Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
Download Book

"yanzu dai naji,amma ki daure ki koma school Allah zan siya miki sabon waya da sabon laptop da sabon ipad kuma zan siya miki sabon kaya ma,na zuwa school madam gayu" tana murmushi tace "Thank you for that,buh bana buqatar komai daka lissafa i just need u beside me,idan wannan baze samu ba,zan haqura nace haka Allah ya tsara" sakin hannun mata yayi yace yana miqewa "Thats very good of u gold,zancen waya kuma i already bought one for you, samsung s8 your favorite product,yana mota muje nabaki " miqewa tayi tana ihu tamkar ta rungumeshi,say akwai principles seyaga dama suke riqe babbar waya fa!! A hanyar fita suka had'u da yaa shaam,uncle say ya miqa masa hannu su gaisa,dakyar ya bashi hannu sannan yace " ke hafsat wai an sanar miki kowane mutum kika dakko secikin gida ake kaishi haka akeyi?? Ga guest parlor can kuje amma se ciki,ba wani privacy kuma bare ma" kallon mamaki say ya masa ita kuwa taja hannun say batare data koda kalle shiba domin kuwa ita alqawari tayi idan yayi sallama zata amsa,ita kuma tashigo koda shi kadaine a wuri zata masa sallama amma bazata taba yi masa magana ba,koda ze mata bazata kulashi ba, gabansu yasha sekace wani dolo yace "ke badake nake magana ba?" say ne yace "kayi hakuri Dr. Shammaz inshaa Allah bazan qara zuwa muku gidan bama gaba daya bare kayi fadan bare ya shiga ciki" kawai se hafsa ta saka masa kuka " look uncle say,lemme just go n pack my things im going back to my Abba's house,im tired of this mesa daga zuwa hutu,Allah bazan kuma dawowa Niger ba sena gama school" hannu ya sanya ya dauko mata mayafin daya fadi ya rufe mata kanta sannan yace " Ina sauri ne gold,muje na baki wayanki" wani kishine ya tasowa shaam yace kai din dan iskan inane dazaka taba ta?? Dama iskancin dakuke kenan ko?" sosai rayuwar say ta baci ya wuce su zuwa mota,ya shige ita kuwa hafsat bakin ciki ya hanata koda motsi daga inda take se kallon say takeyi kunyarsa dukta rufe ta,hannun ta shaam yaja ya mannata da kofar parlor din yace " Ke wlhy ko zaki mutu sekin koma gidana wlhy ki sani wannan kayan dakika tara sena mora,bazan bari banza ta wuce niba" kallonshi kawai takeyi harya gama ya saketa batace dashi ci kanka ba,rayuwarata intayi dubu tota baci,haka ta zauna ta dinga kuka tana kiran uncle say yamma yaqi dagawa gaba daya ta damu da fushin sa,tsinuwa kuwa shaam yashata cikin kwando dubu.... Koyaya zata kaya a wannan bada qalar,gamu gani dai..... Mom Nu'aiym ce🔨 [1/30, 8:18 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 17 Yaa shaam juyawa yayi zuwa gidansa,ransa a b'ace yarasa dalilin sha'awar hafsat da Allah ya jarabeshi da ita,gashi sam shi har yanzu beji yana santaba,amma dai tunanin ta kullum dashi yake kwana yake kuma tashi.......hafsat har washe gari idan takira wayar uncle say baya d'agawa duk hankalinta ya tashi, se messages take sending mai na ban hakuri sekace ita ta masa laifi,ganin dukta damu mero ta kalleta tace " kulele lapiya dai?? Naga tun jiya kamar kina cikin damuwa?" lumshe idonta tayi sannan tace a wahalce "Uncle say ne yake fushi dani mero,sam yaqi ya saurareni" kallon nutsuwa ta mata take hankalin mero ya tashi,kaddai ace hafsat san wannan sayyeed d'in takeyi? Inko hakane wannan yarinyar taga rayuwa ita gaba daya kullum san maso wani takeyi,kuma a yanda ta kula koda tana san say din batamasan tana yiba,ta yiyu wannan karon da sabon salon