Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,256 words 0 views Progress saved
Download Book

yaqe umman ta somayi "Laa wai itace kinsan fani nafi ganewa ace shammaz sam datace shaam ban gane wa take nufi ba,kikace hafsat sunanta sannu kinji 'yata zonan kusa dani,kinga munata surutu wlhy bamuji sallamarkiba" ahaka dai suka rinqa zuba uban surutu wananna yace mata wannan wancan yace wannan,dazasu fita kuwa aka rinqa kwaso mata kyaututtuka,itadai shigowar farko dukda tanada kuruciya gidan be mataba wayannan yan matan masu zubin karuwai.....!!!! Amota kuwa leemah se janta takeyi da hira ita kuwa taqi ta saki jikinta gaba d'aya a tsure take hankalinta baya jikinta tunaninta daya yazatayi kar yaya ya auri wannan itafa lokaci daya taji ta tsaneta da yan gidansu gaba daya,haka sukaje siyan wayar yaa shaam ya siya mata iri daya dana leemah wanda atake ta fahimci cewar bataji dadi ba sabida kallonsa tayi tace "Boo me wannan qaramar yarinyar zaka siyawa danqareriyar waya irin wannan a gaskiya kunaso ku b'atata da yawa" a yanda kuma hafsat ta fahimta shima beji dadin yanda tayi ba domin kuwa be kula da zancenta ba,daganan ya siya musu ice cream da kaza ya mayarda leemah gida....tana shiga kuwa tacire mayafin ta fada tsakiyar parlon da sukecin kasuwa tace "Umma wlhy da matsala wannan shekiyar qanwar tasa itace matsalar tamu,baya shayin mata komai,kinga yawan kaza da ice cream d'aya ya siya mana abin haushin ma wai hatta waya iri d'aya ya siya mana yarinya sekace kishiyata,ina wannan yarinyar ina riqe babbar waya har haka wlhy rashin hankali ne tsantsa,kuma tsaf maganinta zamuyi domin idan ba haka ba ita zata takurawa rayuwarmu ta hanamu cimma burinmu" gyada umman tayi tace "Ai maganin shegiya zamuyi ku barni da ita gashi sam batada kunya ko kadan wlhy amma damu take zancen!!!! *Washe gari pooja a bisa rashin sani tashiga interview na wayanda ke neman shiga ss3 kuma abun mamaki tazo na daya acikin su kusan 32 koda suka je bincike aka tabbatar musu taci akan ta soma zuwa on monday,monday tana zuwa taga an kaita ss3 mamaki ya kamata tace dasu kuskure ne ita ss1 zataje su kuwa suka kafe akan ko exam datayi na ss3 ne kuma itace overall gaba daya,haka ta zauna ita kadai qaramar yarinya acikin manya kowa se tsokanarta yake dukta takura,tana dawowa gida kai tsaye part din yaa shaam ta nufa harda kukanta ta sanar masa "ke wace iriyar sakarai ce dazaki shige exam daba nakuba?" share kwallanta tayi tace "yaa shaam nifa na gaji dajirane inajin ankira badge 3 seniours sena shiga kawai ashe ss3 ne" shiru yayi yace taje se gobe,juyin duniya yayi dasu akan yarinyace amma sun dage akan bazasu mayarda overall student tasu abaya ba,seda aka qara bata exam din lapiya lau ta lashe komai dole haka ya hakura akan ta zauna din,data dawo gida yayi kiranta akan ya akayi ta iya abubuwan ss3 anan yakeji cewar a library na school dinsu har books na nursery take karantawa dana ss3 kuma abinda bata ganeba taje gun malaminsu ko principal idan besan amsaba ya hada ta da malamin dake subject din" gamsuwa yayi da bayanan yamata fatan alkhairi sannan ta juya ciki...... Mom Nua'iym [1/10, 9:57 PM] Billy Galadanci: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi Vote me on wattpadd@68billygaladanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 04 Sam yaa shaam baya saurarawa Elham indai zancen karatune,har me extra lesson yanema bata dawowa gida se 5,kuma anayin isha malamin islamiyyarsu zezo ita da mero sekuma 9,wannan ne ya sanya sam batada time,a haka har lokacin waec da neco yazo lapiya lau sukayi suka gama a wannan lokacin hafsat takeda shekaru sha biyar a duniya qawayenta dasuke school tare duk sun girmeta babbar