Chapter 22
Chapter 22
kuwa ya zama tsoho tunda qanwarsa ta girma" Murmushi yayi ya shafi gefen fuskarsa "Ki shiga ciki yan matan Yaa shaam" wata dariya tayi me cikeda ka raina kanka ta wuce ciki kawai.... Tunda yaa shaam yaga hafsat na sakar masa fuska se kawai ya qudurta aranshi shine ze angwance da ita,da wannan har tunaninsa ya kaishi ga zuwa ya ziyarci Innah wato kakarsu ta wurin iyayensu maza.... Zama yayi ya saka mata uban kuka,akan wai ai asiri aka masa ada,yanzu kowa yasan yana san matarsa Amma abba haris dasu daddy sun hanashi sun baiwa wani har an saka rana nanda watanni hud'u,Innah kuwa tacika fam ta fusata,i da take shiga batanan take fita ba akan za'a hanawa magaji mata,aikam tana da rai basu isaba,da wannan tayi kiran kowa da kowa a gidan ta!!!! Kallonsu tayi bayan kowa ga natsa yana saurarenta tace dasu "Dama akan zancen hafsat ne da Magaji,tayaya dukkaninku kunsan airine yayi tasiri akan shi a wancan lokacin yanzu zece yanaso amayar masa da matarsa hankalinsa ya dawo jikinsa amma tsabar bakusan muhimmancin zumunci ba zaku rufe ido ku baiwa wani inada rai banma sani ba,to wlhy kunyi kadan kunji na gaya muku,na baiwa shaam auren hafsat tunda dama saku d'ayane a tsakaninsu,kuma na dawo ma da bikin wata me fita" kallonta Abba haris yayi cikin rudu yace "Innah dan Allah karki taso da wannan maganar yarinyar nan yanzu ta samu wanda takeso,kuma bazamu zamo qananun mutane ba munyi magana kuma mu dawo muce dasu wai amfasa,dan Allah ki rufa mana asiri maganar nan tunkan ta tashi daga nan mu barta" kanwar haris me binsa ma tasa baki kowa dai yayi magana tana jinsu seda duk suka gama sannan ta kallesu tace "Dukkaninku nan baku isa kun sauyan ra'ayi ba,sannan idan qaranta kuke gudu ni nan bana gudunta,ku sani wlhy ko yau na mutu duk wanda ya sauya wannan maganar tsakanina dashi Allah ya isa ban yafe ba" zaro ido sukayi dukkansu suka shiga lallami da ban baki,amma qememe tace dasu acikinsu ma wanda ya kuma tada zancen bata yafe ba,indai ba akan zancen bikin bane,kar wanda yazo mata dashi kuma kartaji sun sanar wa Alhj wato mahaifinsu" ai gaba d'aya mamaki ne ya damqe ilahirin su,suka silale d'aya bayan d'aya..... Mom Nu'aiym ce [2/6, 9:16 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅 Love story 2018 Billy galadanchi *HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.) Wattpadd@ 68billygaladanchi *Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha* 20 Zirga zirga abba haris keyi tamkar me ynqurin naquda,sam ya kasa gayawa hafsat meke tafiya gata durqushe a gabansa amma se gumi yake had'awa,kar yarunyar nan tayi tunanin cewar san kai yake mata akan d'ansa,ganin yayi shiru beyi magana ba ya sanya takuma cewa "Abbana gani" jikinsa ne yayi mugun mutuwa jin takirasa da abbanta, yasani hafsat duk gatan da mahaifinta keyi mata gani takeyi tamkar shine ya haifeta kuma yafi santa,hannu ya sanya ya rage zufar data tsatsafo masa a goshi sannan yace, "jeki ki dakko mayafinki kizo mu je wani wuri" dubanshi tayi haka kurun taji qirjinta na dokawa kuma kanta ya soma sara mata,jiki a mace ta miqe zuwa part nasu ta sako hijab a saman doguwan rigar atamfar dake jikinta tafito...... *A parlor daddy* Tunda hafsat ta ga kowa zaune har yaa shaam jikinta ya mata sanyi,gaba ki d'aya setaji wani iri,zama tayi yaukam ma akasan carpet ta gayar da kowa,kallonta daddy yayi yace "Hafsat ina fatan kin san cewar mu iyayenki ne kuma mun isa mu sakaki komai a yanda muke so muke kuma ganin ya dace?" kallon su tayi d'aya bayan d'aya sannan