Skip to content

Chapter 25

Chapter 25

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
Download Book

a nice person" shiru ta masa kawai amma bawai danta yarda ba,tanaso ta tsani muhammad dinnan amma zuciyarta taqi aminta da tsanar tasan...... Wuraren sha dayan dare unle say ya dawo wurin hafsat,zama yayi kusa da ita yamata a dua lokacin tamayi bacci sannan ya kashe fitilar dakin ya fito ganin ko momy bacci ya kwashe ta batare data kashe fitilar ba,yana barin dakin ya kula da mutumin daya wuce part din fuskarsa a rufe da mask se suaune kansa yakeyi,harya wuce kuma seyakasa nutsuwa ya dawo baya gaba daya,binsa yayi yaga lallai dakin ya dosa,ya murda sad'af sad'af ya shige aikam say da sauri ya biyo bayansa shima yafada dakin,ganin yayi mutumin ya dauki filo ya danne fuskar hafsa se shura kafa takeyi acikin duhun dakin,kuka kura yayi yayi kanshi aikam fada ya kaure har suka tashi momy,da sauri ta haska torch light dinta tana ganin haka ta kunna fitilar dakin kokawa suke sosai da sauri ta kwallah kara,amma kan wani ya farga kasancewar darene har mutuminnan ya daga wuqa ya cakawa uncle say a qahon zuci har wurare biyu......ko kafin mutane su zo wancan mutumin ya gudu,hafsat ma ta farka tuni sakkowa tayi tama manta zancen karaya,sayyeed kuwa tuni rayuwa tayi halinta,se kuka takeyi tamkar ranta ze fita a haka doctors dake nan sukaxo,kowa se hawaye yakeyi ana fadar mutuwarsa .... Mom nuaiym [2/9, 8:55 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 23 Ba shakka hafsat ta gama haukacewa da mutuwar uncle say,tsakani da Allah tanki tana gani aka fita da gawarsa wanda ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar wlhy ya mutu,ko dan ganin jinin daya zuba ajikinsa, kasa zama tayi asibiti dole aka wuce da ita gidansu.......tunda hafsa taje gida take kuka ba qaqqautawa shi kanshi shaam din ya girgiza da mutuwar sayyeed,musamman da yake ko a dakin da hafsat take aka kashe shi,kuma ita bata gane wanda ya danne mata fuska ba da filo,kasancewar acikin dubu ne farkawar momy ne ta ga sayyeed..... Da yamma yan sanda sukazo gunsu da tambayoyi kallon ta sukayi bayan ta momy ta gama fadar iya abunda ta sani suka ce da hafsat "Hafsat dukda yake munsha mamakin ance kinada matsalar ido,amma se gashi faruwar abinnan idon naki ya bude,muna san sanin shin sanda abun ya faru kina ganine? Ko kuma aa bayan faruwar abun kika soma gani" kallon dan sandan tayi gaba daya gani tayi ya gama raina mata idan dai har karatun datayi na lauya harta zama qwararriya ba shirme bane a yanda ta fahimci kalamansa zarkin nasa akanta ya fara shi "Tun ranar danayi a hatsari na farfado komai ina ganinsa lapiya lau" gyaran zamansa yayi ya kalleta sannan yace "To meyasanya likitoci sukace bakya gani,kema kuma kike ta faman pretending?" kallonshi tayi shima sanda ya razana da kallon sannan tace.."Banasan auren yaa shaam,shikuwa so yake na aureshi sabida wata manufa tashi da ban santa ba,nakuma san ba dan Allah bane da wannan yaje ya sanya kakanmu tace dole sena aureshi,ranar dana samu accident ranar naji doctor yana wa su daddy bayanin cewar idan har na farfado idona ya sake tabuwa baze gyaruba,kasancewar shine na biyu,daganan dabara tazomun ta nunawa duniya cewar bana gani sabida nasan yaa shammaz baze aureniba ina naqasashiya,uncle say da abokinsa Dr.shuraim sunsan ina gani tangaram dama shirine se bayan na auri zabina sannan kowa yasan ina gani clear" nisawa kowa dake wurin yayi ganin tana fad'ar gaskiar ta kai tsaye,police din ya sake cewa "Menene zaki iya tuna ya faru a daren jiya?" hawayen daya