Chapter 20
Chapter 20
hawaye ya sanya ta danja baya a d'an tsorace,k'ura mata ido yayi itama din shi take kallo,zama tayi kusa dashi ta kalleshi cikin kulawa tace cinkin mutuwar jiki "Uncle me kuka kuma? Meya sameka haka?" d'an juyar da kanshi yayi yace "Hafsat suhaila na,suhaila na nake tunawa,yaushe zan samu macen da zata mayemun gurbinta arayuwa?? Wlhy ina matukar kewarta" tausayin sa ne ya kamata tace jikinta a mace "Uncle say dan Allah ka rage damuwar nan,idan kana wannan kukan mu kuma muce me? Batun yauba na kula dakai sosai kake damuwa da rashin ta koka manta cewar Allah wanda yafi kowa santa mahaliccin ta shine ya karb'e abarsa,kuma arayuwa ba'a tab'a barin wani dan wani kuma Allah shi yasan dalilinsa na dauke rayuwarta alokacin daka fi buqatarta,dan Allah kayi hakuri" kallon ta yayi yace "Na sani hafsat wlhy na sani narasa dalilin daya sanya na kasa cireta araina,kuma kullum tunanina a duniya waye zata mayemun gurbin suhaila? Waye ze soni kamar yanda suhaila take sona,wa zata kula dani kamar yanda suhaila take kula dani?" riqo hannunsa tayi sannan tace tana zubar kwalla "Nice nan zan maka dukkanin abubuwan nan daka rasa uncle say,meyasa bakasan kawa kanka adalci ne,had'uwana dakai had'in Allah ne sabida haka tun farkon had'uwa na dakai nakeji ajikina i meant for u and u alone,Ban tab'aji araina ina sanka ba ko kadan bantaba jin soyayyarka araina ba,amma kullum ina tambayar kaina menene k'auna? Banida mutumin danike matukar kewa sama dakai aduk fad'in duniyar nan,banida mutumin danike matukar tausayi aduk fadin duniyar nan sama dakai,banida wanda nakejin damuwar sa tawace har raina se kai kad'ai uncle say,banida wanda arayuwa nakejin tamkar zan rasa farin cikina idan yana fushi dani sama dakai,banida wanda arayuwa banida burin daya wuce naganni kusa dashi sama dakai,banida wanda nakejin zan iya sadaukar da dukkanin farin cikina akansa se kai kad'ai uncle say,banida burin daya wuce farin cikinka arayuwa,babu abinda yake qayatar dani se inganka cikin walwala,babu abu mafi soyuwa agareni se ganin farin cikinka inga kana dariya yafi komai saukarmun da nishad'i,a iya tunani wayannan abubuwan ba soyayya bace,k'aunace me zafin gaske,ada nayi tunanin so shine komai se yanzu danake rayuwa dakai na tabbatar wa kaina cewan so shirmene zallah,ada nayi tsammanin cewa akan soyayyar shammaz na shige halin da nashiga na ciwon zuciya se daga baya na fahimci cewar zallar mugunta,cin amana,cin zarafi dakuma wulakantanin dayakene ya sakamun ciwon zuciya,sabida soyayya ruwan shayi ce yana zubewa a qasa kuma sedai kanemi madarar ka rasa shimfidar ruwan banza kawai zaka gani a kasa,kauna kuwa kakkauran kindirmo ce sabida zubewar sa a qasa baze tab'a zama sanadiyar b'acewa kalarsa ba,itace nake maka zallarta,dan Allah uncle say ka k'aunaceni,dukkaninmu muna tsananin buqatar kulawar junanmu" sosai yake kallonta harya kasance ko qiftawa bayayi ya rasa dalilin sa najin komai tamkar a mafarki jikinsa gaba d'aya yayi sanyi,har yanzu hafsat yarinya ce bazata tab'a fahimtar saba idan yace mata kuma bashida hanyar daze bar zuciyarsa ta k'aunace ta sabida wasu manya manyan dalilai,batare dayace mata qala ba ya miqe yabar parlor d'in fuska kici kicin zuciyarnan sam babu dadi a jagule...... *kome hakan yake nufi,da Alama hafsat batada farin jinin masoya a duniya,ba wanda yatab'a cewa yana santa,sannan kuma ita sedai taso wannan taso wancan amma babu wata nasara,Allah ya temaketa dai,muje zuwa kuci gaba da bin alqalamin mom Nu'aiym..... [2/1, 8:32 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 18 Dafe kanshi yayi bayan ya kwanta yace cikin kukan dabesan sanda ya