Chapter 29
Chapter 29
qarar shigowar message taji a wayarta kamar haka "This should the very first and last time dazaki ajiye mun waya,koda mun gama magana kuwa lallai nine zan zama na farko da zan ajiye" jikintane ya qara macewa jin kalamansa ta daga waya takuma kiransa yana d'agaba tace dashi "Yaa muhammad kayi hakuri" cikin sanyin murya yace "wuyarta ka bani hakuri kai tsaye za'a wuce wurin,dama gobe zanzo zancen kayan lefenki ki shirya zuwa dubai" "To Allah ya kara girma na gode sosai" "Se anjima" shine abunda ya fada a zatonta ya ajiye wayar ashe be kashe ba,ajiye tata wayar tayi ta sanya hannunta a kirjinta ta shiga rero kuka tana sambatu ta shiga uku,ita dai batayi sa'an zuwanta duniya yazatyi da masifan yaa muhammad,tunda tasan hankalinta take kwasar bakin cikin d'a miji,da karfi ta furta "Allah na tuba ka yafeni,Allah idan na aikata wani laifin ake jarabtana da wannan masifun Allah na tuba ka yafeni,kuma ka bani ikon cinye jarawar nan daka dauramun" kuka take sosai,muhammad dake saurarenta ma dafe kanshi yayi,ba abunda ke hanashi zuwa gun hafsa illah wannan kukan nata,ya tsani kukan ta masifaffen tausayinta yakeji,shidai bazece yana santa ba kuma bawai wata manufa ta cutar da ita yake da itaba kurun dai tausayinta yakeji yana gani kamar lallai idan ta auri wani zatasha wuya ne,tunda kuwa ya binciki tarihin rayuwar ta kaf,ya sani sarai dabe biyo mata ta wannan hanyar ba,shaam zata komawa kuma matar sa ma masiface a wurinta,kwanciya yayi ya runtse idansa yana mejin zafin zubar hawayenta..... Menen ra'ayoyinku game da auren hafsat da muhammad? Ina tsumayin jin comments naku. Vote plss Mom Nu'aiym ca [2/12, 8:21 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 26 Washe gari da yamma hafsat tana kwance mero ta shigo tace da ita "Kulele kije guest parlor muhammad yana jiranki yace wai baya samun wayanki" k'irjinta ne ya dan doka ta dago ta kalli meron "Ke kika ganshi da kanki?" kallon ta mero tayi,batun yauba ta fahimci ko zancen muhammad akayi hafsat tsorata takeyi tausayin tane ya kamata tace tana dafa kafad'arta "Inshaa Allah babu abinda ze sameki,kuma inaji ajikina tarayyarki da wannan muhammad d'in alkhairi ne mutum ne me nagarta sosai na kula da hakan tun a yanayin gaisawar da yakeyi da mutane,dan Allah ki saisaita nutsuwarki gu d'aya" batace komai ba ta sanya hijab dinta ta sauka zuwa qasan......Da sallama ta shiga parlor d'in kanta a kasa,ansawa yayi batare daya kalli inda take ba,karasowa tayi ta zauna kusa a kujerar dake fuskantar tasa tace "Ina wuni yaa muhammad?" Amaimakon ya amsa ta seya wurgo mata tambaya "Mesa kika kashe wayanki,bayan na sanr dake tun jiya yau zanzo?" kanta a kasa yayinda qirjinta keci gaba da uban dokawa tace "Banida caji ne" "Bakuda wutane?" ya wurgo mata wannan tambayar cikin tane ya juya ta dago da sauri suka had'a ido saurin janye nata idan tayi sannan tace "Da Akwai wuta caja nane ya lala ce" D'an kishin gida yayi sannan yace "Mesa baki saka layinki a wayan dana baki ba,kumama mesa bakya amfani da ita tunda na kawo miki ita da layine a ciki" "Kayi hakuri" shine abunda ta furta,ya tsani wannan ban haqurin na hafsat wlhy ita komai se ban hakuri qara tubire fuskar sa yayi yace "Zancen zuwa dubai ne had'o kayan lefe,idan ina irqawa daidai yau saura 27 day's daurin aure,so inasan sanin keda wa kuke da intl pasport wacce ayau zaku iya tashi zuwa dubai ko gobe a misali?" kanta a qasa tace "Nida khairiyya ne,amma inaga anan ma za'a iya siya ai base anje dubai ba" kallonta yayi na yan daqiqu