Chapter 1
Chapter 1
[1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha. *Wannan shafin nakine 'Yar uwata Hafsat Elham, Allah yabar mana zumuncinmu, Yakuma albarkaci rayuwarki Ameen* 01 Hafsat!! Malamin nasu ya daka mata tsawa,d'aukacin yaran class d'in sun tsorata da wannan tsawar amma Hafsat ko'a jikinta a zahiri ma ko d'ago kanta batayi ta Kalli malamin ba, zuwa yayi cikin azama ya daki teburin da take Kai yace cikin fusata "How dare you! Are u stupid? " a hankali ta miqe daga zaman datake sannan cikin ko inkula tace "No sir I'm not" cikin qaraji yace "what!! Repeat what u just said now" cikeda kwanciyar hankali ba alamun tsoro tattare da ita tace " I just say I'm not sir" murmushin mugunta yayi dama yana jiranta a cike yake da ita fam "Hafsat look into my eyes and repeat after me OK? "batayi magana ba ya kuma cewa "oya say that you,you are stupid " wani shu'umin murmushi tayi sannan tace "You! You are stupid!!!! " zaro idonshi yayi sabida ba haka yake tsammanin zatace ba yace " How dare you, are u in ur senses? " ita d'inma cikeda raini tace tana Zare ido Kamar yanda yayi tace " How dare you? Are you in ur senses?? " cikin azama ya sanya qaton hannunshi irinna yarbawa ya zabga mata lafiyayyan Mari seda taga jiri dafe wurin tayi ta saka kuka aikam malamin se wani cicika yakeyi irin ya hasala, hanyar fita waje tayi Kai tsaye office na principal nasu ta nufa Tanata uban kuka irinna shagwab'abb'un yarannan marasa ta ido, PC na ganinta ya miqe tsaye ya sani idan ba'ayi sa'a ba lokacin korar wani malamin ne yazo "Hafsat lapiya me kikewa kuka haka? Meya sameki?" tana kukan ta kwashe qarya da gaskiya ta sanar masa, a haka aka tarar wa malamin sanda ya bata haquri sannan tace ta yadda bazata fad'awa daddyn tab'a, domin kuwa mahaifin nata shine mamallakin makarantar kuma itadin yar gatace gaba da baya ba Wanda ya isa ya taba Hafsat Poojah ya zauna lapiya mahaifinta be had'a kowa da itaba kasancewar ita k'adaice 'ya d'aya tilo da Allah ya bashi se kuwa yayan ta shammaz...... Class dinsu ta koma,dashigarta mazan class d'in suka dauki ihu,pooja!pooja!pooja!....wani Yaro dan masu ji da naira nalura yana dai daga cikin taqadarun students d'in makarantar yace, Poojah babe ina fatan kinsa an lallasa wannan malamin?, Abokinsa Wanda duk halinsu d'aya yace, Ni bama Sonai takaishi Kara ba, Sonayi itama ta kifa masa Mari ya za'ayi tana yar me makaranta ya Mareta?, Haushi taji yadda yanuna rashin gamsuwarsa da abinda tayi, wato ma bata burgeshi ba harara ta kwadamai kafin tace, Banga damar ramawa bane,kaima kasan inkifa masa Marin yana dai daga cikin kananun ayyukana kamar yadda Kaima baka wuce in zabga MA Marin ba mtswww, Baki asake yake kallonta se Abokinsa wizkid Yasoma ihun kiran sunanta,poojah!poojah!kina burgeni wallahi, Cikin halinta na basarwa tace, Dalla kuyi mana shiru ninagaji da wannan banzan hayaniyar naku, Sum sum mata da mazan dake a tsaye suka Nemi mazaunin su batareda sunyi magana ba, Wannan shine kadai aikin hafsat a makaranta taga damar submitting plane sheet lokacin exam kuma duk teacher Dinda yai failing dinta ze rasaa aikinsa ne bakuma Dan wai batasan mezata rubutaba sedan kawai ta nuna isa da tantagaryar shagwab ganin makarantar ta mahaifinta ne kuma baya ganin laifin ta aduk shirmen dazatayi, 1:50pm aka Tashe su tun daga sama ta leqo bata hango motar driver dinta ba, tafiya take bata kallon gabanta hartagama saukowa daga stairs d'in be k'araso ba,tafiya take Tana tunanin hukuncin dazatayi wa Ayuba yau,tana isa gate segashi