Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,241 words 0 views Progress saved
Download Book

ta wlhy" tsaki yaja yace "wlhy ba wanda ya isa ya b'atamun qanwa ina numfashi haba mana daddy ni haka kayimun? Ni bansan wannan wane irinn qata kuke nunawa hafsat ba sekace a kanta kuka fara ganin 'ya'ya wlhy ni idan suka gama wannan jlce din sauya mata skul zanyi" momy zatayi magana daddy ya hanata "duk yanda kayi daidai ne shammaz na tsame hannuna a lamuran hafsat tunda magajinta yazo haj kema naki idone lallai idan kina taka masa birki zakija masa raini a gunta kuma kinsan ya isa da ita sannan kuma ke karan kanki nasha sanar miki zaki ruguza rayuwar hafsat ne idan kina biye mata,yarinyar nan tanada kokari sosai zama mu iya cewa gifted idan bakya nuna mata muhimmancin karatun watsarwa zatayi" shiru momy tayi badan ranta yaso hakan ba daganan daddy ya daga hafsat ya bar gidan gaba daya,a gaba shaam ya saka hafsat har wurin mota yayi kiran driver din yace "Daga yau ita zata riqa bude mota da kanta tashiga sannan karna kuma jin kace mata wata hajiya karama,kuma ita zata riqa gayar dakai ba wai ka gaidata ba,yarinya sa'ar y'arka zaka zauna kana wa biyayyah kuma kullum idan tawuce 7/30 batazo kun wuce skul d'in ba kazo ka sanarmu" tana kuka tawuce suka je....... *Bayan wata daya* Tun bayan da yaa shaam ya dawo gaba daya rayuwar poojah ta sauya ko a makaranta sun fahimci hakan,sabida tazamo so quiet a rayuwarta ta tsani yaa shaam kuma masifar tsoransa takeji matuqa,zuwa yanzu duk wani abu dazesa yamata fad'a tofa gudunsa takeyi kuma idan tana parlor d'n k'asa ya shigo yanzu zata gudu shi kanshi ya kula da hakan kuma harga Allah baya san rashin walwalarta a kusa dashi danya kula momy ma ta sauya masa ba kamar daba gani takeyi tamkar yana cutar mata da yarinya......yauma kamar kullum hafsat na zaune a parlor tana kallon wani catoon series na barbie yaa shaam ya shigo ko kallonta beyiba ya zauna tana ganin haka ta miqe zata gudu yace yana danna wayar hannunshi " Hafsat zo" kawai seta soma hawaye dawowa tayi ta tsuguna a gabanshi tana sharar k'wallah,kan yayi magana phone nashi ya soma ringing d'agawa yayi ya kurawa hafsat data sadda kanta ido,mamaki yakeyi me aka mata take wannan hawayen ,cikin sanyin murya yace "Haleema na ya akayi?" a d'aya bangaren seji yayi tana kukan shagwab'a "Haba mana boo me kwana biyu kana cikin garinnan amma sam bakazo ka ganni ba Allah yau idan har bakazoba ni gobe da sassafe zan wuce wana sokoto kuma Allah bazan dawoba sekaje da kanka" k'arayin kasa da murya yayi "Haba leemah dear,zanzo yau dinnan inshaa Allah kuma ma yaune alqawarin new phone nakifa nama isa naqi zuwa,u expect me anything 7:pm inshaa Allah" daga nan sukayi sallama akan se yazo kallon hafsat yakumayi yace "Lele zoki zauna kusa dani" da mamaki ta d'ago ta kalleshi amma bata taso d'inba sanda yakuma cewa "zomana ki zauna anan,magana zamuyi" yafada yana nuna kusa dashi d'in, jiki a mace tazo ta zauna kusa dashi ya kalleta yace " haba lelen dady kukan kuma na menene eye? Ba abinda zan miki,nifa yayan kine uwa daya uba daya,me zaisa kina tsoro na har haka daga yauma mun zama best friends kinji" murmushi tayi tace "To na gode" a sanyaye "Dama zancen school ne,zakice premier kuma interview din gobe ne,ss1 zakiyi interview nasu" girgiza masa kai kurun tayi sannan tace "Zanje nayi sallah se goben" ta miqe " ki shirya zamuje dake wurin yayarki yawo,ko bazakiba?" fara'arta fa fadada tace "Zanje mana gun matar dazaka aura ko yaa shaam Aunty leemah?" murmushi yamata yace "ea can 