Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,281 words 0 views Progress saved
Download Book

yace "Hafsatu manga,sanar dani tsakani da Allah ina kike buqatar a sauya miki?inda bakyso,ma'ana abun be miki ba?" kallon shi ta d'anyi sannan tace "Ni ko ina ma yamun ko ince yamun yawa ma,wancen corridor dinne kawai za'a saka mun console,se dining shelf dababu awurin dining,shima kuma zanwa daddy magana,nagode sosai Allah ya qara girma yakuma kara budi,Allah jikan iyaye kuma ya biya bukatocinka na alkhairi" har cikin ranshi yaji dad'in adu'arta tunawa yayi da Zainab wacce sam bata taba cewa dashi ci kanka ba duk girman alkhairin daze mata kuwa,murmushi ya sakar mata yace "Kinsan ni kwangila na bayar bansan wai ya kamata su zauna awurin ba,yanzu kawai muje shops asiya choice naki,ba wani su daddy" kallonshi tayi "To ai yaa muham......shhhhhh yafada hade da daura hannunsa asaman lips nashi,tunawa tayi da gargad'insa na rashin son gaddama ya sanya tayi gum da bakin nata,koda suka fito kasa hakura tayi dama hafsa akwai surutu tace dashi "Yaa muhammad gidannan yayi kyau sosai wlhy" Bece da ita komai ba kurun murmushi ya mata...... *Bayan kwana uku* Hakan kuwa Akayi,da hafsat da khairii da Aunty surayya suka dauki hanyar dubai a ranar wata wednesday,har suka isa suka kwana suna mamakin hali irin na muhammad,be basu ko sisin siyayyar lefenba,illah kawai tunkan su isa ya sanar dasu akwai driver daze kaisu masauki daga airport,kuma suna cin abincin wurin wanda menu kawai ake kawo wa su selecting,haushi duk ya gama kama hafsat kusamman ya da Aunty surayyah ke faman masifa akan ya rainawa mutane hankali,ko cewa akayi dashi basuda aikin yi,Wayan hafsa ne tayi qara tana dubawa taga number dinshi,a dake ta daga wayar sabida ba shakka ta shaqa yau kam,yace da ita "Hafsat ki fito idan kina masauki ina reception na hotel din" da mamaki ta kalli Aunty surayya dake gefenta tana uban mita,sannan tace dashi "A dubai din?" tsaki yaja yace "Noo a india,danla malama kizo ina reception ma wurin nace dake ko mun fara wasan banza ne haka?" cikin jin zafin gwasaletan da yayi tace "Kayi hakuri ganinan zuwa" kallonta surayya ta "Keda waye kuma Ina zakije?" "Muhammad ne wai yana wajen reception ashe yazo,kuma shi da number shi yake amfani niban sani ba" kallon ta tayi "Au dama shima zezo kika barni ina surfa mar ashar?" "wlhy Aunty bansan zezo ba,ni kawai zancen dan rakiya yamun" jinjina kai Aunty tayi "Wannan shegen muhammad din anyi miskilin masifa,ko wa yakewa iya shegen oho,jeki kiji" batace komai ba ta zari dan mitsitin mayafi tafito ga rigar irin straight gown din nan ne na roba ya kameta over, tun daga nesa tana ganin fuskarsa tasan akwai magana a d'an tsorace ta karaso wurin da yake,zama tayi kusa dashi a kujerar da yake tace "Sannu da zuwa yaa muhammad ya hanya?" kallonta yayi fuskarnan a daure yace "Banasan ya hanyar ki sabida jirgi daya muka zo daku ai,sannan wlhy mintuna goma na baki ki sako sutura dan wannan bakida banbanci tsirara,idan kuma na kuma ganinki da makaman ciyar wannan shigan wlhy sena sassab'a miki,sekace ba 'yar musulmi ba" kallonshi tayi se a lokacin ta tuna yanayinta,waifa ita tayi shigar ne a zuwan tazo garin farar fata kartayi qauyanci, jiki a mace ta miqe,zuwa tayi ta cire kayan ta sako abaya baqa har qasa tayi talha ta fito,surayya na ganin yanayinta tasan shigarta yayiwa masifa amma dai vata dameta da tambaya ba,koda tazo baya nan,wayarta ta daga takirashi amma be dauka ba,anan ta zauna tafi 30 mnt be dawo ba ta qara wayar tashi gaba daya ma tajita a kashe,gwiwa a sace ta koma dakin tace da Aunty surayya wai yace gobe zasuyi magana,kallo daya