Chapter 40
Chapter 40
tashi yaga hafsat gaba daya ta fito da akwatunanta ta jere ko saman mirror dinta ba komai ta kwashe komai, kallon mamaki ya mata "Hafsat lafiya dai?" murmushi ta sakar masa "kacika mantuwa yaa muhammad,yaufa watanni shida cur da auren mu" mamakin aane ya qaru yace "To shine me hafsat?" juyowa tayi da kallon raini,da cikinta daya rigada ya fito tace "Gadai takar danmu nan na agreement,lokaci ya cika watanni shida,kuma indai ba neman magana zan tsaya yiba meye ze kaini kuma zaman dole,tunda har yau bakaji kana sona ba,kuma baka tab'a furtawa ba,kaga dama alqawari na maka cewar idan wata shida ta cika bakaji kana sona ba kuma baka furta ba,zan sake maka mararka kayi fitsari gidanmu zanje ka sauwaqe mun" wata iska me zafi yaja ya kuma fesar sannan ya dafe kanshi ya miqe yazo kusa da ita ya dafa kafadarta "Haba hafsat,yanzu ke dama da gaske kike wannan maganar" dago itanta tayi ta saka acikin nashi.."Da ana wasa da agreement da akayi arubuce har akayi sign ajiki? Kokai sanda mukayi na aure dakai ka manta ne,kalleni muhammad wlhy bari kaji inna zauna dakai baka sona shegiya nake,yaronka dakake tafadar kanaso kuma rabone,inshaa Allah zan baka abunka ina haihuwa so ka aikomun takardana danni yanzu gidanmu zani. Mom nuaiym [2/22, 9:11 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 34 Qura mata muhammad yayi gama daya ta gama rud'ar dashi,kanshi se wani juya masa yakeyi yama kasan cewa komai "Nace ka sallameni malam nikan hanya nake nakuma rigada na shirya" zuwa yayi gabanta yana kallonta kallo daya zaka masa ka gano cewar hankalinsa baya jikinsa "Baby meye haka wai? Nine nace dake bana sanki? Wlhy ina sanki hafsat ina sanki sosai ba kadan ba,tun ranar dana fara ganinki naji ina sanki dan Allah ki janye wannan maganar" murtuqe fuska tayi "Na rantse da Allah yau senaje gidan mu, tayaya ma kai bakayi wasa da agreement namu na farko ba ni zanyi yanzu,ka manta roqon dana maka amma ka nace ko ka manta har tsohon my suruki to be yaje ya roqeka amma kayi mirsisi shan sigarin akuya,wlhy Allah tu da baka sona yau sena tafi" zare idanshi "Hafsa rantsuwa fa kike ta kwalawa? Cewa namiki bana sanki wlhy ina sanki sosai fiye da tunaninki,bakya ganin yanda nake kula wa dake hafsat na?" shwqeqe ta kalleshi ."kake dai kulawa na cikinka dake jikina J.A amma bani ba" mamakin jin takirashi da wannan sunan ya kasheshi a tsaye ya kasa koda motsi, haka taja akwatunanta kwaya biyu tayi gaba dasu se waje,shikam ma yana tsaye a gun tamkar an dasashi yakasa koda motsi sabida sam be kawo zata masa hakan ba,kuma ya hango seriousness a idanta,mota ta figa tsiyace tayi waje....... Gidan Abba haris tawa kanta masauki, a gaban gidan ta ganshi zaune yana karatun news paper,ganinta da akwatuna ya sanya gabanshi fad'uwa sabida dama suna tsammanin badan Allah yayi wannan auren ba,da sauri yazo ya karbi daya sukaje parlor seda suka gama gaisawa sannan yace "Lapiya dai kuleken abba da asubannan da akwatuna haka?" murmushin qarya tayi "Abba dama zeyi tafiyane kusan wata biyu, shine yace tunda lapiya be ishan ba nazo gidannan kanya dawo" wani ajiyar zuciya ya sauke sannan yace yana fara'a "Lallai kam hakan ya dace tunda kinyi nauyi" haka tashiga ciki se murna su khairi keyi dajin zata musu watanni biyu. Tunda safiyarnan yake kiran wayanta baya samu duk ya damu,da yamma ya shirya yaje gidan daddy a tsammaninshi tana can,ganin an masa tarba me kyau ana tambayar sa yasu hafsa se jikinsa ya qara yin