daya zo mata "Menene ya faru yake fushi dake har haka?" dafe kanta tayi sannan ta zayyane mata komai da ya faru ta qara da cewar "Amma mero kinga ya dace ace wai ya d'auki zafi dani har haka? Bafa nice namar laifi ba,taya ma za'ayi laifin wani can ya shafan?" nisawa tayi sannan tace "Tooh hafsat kinsan wani be iya fushi ba ta yiyu bawai fushin yake dakeba ranshi ne kurin a b'ace idan ya huce ze kiraki" kan wani yayi magana wayan ta ya soma qara,jikinta har rawa yakeyi ganin uncle say ne,da sauri ta d'aga ta kara a kunne,kasa magana tayi kurin ta sanya masa kuka me tsuma zuciya a hankali yace "Rose menene kuma na kukan,ke komai bakida wani uzuri,kizo ina parlorn qasa a gidan daddy" zabura tayi ta suri mayafinta ta sauke da sauri,taje kusa dashi ta zauna tace tana sharar kwallah " Uncle say im so sorry" kallonta yayi yace "meye na bani hakuri kuma me kika mun,naga cols dinki ne,inata fama attending patients jiya goda naje gida it was late i coul'nt col u back,yau kuma tun asuba aka mun waya muna emergency thereter,i had to go there wlhy kina raina,shiyasa da sauri ina gamawa da office nazo na ganki kiyi hakuri" share k'wallan daya gangaro mata ta saka hannu ta share sannan ta kalleshi tace "Ni na damu na zata fushi kakeyi dani,rabon danaci abinci tun jiya ma" zaro ido yayi yana kallonta "Wlhy ina ganin mutane masu wawta na dad'e sosai banga irinkiba hafsat,tayaya bakimun laifin komai ba zan soma fushi dake,maza tashi muje na siya miki abun dadi a season 7" murmushi ta masa tace "Karka damu zanyi samosa a gida" B'ata fuska yayi "Lallai ki tashi mu tafi,banasan shashanci" ahaka taje ta sako hijab tazo suka fita,suna fita yaa shaam na danno kan motarsa acikin gidan,qwafa yayi yace aranshi lallai dani kuke zancen sena qulla maka sharrin dabakasan akwai irinsa a duniya ba !!!!!..... *Bayan wata d'aya* Tun bayan da su poojah suka koma school yaa shaan yake cikin damuwa,da kanshi ya fahimci cewar lallai ko bayan sha'awa san poojah ya masa mummunan kamu ba kad'an ba, gaba d'aya mantawa ma yakeyi da wata haleemah a rayuwar sa kuma sam yadena bata kud'i hasalima baya kwanciya wuri d'aya da ita sun raba jaha ita kuwa dama ba sanshi takeba wannan ya sanya bata damu ba neman mazan datake kawai tasaka agaba tana samun kudad'e dama abu d'aya ya tsayar da ita shine asibitinsa daya saura ta k'wace masa,ganin kuma baya zuwa wurinta azatonta aikin da boka yace ze koma yine na ganin sun kwace asibitin daya kuma cewa lallai ne seya hanashi jin sha'awarta,wannan ya sanya hankalinta yake a kwance,yau shiri na musamman yayiwa zuwa gidan daddy akan maganar auren sa da hafsat wanda yake wannan kadaice mafita agareshi,koda yaje ga mamakinsa daddy haquri ya bashi akan lallai se idan hafsat dince da kanta ta amincewa komawa gidan sa amma muddin ba ita kesan koma masa ba toko lallai ya zame masa dole ya haqura,da wannan b'acin ran ya koma gidan sa. *INDIA* Tun bayan rasuwar matar Dr. Say yake cikin tsananin damuwa,shidai sosai ba kadan ba yake santa over,yaji zafin mutuwar ta fiyeda tunanin me hankali,zaune yake a babban parlor ya rufe fuskarsa da littafin dayake nazari,tunani ne fal a ranshi na suhaila wanda sam bemasan cewar hawaye sun fara gangaro masa ba,poojah kuwa tajima tsaye akanshi tana nazarinsa wanda shigowarta gidan kenan daga makaranta,a hankalibta sanya hannu ta janye littafin dake saman fuskar tasa ganin

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44