kwace masa ba "Meya sanya arayuwa Hafsat take shan wahala har haka,ina tsananin sanki hafsat amma bazanyi ganganci nuna miki hakan ba,kamar yanda bazan tab'a bari soyayya ta tayi tasiri azuciyarki ba,gwaramun haqura dake a matsayin mata akan narasa rayuwarki har abada.." kukan yashigayi kaikace qaramun yarone,ganin wannan bazata fiddashi ba ya sanya ya shirya zuwa gun amininsa kamal khan domin sanar masa matsalarsa...... "Kamal akwai damuwa fa babba wlhy,duk sanda na kwanta senati mugwayen mafarkai akan lallai idan har na kuskura na auri yarinyar nan se an kasheta har lahira,ni bazasu iyamun komai ba sabida riqon addini haka sukace amma wai itad'in alqawarine duk mesan tan daya aureta lallai se sun ga bayanshi babu ita ba tarawa da wani d'a namiji harta bar duniya ni sosai take ban tausayi wlhy,wama yasan ko wancan yayan nata hakance ta faru dashi,ni ina matukar san hafsat son daban taba yiwa wata 'ya mace irin saba a duniya,rashin adalci d'aya zuciyarta tamun na sanya ta qaunaceni,Bansan yanda zatayi da ciwon zuciya ba idan har naguje mata,kuma ni bazan iya cewa da ita ga abunda yake faruwa ba harga Allah" nisawa khan yayi cikin yaren india yace " Sam karka gjjeta,karkuma ka nuna mata baka santa,wannan ba abinda zeyi illah ya wargaza mata zuciya gaba daya,sanan ni ina abu d'aya ne cikin biyu,kodai iskokaine da ita kokuma asiri aka mata,danni bantab'a jin hakan ba se'a irin harkar iskan nan,nifa a nawa tunanin kabata lokaci,ka kula da ita ka nuna mata soyayyar dakake mata inyaso a hankali kana koyar da ita girman adu'a da tsare azkhar safe rana da dare dakuma yawaita yin azumun litinin da alhamis,kana ana yawaita yin salatin annabi ba adadi,idan ma iskane zasu bayyana kansu idan kuma asirine lallai Allah ze taimaka kaga abun ya karye" murmushi yayi ya daura hannunshi akan kafadar khan "Inajin dadin shawar warinka abokina,Allah bar zumunci hakan zamuyi ai dole ma". Tunda hafsat taga yananyin Uncle say se jikinta ya mata sanyi,dak'yar ta iya jan jikinta zuwa bedroom nasu,har akayi magrib da ish bata fito ba,har akazo cin dinner koda aka aika kiranta se cewa khairii tayi ta qoshi tasha fresh milk,ganin haka Uncle say ya gano damuwa tashi ga wannan yasanya ya janyo wayarsa ya rubuta mata txt kamar haka "My love i swer idan bakizo munci abinci ba bazan ciba nima,kuma na tabbatar bazaki so Uncle say naki ya zauna da yunwa,plss kizo I LOVE YOU". Kasa dauke idanta tayi daga message din tana mamakin kalamansa har ya kuma turo wani jinta shiru "Baby na dagaske fushi kike sabida namiki shiru dazu,tsabar jin dadin kalamanki ne yake shirin sakani kuka a dazun,kuma inajin kunyar nayi kuka a gabanki amma trust me i love you more than words can tell,plss com and hav dinner together with ur fam" Tana murmushin jin dadi tazo dining d'in ta zauna amma me tarasa dalilin daya sanya matukar kunya ya hanata had'ata ido dashi har abincinma ta gagara ci se wasa takeyi da cokalin hannunta,wayarsa ya dauka ya rubuta mata "Meye hakan kunyan wa kike kuma? Yauba shagwab'a kenan" karayin k'asa tayi da kanta bayan ta karanta message d'in amma batayi replyin nashi ba,murmushi yankumayi yace cikin message "u go and get set,we r going for a date" murmushin dake qarawa fuskarta kyau ta d'ago tana masa cikeda qauna sannan a hankali bayan sun had'a ido ta sadda nata idon k'asa lokaci daya taji tana masifar jin nauyinsa kuma ya mata kwarjini,miqewa yayi kakarsa ta kallesa tace "Bakaci komaiba?" murmushi ya sakar mata "Nida hafsat zamuje yawo ne,bamasan mu qoshi danyawa a gida,murmushin tayi itama bata tankaba,tun dazu ta kula da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44