Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Bakin Rijiya Book One Complete Hausa Novel 1,253 words 0 views Progress saved
Download Book

san son nashi ya kasheta kenan,aranta ta kudirta gayawa momy gaskiya sedai ya kashe ta...... Bayan isha mero taje ta samu momy a d'aki bayan ta gaidata ta zauna ta fuskanceta sannan tace "Momy wata muhimmiyar magana nakeso muyi dangane da hafsat domin kuwa akwai matsala akasa" kallonta momy tayi batare da bawa maganar muhimmanciba tace "Ina jinki" "Momy na sani bani kadaiba dukkan nin mutanen gidannan sun kula cewar Kulele bata cikin nutsuwarta da walwala sam,sa'annan ko abinci bataci gashi batama koda kallon data sabayi" gyada kai kurun mony tayi taci gaba "To wannan kukan dakikaga tanayi a d'azu ba komai bane illah kishin zancen auren yaa shaam datakeyi domin kuwa da bakinta naji tana sanar masa,take ta kwashe komai ta sanar mata har sanda taji tana baiwa qawarta labari da abinda qawar tace mata har tambayar data mata akan zancen yayanta ne kuwa uwa daya uba daya?" shiru momy tayi tana nazarin kalaman mero tabbas idan basanshi takeyiba ba abunda ze sanya taji hakan,inko hakane to wlhy da sake domin kuwa so sone amma sankai yafi komai,da wannan tamiqe zuwa b'angaren daddy......ita kuwa Hafsat a daidai wannan lokacin ta shirya zuwa roqar daddy akan ya barta taje gidan abba haris batasan yan biki su cika gidan ana hayaniya,zama momy tayi ta zayyanewa daddy komai shi kuwa cikin fada yace "Haba Nasara!!! Ina nidake muka zauna muka roqi dangi akan su rufe zancen cewa shaamaz da Hafsat ba uwarsu daya ubansu daya ba har abada,tayaya ma yarinya zata so yayanta inama hafsat ina sanin meye so?? Meta tauna vare ta had'a arayuwa?? " cikin fusata momyn tace "Haba Alhj mesanya agaban duniya ka nuna kanasan gmhafsat amma a bad'ini ba haka bane,karfa ma manta tsakaninta da shaam waka haifa da cikinka?? Itace 'ya daya tilo da Allah ya baka,tayaya akan abunda bekai ya kawo ba seka dau zafi haka,tunda har tana sanshi mezai hana a hadasu susu biyu a aura masa kowa ya huta" hara daddy ya wurga mata yace "wlhy kinji na rantse kobada shaam ba bazan wa hafsat aure yanzu ba,tsabar mata bakuda hankali,ke kinga karma ki nuna mata kinsan tana sanshi ki barta tayita haukanta,amma ba zancen auren a tsakaninsu yana da wacce yakeso ita kuwa taji dashi karna kuma jin wannan maganar wlhy" hafsat dake a waje kuma taji komai dafe qirjinta tayi tace "Ba daddynmu daya dakai ba yaa shaam to waye babanka?? Menene ma dangar takarmj dakai?? SO SO kuma tayaya meye mashi? Wannan shine abunda nakejin friend kullum tana mun magana akanshi game da saurayinta da gaske san yaa shaam nakeyi? Anya ban dakkowa kaina wahala ba kuwa? Lallai kuwa da babban aiki jaaa ma agabana. Mom Nua'iym [1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi Wattpad@galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 06 Jiki ba k'wari ta juya zuwa d'akinta,sam hankalin hafsat beyi yawan dazatayi zurfin tunaniba ta kasa tariyo komai,wayarta ta ciro daga k'asan filo ta kira huda,d'agawar farko tace "Huda dan Allah kina ina yanzu??" da mamaki hudan tace "Ina kan hanyar zuwa gun Ashraf tela" to yayi nima ganinan zuwa da maganar danike so muyi" kan huda tayi magana ta katse wayan,da sauri ta zari hijab tayi k'asa a hanya tayi karo da yaa shaam ko kallonshi batayiba sabida hankalinta sam baya jikinta,driver din momy ta gani tayi kiranshi da hannu,ta fada mota sukayi gaba....a shagon janyo hannun huda tayi suka dawo mota ta kalleta bayan tayiwa driver din umarni daya fita waje tace "Huda wai da gaske sosai ni Hafsat ina san yaa shammaz??" kallon ta