ta sauke idanta akan yaa shaam dayake ta faman murmurshi a hankali hawayenda suka taru mata tun farko suka silalo,ta gyad'a mar kai alamar gamsuwa da jawabinsa sannan yaci gaba "kuma kinsan cewar dukda muke iyaye a wurinku muma muna da iyayen dasuke sakamu abu adole koda bamaso se munyi shi?" nanma d'aga masa kai kurun tayi wannan lokacin kam tana kuka sosai,ganin yaa shaam na murmushi ta gano da babbar matsala,daddy yaci gaba "Innah ce da kanta tayi mana umarni akan lallai mu d'aura aurenki da shammaz nanda wata d'aya me zuwa,kuma idan d'ayanmu ya sauya wannan maganar ko bayan ranta bata yafe masa ba" qirjinta ya dad'a dokawa fiye da da,ta d'ago cikeda razani ta kalleshi,idonta ya kada yayi jajir yanzu kam tama kasa kukan se quna da zuciyarta keyi,miqewa tayi ranta a b'ace ta qarewa kowa kallo sannan ta kalli Abba haris tace cikin wata murya me d'aci wacce basu santa da ita ba "Abba na da gaske wai Innanku ne ta fad'a haka ba shiri bane wannan,na tabbatar kai kadaine zaka sanarmun zallar gaskiya" wasu yawu ya had'aya dak'yar masu d'acin gaske sannan yace dak'yar "Inna ce ta bada umarnin nan jiya hafsat" hijabinta ta gyarawa zama sannan tace " To yayi" Ta juya da gudu zuwa waje batare da tasan me yake damunta ba ko ina zataje ba,daddy da Abba haris ne suka bi bayanta,da gudunta suma haka a haka tafito daga gate d'in gidan tana kawowa kuwa wata motar na dannowa da gudun fanfalaqi atake tayi mata ebar karan mahaukaciya.......dafe kai sukayi dukkansu bame abunyi haka aka cillata acikin drainage dake gefen titin,abbah haris na kuka kamar wani yaro yaje ya fada ya cirota,sam babu alamun numfashi a tattare ita,ta sume mamallakin motar ma daya kasance matashin saurayi dan gayu fitowa yayi ya taya abba haris daukarta suka saka ta mota suka fada atare yaja da karfin gaske sukayi gaba,anan suka bar abba a tsaya ya kasa koda motsi sabida rudu,dakyar ya iya komawa ciki ya kallesu yace "Bana tunanin hafsat , Zata tashi,koda kuwa ta tashin bana tsammanin mata ingantacciyar rayuwa a yanda mota tayi mata wannan eban karan mahaukaciya ta cillata a gota" momy ce ta riga kowa miqewa jin kalamansa ta dage qirji "A ina wannan ya faru Alhj?" kallonta yayi da rinannun idanunsa yace "A kofar gida yanzu data fita da gudu,ina jiye mata idan ba ajali bane ya fitar da ita" zarewa momy tayi tayi waje da gudu shi kuma ya bita, dak'yar ya samu kanta tazo aka dunguma mota bayan sun kira abba ya sanar musu suna asibitin uduth wurin dr. Say....... Say yana zaune a office abba haris ya shigo masaa birkice,dakyar ya iya sanar masa mota ta kad'e hafsa tana waje,ai banke abban yayi ya fito da gudu,Trauma suka wuce kai tsaye da ita,babban tashin hankalin say be wuce ganin pause nata yayi qasa ba sosai,sannan gashi bata numfashi daidai abu mafi ban tsoro shine jininta dakeyin qasa sosai amaimakon ya hau,yaukam kasa yin komai yayi ya janyewa wasu likitocin suyi,har yamma suna kanta sedai ba sa'a,Dr. Shuraim ne yafito ya sameshi har iffice shida abba haris da daddy,suna ganin ya shigo suka tashi tsaye,kai tsaye wurin sayyed ya nufa ya dafa kafad'arshi,hannun nashi say yafara kallo sannan ya kalleshi da kyau,yace kafin shuraim yace wani abun "Dr. Shuraim karkace dani abunda nake tsammani?" kallonshi shuraim yayi cikeda tausaya wa,duk sunsan hafsat itace xe aura kuma yana matukar santa yace "To zaka ja da ikon Allah ne sayyeed?" kafin wani yace wani abun say ya sulale wurin a sume.... Mom Nua'iym [2/7, 9:14 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44