6:45pm kina sallame magrib ki sameni mota,bana karbar uzurin african time?" juyawa tayi tana murmushi tana kuma mamakin sauyawar yayan nata lokaci daya,dukkuwa dayake ta hango sosai ba wasa a lamuransa musamman akan karatu"..... Mom nuaiym. [1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi Vote me on wattpadd@68billygaladanchi. *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 03 Hafsat kyakyawar yarinya ce fara qal me tsayin gashin kai,siririyace samb'al sedai fa ba gaba ba baya duk da yake bazamu yankewa surarta hukunciba kasancewarta yarinya y'ar shekaru goma sha hud'u wanda har yanzu bata gama hada girman jikinta ba,tana da dogon hanci me tsayin gaske da manya manyan dara daran fararen idanu masu wani d'igon zaiba zaiba aciki koda wane lokaci idanun zaka gansu a lumshe tana da d'an mitsitsin baki amma lips nata suna da dan kauri sedai ba cancanba,sosai takeda gashin gira dana girar ido baki wuluk,sannan kuma suman kanta yazo har k'asan goshinta kwance luf luf gwanin ban sha'awa...... Ilai kuwa lokacin daya fad'a lokacin ta isa jikin motarsa sanye da wando jeans blue da red top ta yane kanta da mayafi red tayi kyau matuqa,batare dayace komai ba yaja suka tafi sanda suka kama hanya sannan yace "Poojah" gabantane ya yanke yayi mugun fad'uwa jinya kirata da wannan sunan ta kasa cewa komai,hannunta ya kamo ya saka a nashi yace "kinaji ina kiranki zakimun banza,ina poojah shine sunan da friends naki suke kiranki kuma karki manta we r now friends arn't we?" murmushi tayi tace "sure mana we are" murmushin ya kuma yi "Wane kalan waya kikeso kinsanfa ban kawo miki tsara baba shine zan fanshe" itafa sam bata sakin jikinta dashi harga Allah tsoron shi takeyi murmushin takumayi "ko wanne ma inaso" yagano a tsorace take ya sanya be kuma cewa komaiba,dasuka isa k'ofar gidansu leemah seyace tashiga ta gaisa dasu umman leemah inyaso su fito tare,ba musu tashiga gidan,da sallama ta isa har kofar parlor din amma ba wanda ya ansata haka ta danna kai ta shiga dama hafsa ba manners,tana zuwa taga ashe kowama yana zazzaune a tsakiyar parlor din suna zazzaune abinsu suna hira,yan mata ne sunfi su shida se babbar mace a tsakiyansu, kallonta kowa keyi amma ba wanda yace da ita kanzil a kasale tace "Sannunku Aunty haleemah nake nema?" babbar macen ce tace "ke wacece yarinya baki iya gaisuwa bane?" kallon matar take ta qara lumshe lumsassun idanunta tace a wahalce "Namayi kokarin ce muku sannu ai ina tundazu nake ta rafka uwar sallama kukamun banza" da mamajin furucinta umman ta miqe tsaye tace "wacece ke yarinya meye kike nema awurin haleema?" cikeda takaici tace " yaa shaam ne yace nazo na gayarda umman matarsa daze aura haleemah, kuma yace nace ta fito su tafi inda zasun" ana haka sega haleemah tafito,kallon Hafsat tayi tace "ke meye haka lapiya?" kallonta kurun hafsat tayi tace "yaa shaam na jiranki a waje" tana kaiwa nan ta juya abinta bata ko kalletaba,da gudu taje tariqe rigar hafsa ta baya tasanya hannu ta dungure mata kai tare da kai mata ranqwashi tace "y'ar gidan uban waye me dazaki wa mutane iskanci haka ake fadar saqo" atake idon hafsat ya cicciko tace " Yar gidan uban yaa shaam ceni kuma nice qanwarsa dayake da ita hafsat,akwai wani magana ne??" da sauri leemah ta seseta kanta tace "Allah sarki hafsat kulele,ya kike wlhy ban ganekiba,nasha fitsararrun yaran unguwane ashe babbar sis ce,umma kinga qanwar shaam" tafada tana kallon umman tare da kashe mata ido daya alamar a saisaita zancen,murmushin

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44