gangaro mata ta saka hannunta ta share sannan tace " Kawai dai nasan munyi sallama da uncle say tun karfe tara na dare akan se washe gari,daganan yana fita na kwanta nayi bacci,acikin baccin ne naji an sakamun pillow a danne mun fuska sosai bana iya numfashi,can kuma sena ji an sakeni na sanya hannuna da ke lapiya na janye pillow din amma sabida yanayin dakin ba wadatar haske banga komai ba seda momy ta farka ta haska torchlight jin hayaniya,ananne naga uncle say da wannan mutumin me mask a fuska suna kokawa,harya caka masa wukar,kuma kan momy tayi wani yunkuri mutumin ya fita da gudu,amma fa ni naga face d'insa asanda uncle yaji azabar ya caka masa wuqa ya da damko face mask din wacce ina saran tana hannunku" nisawa police din yayi yace "mungode da amsoshinki kai tsaye,dakuma hadin kai,muna fatar idan muka dawo zamu samu hadin kanki idan buqatar hakan ya taso" a fusace ta miqe tace "Sabida yana da kudi? Ko sabida yana taqama da isa dacewar shidin wanine ze kashe mun muji ya zauna lapiya,ku sani akwai sadakin sayyees akaina wanda yake nuni ya kuma isa hujjar kasancewata matarsa sabida haka wlhy sena ga karshen shari'ar nan,matsayi na na cikakkiyar lauya nice zanyi bincike me ma'ana idan har ku bazakuyi ba" cikeda rashin fahimta suka kalli juna sannan dayan yace "Ban gmfahim ceki ba?" atake ta zayyane musu abubuwan dasuka faru tsakanin muhammad da sayyeed da kuma furucin muhammad ta qara da cewar "A shari'ance muhammad ya aikata babban kuskura furta wannan kalamin kawai balanta na yakai ga aikatawa,nice zan sameshi da nawa tuhumar nice zan bincikeshi dan kaina ina ikon tsayawa kaina nima din cikakkiyar lauya ce meji da kanta" kallonta mutumin yakumayi yacewa "haj amma ina ganin kamar Barrister muhammad kike magana ko?,a iya sanina dai shine mutumin da akace ya kade ki,kuma babban lauya ne da ake fafatawa dashi a fadin kasar nan gaba daya" tsaki taja ta sanya hannunta me lapiya ta bubbuga kirjinta "Sabida yana taqamar shi babban lauyane seya kashe mutum? To nima babbat lauyace ta kaina,kuma wlhy senabi jinin mijina" shiru sukayi ganin yarinyar nacikin zafin mutuwar.... *Bayan kwana uku* Shirin ta tayi tsaf kasancewar mahaifinta yamata komai na lauya me zaman kanta bata gwamnati ba,domin kare haqqin sayyeed daya mutu akanta,kai tsaye gidan Barrister muhammad jalalludeen Auwal yana zaune a harabar gidansa yana kurbar lemo a hankali cikeda yanga,dama kuma yasan da zuwanta kuma police ma sunzo sunyi nasu har sun wuce,har a news paper an sanya tuhimarsa da yake wanda wannan ko kadan be daga masa hankali ba sam sabida yasan meya taka hmmmm.....A yangace ta fito daga cikin motar zuwa inda yake zaune shi kuwa tun daga nesa yake kallonta yana wani murmushin kin rainawa kanki hankali,Tana zuwa ya miqe tsaye sinfi mintuna biyu suna kallon juna,hannu ya miqa mata,sanda tabi hannun nashi da kallo sannan a wulaknace ta miqa masa nata yace cikin muryarsa me tarwatsa littafinta "Bar.muhammad j Auwal AkA j.A" murmushi tasaki me ban haushi ta furta a yangace "Bar. Hafsat muhammad gaya AKA Miss poojah" murmushi ya sake meban dariya "Nice meeting u young barrister" "Nice meeting u too the oldest one" murmushin ya sakeyi tace "ina fatan kasamu labarin suing naka damuka yi a court,ina kuma fatan ka nemi qwararren lauya macecinka" juice ya dauko ya kurba sannan ya zauna ya kalleta ya nuna mata da hannu kujera "Have a sit miss poojah" zama tayi ta dauki cup na juice da hannunta me lapiya ta kurba sannan ta kai dubanta zuwa gareshi tace "Bakace

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44