qawarta me suna huda shekarunta sha takwas ma,sosai suka shaqu ba kadan ba tana d'aura hafsat akan hanyoyi masu kyau sabida tanada hankali kuma ba laifi tana ragewa dukda yake shagwab'a irinna hafsat bawai tana denawa bane kurun dai ta rage yiwa mutane rashin kunya......wannan kenan Yaa shaam shine babban yaron da Alhaj muhammad gaya dakuma haj Nasara suka haifa wanda bayan haihuwarsa sun cire rai gaba daya da cewar zasu qara haihuwa kasancewar kafin samuwarshi ma ansha fama,sosai suke qaunar shammaz ba kad'an ba wanda bayan an haifi hafsat ma soyayyarshi ko kad'an be ragu ba a zukatansu,sedai fa sun d'auki soyayyar duniya sun d'aura akan hafsat basu bama har Abba haris wanda ya kasance qanine a wurin daddy uwa d'aya uba d'aya,a wurin mahaifansu su hudu ne kacal maza biyu mata biyu haj maryam dakuma autarsu haj Harira,Abba haris yanada yara bakwai,Surayya itace babba se yan biyu hassana da husaina,se khairiyya da Auwal sannan Abduljabbar da Abdurqadir...Maryam kuwa yaranta biyu rak Bunyameen da yusuf,harira keda biyar saratu,sa'adatu,shamsiyyah, sha'awanatu se autarta safiyyah.batada namiji ko d'aya gaba dayan wannan babban family din su a qaunar junansu baka tab'ajin wani munafurci ya taso a tsakaninsu ko rashin jituwa koya yana kokarin hakuri da d'an uwansa kazalika kuma dukkaninsu 'yan boko ne masu ji da kud'i muhammad shine babban cikinsu sannan kuma gaba dayansu yafisu kud'i,mahaifiyarsu wacce sunanta hafsat taci tana nan daram ita da mijinta mlm Abubakar gaya,sune ma sukafi kowa shagwaba hafsat domin kuwa suna matukar kaunar yarinyar....... Shaam tun yana secondry school yake soyayya da leemah lokacin yana ss3 ita kuwa tana jss3,sam leemah bawai yarinya ce,sabida yanzu tayi 27 yrs ko shaam shekarunshi 8 baya kasar be dawoba seda yazama cikakken likitan zuciya kuma ma kan yaje yayi kusan 2yrs da gama makaranta bejeba,duk sanda ya dawo hutu suna manne da juna,sam wlhy 'yan gidansu leemah basuda kunya ko kad'an akansu sannan kuma dukkansu basusan girman mahaifinsba yan matane su bakwai rasss se uwarsu mara kunya da hankali sun mayarda mahaifinsu wagili basa ganin girmansa sabida bashida karfi sune da kansu suke karuwanci suna cida kansu da uwarsu,sam ba dan Allah leemah ta nacewa shaam shikadai yake haukansa amma itakam ta da biyu takeyi...... Hafsat zaune asaman stairs dake sadaka da saman gidan tana latsa wayarta,sam hankalinta baya kan wayar ta rasa dalilin daya sanya zuciyarta take azalzalarta akan yayanta shaam,sam idan bata ganshiba a wuni wani zazzafan zazzabi takeji yana rufeta,ganin har shabiyun rana ya gota be shigoba ya sanya tamiqe ta nufi part d'inshi,knocking tasomayi a hankali shikuwa ya taso ya bud'e,kallon mamaki yamata yace "poojah yadai" d'an murmushi ta msa tace "Dama nayi tunanin baka karyaba bane kuma banga ka shigo cikiba,shine nace barinzo in duba inga ko lapiya" mamaki yarinyar ta bashi sosai sabida shidai wannan yarinyar har yanzu be gama gamsuwa da nutsuwartaba gyaran murya yayi yace "Tunda aka fara zancen aurennan senakeji ko yunwar ma banaji mantawa ma nakeyi da abinci abubuwa sunmin yawa gashi im all alone" murmishin yaqe tayi haka kawai taji gabanta na faduwa jin yayi zancen aurennan,kuma ta rasa dalilin jin hakan dukkuwa dayake sam ita bata damu da wannan shegiyar matar da yayan nata ze aura ba "Aikam yaya daka dena zama da yunwa,baka ganin zaka kasa hidimomin idan ulcer ya damk'eka mezan dafa maka ne??" murmushi yayi yace "ke me kika iya lelen daddy?" shagwab'e fuska tayi tace "yaya bayan tunda ka dawo gaba daya ka sauyamun rayuwa,tare dani fa ake girki a gida,nifa yanzu koma meye zan iya girka maka tumba

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44