huda tayi cikeda nutsuwa tace "Ban fahimce kiba?" kwashe komai tayi dataji su momy na fada ta gayawa huda ta qara da cewan "ke kadaine zaki iya fadamun gaskia dan Allah waida gaske wannan abun danaketaji gameda yaa shaam shine so? Kuma shi din suwaye iyayenshi??" sosai huda ta gano hafsat kuruciya ya mata yawa, banda haka ina zatasan su waye iyayen shaam,ni sawa tayi tace "poojah ki nutsu mana,zancen gaskiya ko shakka banayi kina san yayanki kuma sosai bawai kadanba,amma abunda nakeso dake shine kibi komai a hankali sabida kinga already an kusa aurenshi kuma tunda su momy basusan kinji maganar suba karki fadawa kowa karkuma ki nuna musu,wannan abun dakikeji idan yana waya da wacce ze aura da kuma idan ana zancen aurenshi shi ake kira kishi,kuma kishin ya miki yawa ina tausaya miki sabida tunkan kisan meye so da kishi kika fara kinsan kuwa illan kishi a tattare dake? Kishi masifane kamar yanda yake halittane na Allah ajikin d'an adam sedai da yake na wani yafi na wani zafin,dan Allah hafsat ki daure ki yakice sanshi a ranki,a yanda na fahimta da kika masa bayanin abinda kikeji game dashi sarai ya gano sanshi kike sabida baya muradin ki yasanya yace karki sanar wa kowa,ki manta dashi kici gaba da kallonshi a matsayin yayanki uwa d'aya uba d'aya" hawayen daketa faman tarewane suka gangaro mata tace "Huda lallai so masifa ne kuma kishi fitinane,indai haka so yake to a gaskiya da matsala,ni bansan sanda na fara sanshiba tayaya zakice in cire sanshi a raina? Nida bansan yanda ya shiga ba ya zansan yanda zan cire?? Wlhy bazan iyaba" tausayinta huda taji ta janyota ta rungume tana bubbuga bayanta a hankali,a haka suka rabu jiki ba k'wari..... *Bayan sati biyu* Sosai aka cashe wurin bikin yaa shaam kuma acikin part d'inshi dake gidan anan aka kawo amarya Haleematu,yau sati daya kenan da tariyarta,kullum hafsat ke zuwa tayata aiki,kasancewar ba abinda takeyi agidan,ta d'auki shawarar qawarta ta dena nuna komai a idon mutane harma momy ta soma qaryata zancen cewar hafsat tana san yayan nata....yauma kamar kullum tana kitchen din Aunty haleema tana tayata aiki,suna d'an tab'a hira yaa shaam ya shigo,ba kunya suka rungume juna har tana manna masa sumba a wuya " Baby yadai? Bana hanaki yawan aikinnan ba? Kije ki huta mana tunda ga Hafsat ta iya komai" kallon shi tai cikeda kissa tace "Haba honey yaya daga zuwan yarinya tayani aiki seka wani ce na barta tayi,nooo ni banasan small oga ta tasha wahala" hancinta ya danja ta saka qara yace "Kinga Baby da gaske ki rage yawan aikinnan ita wannan sakaryar yarinyar shagwab'abb'iyan yarinyane yanzu take koyan aiki ki barta ta koya kekuwa semu huta abunmu" wani langwabe kai tayi tace "Haba shaam meye hakannan wai,nika tafi idan muka gama zanzo" hannu biyu ya saka dukda zaman ta katuwa ya dauketa yabar kitchen din da ita,ita kuwa dama gulmane haka takeso ya sanya bata wani musa masa ba, hannu hafsat ta sanya ta share k'wallan daya kwaranyo mata "Yaa Allah ka yayemun wannan masifar,Allah ka rabani da k'aunar yaa shaam,Allah ka ciremun kishinsa,Allah ka kawomun agaji" wannan itace adu'ar datakeyi a sarari cikin kuka,tafi mintuna biyar a haka,kanta barwa Allah taci gaba da aikinta.....haka rayuwa taci gaba wa hafsat kullum itace da bauta agidan yaa shaam sekace wata yar aiki,shi kuwa kullum kwanan duniya qara tsanarta yakeyi yakuma rasa dalilin tsanar dayake wa kanwar tashi wanda a sanda tana qarama bashida wacce takeso sama da ita,amma yanzu tun sanda yagano sanshi takeyi seya dauki hakan a matsayin raini ya d'auki

Table of Contents

Chapters

44 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44