sanyi, haka ya musu sallama sannan yafito ya nufi gidan Abba haris, koda abba ya ganshi mamaki yayi don kuwa hafsat cewa ta masa yama wuce,ya kalleshi bayan sun gaisa yace dashi "Ashe ka dawo,tace damu watanni biyu zakayi a tafiyar shiyasa kace tazo gida,ko tafiyar ta fasu ne?" Take ya gano b'oyewa iyayen ta gaskian maganar tayi sosa kanshi yayi "Ea wato Abba tafiyar ce dai ta fasu, shine harnaje kaduna na dawo senan da sati daya" "A toto Allah ya kaimu,tana ciki kuwa bismillah kaje parlor na na maka kiranta" haka ya wuce jiki a sanyaye yana yaba wayo irin na yarinyar wato ma cewa tawa iyayenta tafiya zeyi,yana zaune ta shigo tana turin ciki,ko sallama bata masa yau,kallonta yayi tazo ta zauna nesa dashi sosai, tasowa yayi cikeda da tsanaki ya zauna kusa da ita ya kamo hannun ta yace "Mesa zakiwa Abba qarya? Mesa bakiyi maganar ainahin abinda ya faru ba?" turo baki tayi tace bayan ta had'e girar sama data qasa "Kai ba kanada baki ba,mesa baka sanar dasu takardar sakina ka cike ba idan mukayi wata shida da aure,ka sani wlhy muhammad bazan maka lamuni ba,nika rubutamun takar dar saki na in huta da wannan rayuwar" Sassauta murya yayi yace "Haba mana hafsat na,dan Allah ki dena wannan zancen,tsakanina dake har gaban abada muna tare,mutuka raba" kallon shi tayi "yaa muhammad kasan wai me ake nufi da haqiqani? Tofa ni iyakar gaskia ta kenan,sedai kotu ta raba mun aurena dakai" Langwab'e kanshi yayi ya qasqantar da kai " Hafsat dan Allah kiyi hakuri,wlhy kece hasken rayuwata,kuma ki dena cewa bana sanki wlhy nafi sanki fiye da kaina da komai ma" Miqewa tayi "Ni banida lokacin ka,kaje ka aikomun da takardar sakina" ta barshi gun a zaune tayi ciki, a kunnen Abba yaji komai,yakuma fahimci da matsala karya suka masa,bari yayi yaga iya gudun ruwansu dukansu danya fahimci muhammad bawai niyyar sakin ne dashi ba. Haka dai muhammad yafi sati biyu yana yawo kullum seya yiwa hafsat magiya,sunbar su Abba akan yana zuwa dubata ne wai ayyuka sun mata yawa gwara ta zauna anan,yaudai dayaje yaga hafsat borin nata yafi na kullum se kawai ya wuce gidansu,kai tsaye part d'in mahaifiyarshi ya wuce tana zaune ta idar da sallah,kallonsa tayi tace "Baban mamana lapiya dai?" dafe kanshi yayi yace "Ammy Hafsat ce" da mamaki ta kalleshi "Meya samu hafsat me sunan me gida?" Hawayen daine suka kwaranyo daga idanshi dayaketa tarewa,kwashe komai yayi ya sanar da ita tun daga farko haduwarsu har kawo wannan abun daya faru "Haba me sunan me gida,tayaya ina ganinka da hankali zaka aikata hakan? Da iliminka da komai,zaka je kayi auren yarjeje niya hadda kafewa da iyayen yarinyar suma roqeka,shiyasa mana akayi aure cikin qanqanin lokaci wlhy ka bani kunya kuma ni maza ka bani wuri" da sauri ya d'ago ya kalleta yace cikin rudu "Ammy karkimun haka,kece gatana banida kowa seke,dan Allah ki baiwa hafsat hakuri wlhy Ammy ina santa sosai bazan iya zama babu ita ba" kallonshi tayi sosai ta jima tana nazarin kalamanshi sannan da yanayin shi,saboda bazata iya tuna when last taga yana kuka ba lallai lamarin babbane "Yanzu ya kakeso ayi?" "Ammy kije ki baiwa hafsat haquri,cewa fa tayi lallai sedai muje court" kan wani yayi magana se kawai wayanshi yayi qara,hafsa ce da sauri ya d'aga sabida batama d'aga wayarshi "Wai kazo inji Abba haris" tafada da kukan ta da komai,gayawa Ammy yayi ta ce ya jira suje tare. Koda sukaje Abba haris fad'a sosai yayiwa muhammad da hafsat sannan yace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44