Chapter 21
Chapter 21
yananyinsu ai yau taga sauyi sosai awurin dukkansu musamman Sayyeed dabaya iya d'auke idanshi akanta duk wani zumud'i yake ji...... A hanya yau hafsat gaba d'aya ta kasa sakin jikinta dashi,hannunta ya janyo yace "'Yan matan uncle say yadai niyau tsiwar nakesanji sa shagwab'ar" batayi magana kurun dai ta juyar da kanta d'ayan gefen tana murmushi,hannunta dake had'e da nasa ya matse sosai da sauri tashiga janye hannun ta saka wata qaramar qara,tace cikin shagwab'a "Nashiga uku Uncle say dazafi wlhy" sake hannun yayi yace yana dariya "gobe ma kya kuma mun banza idan ina miki magana" batace komai ba,shima shirun ya d'anyi,se can taje bayan ya wuce wani samosa joint "Uncle say onions samosa zanci" kallonta yayi yace "sekin cemun baby tukunna" zaro ido tayi tace "Haba mana Uncle sayyeed" murmushi ya sakar mata yace yana kallon dayan gefen alokacin dayake shan kwanar barin layin "Kinwa kanki sekince Baby say zan siya miki komai ma" Turo baki sannan ta sadda kanta kasa a hankali tace "Baby" dariyar mugunta ya saki sannan yakuma cewa "Cewa zakiyi,Baby say zanci onions samosa" Kara turo baki tayi batai magana na yace "Bazaki fada ba na qara gudu kinwa kanki kenan??" cikin muryan kuka tace "Baby say zanci onion samosa" parking yayi ya mayarda hankalinshi akanta,sannan yace "kinsan Allah hafsat ba wasa a zancena akan wannan yawan koke koken wlhy semunyi fad'a ke ko wasa aka miki se kinyi kuka,bazan ma qara miki wasa ba" D'agowa tayi tace tana share kwallan " Im so sorry Uncle say,bazan kara ba" cikin kuka tayi maganan ko yanzu,shi wlhy dariya ma ta basa,itafa komai qarantar abu kukane,kannewa yayi yace "Oya call me Baby say again" tana kukan tace "Baby say" yace "Noo cewa zakiyi I love u baby say" kallonshi takumayi sannan tace "I love you Baby say" ta fashe da kuka" jiyayy kamar ya rungumota amma ba hali,ya tabbatar cewar lallai jitai kamar yace ta maresa dayace setace masa baby,yasani tanajin nauyinsa amma wannan ita kadaice damar dazeyi amfani da ita ta saki jikinta dashi mastayin saurayi seya ganar da ita amfanin suturta jiki dakuma yawaita ibadar mahaliccii.... Da wannan yace "kiyi hakuri dear,bazan kuma sakaki kuka ba kinji?" daga masa kai tayi tace "Tokimun matashin murmushi mana,dariya tayi gaba daya hawaye shabe shabe a fuskarta tace " Uncle say a murmushin ma akwai matashine?" dariya ya saki shima "Ea mana bagashi kinyi ba?" suka saka dukkansu...... Mom Nu'aiym [2/4, 9:26 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 19 Shammaz zaune a office d'insa duniyar habaki d'ayanta baqi take masa yarasa yazeyi akan zancen hafsat,sam mahaifinsa yaqi ya basa fuska,gaisuwar sa ma dak'yar yake amsawa,gashi gaba d'aya Haleemah ta gama rainashi zaman auren kawai sukeyi amma sam bajin dad'i har qasar take bari bada izininsa ba,yama rasa tayaya zeyi gashi dai hafsat yanzu kusan shekaru hudu da barinta qasar acewar Mommy ma takusa dawowa domin tace qasarta zata bautawa,amma duk inda yaje da zancenta ba sauqi har wurin hajiyar su wato kakarsa...... Sosai hafsat ta tara abubuwan burgewa ajikinta,yanzu batada wata damuwa ita da uncle say sambarka,duk da yabar qasar ya koma Niger amma koda wane lokaci suna maqale da juna awaya,sunyi wani sabo mara misaltuwa,kwance take acikin dakinsu tana karatun wani English novel me suna she's with me,khairii ce tashigo ta kalleta taja tsaki "Allah hafsa kin shiga ukunki kekam,wannan wane irin karatun jarabane kikeyi haka? Kinfasa tafiyarmu nanda kwana ukune, amma meye naki na tsayawa karatun wani banzan novel,kofa kayanki baki had'a ba wannan zumud'in na uncle say duk