sannan yace "Ba zuwa nayi ki bani shawara ba umarnin tafiyar nake baki hafsat,abu d'ayane zaki riqe mu zauna lafiya shine rashin yimun gaddama,nine da kaina zan sanarwa da Abba haris zancen tafiyar nanda kwana biyu zakuyi tafiyar,yanzu zamuje gidan Abba haris mu karbi pasport din nata,kema ki bani naki daga can zan masa bayanin tafiyar,akwai kayan dana saka aka kawo daga saudi wasu daga dubai,suma zamuje ki duba ,kayan gidane abinda be miki ba ki fada a sauya wani" kallonshi tayi taso tace dashi ai su daddy zasu siya mata kayan daki,amma tunawa da tayi yace bayasan gaddama ya sanya taja bakinta ta guntse.... Abba haris bayan ya gama jin bayanin muhammad tare dajin cewar wannan tsarin sane kana yanaso ma aqara sati biyu akan ranar daurin auren kasancewar bayaso a samo matsala tunda tafiya na Allah ne,be masa gaddama ba sedai yace sedai suyi tafiyar tare da babbar Aunty d'insu Aunty surayya,sabida zamanto warsu mata qananun yara,zuwan na surayya kuwa shine ze dauki nauyin sa,idan har mijinta ya Aminta,kara kallon abban yayi yace "Abba zancen kaya gida kuma,dan Allah karkuga kamar na raina iyawar ku kawai dai tsarinane nine nake siyan kayan gidana da komai,matana ta farko ma nina mata, sabida haka hafsat ma na riga na siya komai,kayan kitchen ne kawai bana siya,amma komai nine nakeyi" nisawa Abba yayi "Bazamu hanaka yiwa matarka alkhairi ba,sedai muma haqqin mune muyiwa hafsat, gyaran daki sabida haka zamu bata kud'inta tsaba,shawarar yanda zatayi dasu kuwa ze shiga tsakanin kai da ita ne,sabida kaine mijinta" Godiya yayi sosai sannan yamasa sallama,waya yawa hafsat tafito suka kama hanyar zuwa ganin kaya,kallonta yayi sosai ya furta "Hafsat karki qara yimun karya daga yau,a ina kika samu cajin yanzu? Kuma naga wayar kusan full ma? Bakida labarin karya ba kyau,kuma batada kad'an?" sosai taji kunya wannan ya sanya ta sauke kanta qasa tace "Insha Allah bazan kara ba kayi hakuri" murmushi yayi "Mesa kika kashe wayar ki?" murya a kasa tace "Nima dai yau sena tashi banso a kirani,shiyasa kawai amma ba komai" be kara cewa komai ba ita mad'in shiru tayi sanda suka isa wani qayataccen gida me kyawun gaske,tun a gaban gidan zakaga had'uwarsa da qayatuwarsa ba karya...Gate din automatic ne wannan ya sanya ya bud'e kanshi yana ganin dosowar motar, a wani farfajiyar ajiye motoci ya ajiye motarsa wanda had'uwars ba'a ma maganarta, kallon ta yayi yace "Bismillah muje ciki" Batayi musu ba kawai ta bishi suka wuce,ta bayanshi take se kallon cikar halittarsa takeyi yanayin halinsa yanayin maganarsa da uban ikon sa,wata kofa taga ya sakawa wani card lokaci d'aya ta wangale,kai tsaye ciki suka shiga tun a parlor ta raina dukiyar datake taqamar wai suna da ita,gabaki dayan parlor din komai na ciki gold ne se daukar ido yakeyi,dakuna guda biyar ne acikin gidan kuma flate ne me masifar kyau se paluka guda uku da fankacecen ktchn wanda ya gama hadewa da tsadaddiyar carbinet,gas cooker ne kawai aciki se freezer ta kwance da double door,a bed rooms din kuwa duka english bed's ne aciki,dayan dakin red and white,dayan blue wanda shi kuma akwai parlor aciki da lubby me kyau ga coffee chairs a walk way na zuwa barin,kuma komai light blue ne da white,dayan dakin purple dayan kuma pink $ white se thee green wanda aciki duk shine yafi burgeta,ko wane daki da toilet nashi,wanda a iya Bathrooms din idan aka barka zaka kwana kana kallon abubuwan ban mamaki,gidan ya hadu over bayan sun dawo parlor ne ya kalleta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44