab zanci uwar me garinku idan kikayi gigin taba'ani and karna kuma ganinki a k'ofar gidannan sabida bawai gidan ki bane nan din kinaji ko" shaqo rigar ta zainab tayi "ke dan ubanki ni zaki mara?wlhy yau sena hallakar dake shegiya me mugun bakin hali sati daya da aure anje gantale banza karuwa me aure aure kin kashe wanda zaki aura kinzo cin dukiyar dan tsohon gwamna,adaidai wannan lokacin muhammad yashigo gidan ya dawo daga masallacin sallar isha,da sauri ya karaso ya b'anb'are hannun zainab,yace yana kallon ta "Zainab karna kuma ganin ana shirin dambe agidan nan,kuma mesa zakizo nan part d'in banda neman fitina,wato dama jira kike ta shigo ki mata rashin m ko?" a kufule ta kalleshi "Yarinyar tayi niyyan kashe ni,hawa ta kaina taso yi da mota fa,wannan ai raini ne ma wlhy" kallonta yayi sosai ya kalli hafsat,ba agaban mutane yaso ya nuna mata kuskuren taba amma seya kalleta "Mesa kikayi niyyan hawa kanta da mota,cewa akayi dani seda ta kauce dagudu sannan tasha,atemted murder kenan fa,kuma kin sani" kallonshi tayi "Idan dai kasan ma'anar atemted murder ya kamata ace matsayin ka na babban lauya kasan ma'anar suicide,wanda suka gaya maka basu sanar maka mota na tafiya tasha gabanta da gangan ba? Ni ai hanya tace kuma tana sani ta kara tome zan mata" shiru yayi sabida yasan halin zeezee zata aika,sannan ya juya a hankali batare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44