gulmane abaki kawai ya tsaya bekai zuciba" bata kula taba,kuma sarai tasani bawai kulatan zatayiba wannan ne ya sanya taja wani tsakin ta shiga had'a musu kayan har hafsat,se zumud'in ta takeyi ita kadai tana mitar san banza irin na hafsat.... *NIGERIA* Gaba d'aya hafsat gani takeyi tamkar mutanen dake yanga akan jirgin basu san ciwon kansu ba,sakkowa ajirki sekace wanda ya tasa tray na samosa agaba,se yanga sukeyi tamkar basa taka qasa,tun a airport na sultan muhammadu maccido dake garin sokoto ta fahimci sauye sauye da dama da aka samu a garin,idon tane ya sauka akan masoyinta uncle say,shekara d'aya kenan rabon data ganshi,takowa tayi a hankali taje har gabansa ta tsaya ta sakar masa lallau san murmushi,kankace meye wannan kuma idonta ya cicciko ta soma kwallan murnar ganinsa,a hankali ta furta "i so much miss u Baby say" murmushin shima ya sakar mata sannan ya ja hannunta ya riqa cikeda kulawa yace "Rose kukan kuma na menene,daga had'uwarmu zaki fara ko Baby?" murmushinta ta fad'ad'a batare data dena zubar wahayen ba tace "Uncle say bakada labarin akwai hawayen dadi? sune nake zubarwa tsabar murnar ganinka" Janta yayi suka juya se mota,dama shi kadai yazo tarar su suka shiga suka wuce gidan abba haris kai tsaye,se labarin soyayya sukeyi cikeda qauna da tsananin murnar ganin junansu...... Satinsu daya agarin aka tsayarda ranar auren say da hafsat nanda watanni hudu masu zuwa,dama can tun tana india akayi tambayar auren kowa ma yasan da zancen auren. *Bayan kwana biyar* Tun da hafsat ta dawo basu hadu da yaa shaam ba har yau,gwara ma matarsa sun had'u a gidan daddy,shi kuwa yana sani yake gujewa ganinta sabida gudun karya tayarwa kanshi cutar so da ta jima tana addabar zuciyarsa,yau dai seda ya kira qaninsa da safe ya sanar masa cewa suna gida sannan ya shirya zuwa gidan na daddy,bashida lamarin hafsat ta dauki al'adar waje bata fiya fitaba seda yamma,wannannya sanya ta zuro doguwar rigar jallabiya ja har qasa tasha shape da bakin mayafi da uban qaton madubin ido,lips dinnan sunsha red lipstick,a hankali take taunar cingam dake bakinta tana yamutsa fuska,yau sam setakeji tamkar batada lapiya driver din na parka wa tafito a yangace zuwa cikin gidan daddy cikeda yanga, A hot na gidan ta hango yaa shaam lokaci d'aya qirjin ta ya mugun dokawa,adu'a taci gaba da karantowa ta dauke kanta tamkar bata ganshi ba,murya ya d'aga yace "Hafsa zo zan" qirjin ne yaci gaba da mugun dokawa amma bata ko waigo ba, yi tayi tamkar bata jishiba, shikuwa ganin haka kuma yasan sarai tana jinsa ya sanya yayi saurin tasowa yafara takowa zuwa inda take,ita d'inma sauri ta qara amma ina kan ta isa kofar dazata sadata da cikin gidan ya rigata,tsayawa tayi cak ta runtse idonta ta sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,a hankali cikin sanyin murya yace "Hafsat ya kwana biyu" bud'e idonta tayi a hankali batare da tayi magana ba,tana kallonshi ta cikin gilashin idonta,ya kuma cewa "Bazak gayarda yayan naki ba?" hannu ta saka ta zare madubin idonta sannan ta lumshe manya manyan ida nuwanta tace "Yaa shaam ina wuni,ya kwana biyu?" murmushi yayi shima hade da daura hannunsa saman qirjinsa yace "Lapiya qalau hafsat yaushe agarin?" murmushin itama tayi tace "Au baka masan zanzo ba aikuwan na cika tara,seka biya" wani dad'i ne ya xiyar cesa ganin ta sakko,besan kuwa nan umarnin yaa say kawai take bi ba abun beyi wani damuntaba,dak'yar ma take masa murmushin,shikuwa se dadi yake ji ya kalleta sosai "poojan dady an girma fa sosai yanzu" murmushin takumayi tace "yaa shaam d'in daddy
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44