surayya ta mata kuwa ta fahimci da babbar matsala....... Washe gari tun asuba ta koma parlor tayi kiransa a waya,yana kallonta harta tsinke be daga ba, kusan 3 msd col,kawai seta fara hawaye tama rasa dalilin daya sanya take damuwa dashi zuciyarta sam batayi adalciba,data saka masa wannan tsoron na muhammad,tana cikin wannan tunanin taji qarar shigowar message "Room no 10,2nd floor" shine abinda ya aiko mata sarai tabgane nufinsa ta sameshi acan,miqewa tayi ta saka hijab dinta tayi hanyar daze sadata da wurin....knockin tayi yazo ya bude fuskarsa a hade,gaidashi tayi sannan ya janye mata ta shige a daya daga cikin kujerun parlor din ta zauna,ta qura masa ido,shima din ita yake kallo,yaukam seda tagaji da kallon nashi ido cikin ido sannan tace "Kayi hakuri bazan qaraba inshaa Allah" amaimakon ya baiwa maganarta muhimmanci se cewa yayi da ita "Meya faru kike kirana daga yin sallan asuba?" tama rasa mezata ce masa,se kawai ta miqe "zan koma bacci zanyi" tazaci ze dakatar da ita amma bece mata komai ba harta fice,a ranta kuwa taji zafin sa sosai.... *Nigeria* Sun dawo lapiya dauke da lefe da ban mamaki, har masifa su daddy sukayi,amma surayya tace dasu tamasa magana yace hafsa matar sace,babu kuwa wanda ze qayyade masa yawan suturun dayake buqatar wadata su da ita,kuma ya jibgo dogwayen riguna da qananun kaya over.......Aikam rana daya akayi daurin auren muhammad da hafsat,se kuma Shammaz da maryam,kuma aranar aka kai amaren biyu,wanda sam koda ma akayi auren hajia halima batada labari tana wurin gantalen ta dubai,acewarta taje saro kaya shikuwa da gayya ya ganta,yan uwanta kuwa dasuka ga pictures na ebar hankali da ba indiya se hankalinsu ya mugun tashi,amma sam basu sanar mata wai shaam yayi sabuwar amarya ba....... Hafsat kuwa tunda yan kai Amarya suka watse wuraren karfe goma na dare seta soma jin tsoron zaman gidan ita kadai, shi kuwa be leqo bama se sha daya da rabi, Abinci ya kawo mata sannan ya sanya hannu ya yane mayafin dake jikinta ya ajiye gefe ya kalleta, "Kina bazawara wani kunya zakiji,zaki wani lullub'e fuska" sosai maganar sa ya doki qirjinta amma bata nuna masa komai ba kurun dai murmushi tayi masa,ganin haka ya sanya yace "Kici abinci kazane da drinks ga youghurt da ice cream idan zaki sha" kallon su tayi tace "Gaskia Alhamdulillah na koshi,sedai zuwa safiya" miqewa yayi be wani damuba,kizo ki kulle kofofin gidan ni zan tafi seda safe" ko motsawa batayi ba daga inda take sabida mamakin daya bata,to gidan uban wa ze kwana?" ta tambayi kanta,ganin fa tsorone ze hallakata ya sanya harya kai parlor ta rugo ta riqe masa hannu,da mamaki ya kalleta tace dashi "Yaa muhammad zan bika dan Allah" juyowa yayi yabfuskance ta gaba daya "Ina zaki bini hafsat?" "Inda zakaje mana" "Ba inda zani fa, gidan zainab zanje na kwana,kishiyarki" tafi minti uku tana kallanshi, juyawa yayi ze fita ta riqe masa hannu again "Bazan iya kwana anan ni kadai ba,tsoro nakeji" murmushi yayi "Ni ban aureki danna tayaki kwana ba hajiya,ko mun rubuta haka acikin agreement namu?" gaba ki daya tsoro ne ya taso mata ta kalleshi sosai tace cikin dakiya idanta yayi ja sosai amma batasan tayi kuka "Na tuna kuwa babu wannan acikin rubutaccen auren mu,na manta bayan signing takardar yarjejeniya da mukayi ta aure,wurin daurin auren ma mun rubuta cewar kalar auren namu na dabanne ba wanda musulunci ya tsara ba,Kaje amma karka qara kawomun komai daya shafi rayuwar aure,idan bazamu kwana a tare ba babu wani abu dazakamun na aure,na yarda haka tsarin namu auren yake,kaje plss" tafad'a tana me d'addage hannayenta duka biyu alamar

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44