yazo dasauri yazo ya Karbijakarta ya sa bayan motar itama yabude mata tashiga Se cin magani take, Wallahi tallahi tayarce tayi faci dan Allah kiyi hakuri karkisa narasa hanyar cin abinci na,ayuba yasoma bata hakuri bayan yashiga motar, Wannan shine babban kuskuren daka tafka banaso kadamu kunnuwana dawannan kalmar tahakuri Dan bawai zan yibane, Gumi yake ta ko'ina,shine gatan kannen sa da mahaifiyarsu,wannan aikin dayake ciyarda su dashi, Dagudu ta k'arasa wurin daddy ta tana kuka, Lafiya dai Hafsat waye yataba min ke?, Daddy wannan ayuban ne yabarni har Nazo gate dakafa, Subhuhanalillahi, Ayuba dama Kai ya akayi haka?, Wallahi ranka yadade tayarce tayi faci kuyi hakuri, Sautin kukanta Takara, Tsaya Hafsat me kikeso ayi yanzu? Daddy ni akoreshi banasonshi, Kudubi girman Allah kiyi hakuri insha Allah wannan shine nakarshe bazan kuma irin hakaba wannan aikin shine hanyar abincina, Furr taki saurarensa daddy yace to za akawo miki sabo kaikuma Ayuba zaka ringa fita da hajiya dakumawanke motocin gidan, godiya yayi yajuya yana godewa uban giji daya sanya dukda kasancewar hafsat batada m mahaifanta nagartattun mutanene dasuka san girman dan adam matuka.... A tsakiyar parlor ta fara wurgi da jakarta da sannan tacire takalminta a hanyar dazata sadata da matattakalar benen gidan komai a inda ta samu take wurgi dashi gata da tsafta amma bata farin cikin ganin masu aikin gidan suna hutawa,mero me aiki ce ta sameta a daki tace bayan ta saka kayanta da tabi ta tsinto akasa cikin laundry basket ta ajiye school ba da sandal a ma'ajiyarsu " kulelen daddy yau me kike sha'awar ci??" ko kallonta batayi hakan ya tabbatar wa mero bawai kulatan zatayi ba sabida indai da sabo toko ta saba da rashin kunyar Hafsat,wannan ya sanya ta juya kawai taje ta hado mata snacks da apple and avocado smoothie ta kawo mata a saman table na coffee chairs dake a parlor dinta ta ajiye mata sannan ta kalleta tana zaune tana danna remote domin canja channel tace da ita " Hafsat ga favorite dinki nan na hado miki" a wulaknce ta kalli kayan tace "Grill fish and chips,plus sugarcaine and apple juice nakeso ni kenan kullum fulawa so kikeyi na zama bom bom adena yayi na" shiru mero tayi se can tace " ki daure ki dan rage yunwa da wannan sena hado miki wancan din" harara ta wurga mata "nace baran ciba ana dolene?" kwashe kayan mero tayi ta juya tana girgiza kai a hakan ma wai meron kadai ke shiri da ita acikin yan aikin,kuma itace abokiyar hiranta sabida tana mata gatana, itadin ta kasance abokiyar wasan mahaifiyanta ta wurin uwa auren wuri aka mata a qauye Allah yawa mjjin rasuwa itadin bazata wuce shekaru ashirin ba aduniya sedai akwai kaifin hankali,kusan shekararta goma agidan tun hafsat na yar shekaru hudu,sun shaqu sosai da ita. Koda ta dawo daga school mamakin mutanen data gani birjik a kofar gidan tasomayi mafiya hawa daga cikinsu 'yan gidena ma'ana y'an uwansune,bata wani kawo komai arantaba tazo zata wuce su,abba haris ta gani da gudu ta ruga ta fad'a jikinsa tace cikeda shagwab'a "Abba haris zanbika gun ummi" murmushi yayi yace "kulele ai bakui hutu ba,ina saura kwana bakwai kuyi hutu? Bazan ma turo driver ba da kaina zanzo na d'aukeki" murmushin itama tayi sannan tace "To abba zaka sauya mun waya? Anfa dena yayin tawa?" "Lele ai dole na sauya miki yanzu blackberry bold 4 zan siya miki,an dena yayi curve dinnan" tsalle ta kuma ta fada jikinnshi sannan tayi ciki aguje,tab'e baki shammaz dake tsaye yayi wanda akanshi akayi wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44