Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

shiga sanadiyyar alawar da Salmat ta kawo masu had'e da bak'in labari a cewar shi. "Tun ba yau ba nake lurar da kai kan ka gaya mata muradin ka a kanta amma ka tsaya sanya ga abinda ya faru yanzu". Magana kan ta kasa yin ta yake yi saboda sai ya bud'a ba ki ya kasa furta komai. A hakan ya buga mashin d'in shi ya fice daga makarantar da ya ga ta koma mai tamkar . Bai gasga ta maganar ta ba har sai da ya tura manyan shi da maganar aure aka tabbatar mai cewa auren ta saura sati biyu. Har ga Allah ya so yasa mu yarinyar a matsayin abokiyar rayuwar shi, har kullum yazo kwanciya muryar tace ke yimai amsa kuwar maganar da ta yi mai, a tunanin shi duk wanda ya sa me ta ba k'aramar sa'ar rayuwa yayi ba. Fadeel kenan yaro ga Alh Ibrahim da Haj Fatima wanda yataso cikin gata da jin dad'in rayuwa har yake tunanin zai iya taka kowa ba tare da antakura shi ba. Sai gashi yanzu ya yi sanyi sosai tamkar ba Fadeel ba sanadiyyar soyayyar da ya d'orawa Zajlah tun ranar da ta rik'e mai hannu had'e da yimai nasiha kan abinda ya kusa aikatawa, sai gashi kuma ashe ba rabon sa bace. *** Imran ne had'e da Salis suka zo k'ofar gidan su Zajlah, bayan sun gaisa dasu Mal Abu ne suka yi masu bayani kan cewa abokanen Ango ne ya turo su gurin Zajlah ne. Da hakan Mal Inuwa ya shiga gidan shi ya gaya masu su shirya suna da bak'i saboda suna gidan shi. Shimfid'a aka yi masu a zaure ya fito ya gaya masu su shiga daga ciki. Zaman su bai wuce minti biyar ba Zajlah da Salmat suka fito nan suka gaisa duk da basu san su waye ba. Sarkin tsokana ne Salis ya yi gyaran murya had'e da furta. "Amaryar mu ya kike?". . Nok'e kan da tayi ne ya bayyana cewa ita ce amaryar, a ranshi yake k'iyasta lallai Mum ba k'aramin gata tayi wa Alamein ba saboda Zajlah ba tada makusa ko kad'an, don ga alama inta sa mu guri za tafi haka fresh. Gyaran murya Imran ya yi ya kai duban shi ga Salmat yana mai tambayar ta abubuwan da za suyi na aure. "Gaskiya babu abinda muka shirya sai walima wacce za'a yi cikin makarantar mu ranar juma'a ana gobe d'aurin aure". Wani dad'i ya ziyar ci zuciyar su Salis duka sanadiyyar jin ra'ayin su d'aya da Alamein. Yanzu sun sa mu hujjar da za su kare kansu ga friends d'in su koda sun dame su da tambayar ya akayi biki babu wasu events, za su basu amsar amaryar ustaziya ce. "Ashe Ustaziya zamu aura bamu sani ba, to Allah sanya alkhairi ya had'a hankulan ku", cewar Imran. Waya Salis ya fitar yana kira tak'i shiga yakai duban shi ga Imran yana mai cewa' "ka ga wayar mutumen ta k'i shiga yana yuyuwa network ne ba kyau, kuma gashi ya ce yana so yaji zazzak'ar muryar amaryar shi". Ido d'aya ya kashewa Imran saboda ganin ce wa bai fahimci inda yadosa ba har yana batun magana ga shi yana gudun ya kwafsa mai. "Tun da ba'a sa mu wayar shi ba sai ki ba da taki number a tura mai ku gaisa kamin yadawo". "Wallahi banda waya, saboda su Baba sun hana mu rik'a waya". Ba k'aramin dad'i yaji ba da amsar da ta bashi, saboda ya san ko number ya kar6a ko kallo bata ishi Alamein ba, asali ma za ta iya zama silar samun sa6ani tsakanin su. Dubu hamsin suka zube masu domin hidimar aure inji Ango a cewar su. Da hakan sukayi sallama dasu suka fice had'e da yaba hankali da nutsuwar yaran. *** Tabbas yau ya tabbatar da cewa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, "gaskiya ba k'aramar asara nayi ba da ban sa mu Zajlah a matsayin mata ba, saboda ban zaci wannan risk'in ba ko kad'an". "Ko da ance wani bai auren matar wani Allah bai k'addar to aure tsakanin mu ba dole inyi hak'uri in fawwala ma Allah lamari na, takan yuyu ba ita ce alkhairi a gare ni ba". Duk a zuciyar shi yake wannan tunanin yana cikin tsananin tashin hankali, a hakan ya tashi ya yi nafila raka'a biyu had'e da addu'o'i ta ke yaji nutsuwa ta sauko mai. ** Suna koma wa gidan ne Salis ya saka Alamein gaba da surutu har yana ce mai, "Gaskiya friend ka gode ma Allah da wannan gatan da Mum tayi ma, wallahi ta za6o ma Mace mai hankali nutsuwa da ilmin islama, ko fa waya ba'a bari ta rik'a gidan su wallahi hakan ya burge ni sosai". "Saboda waya ga budurwa ba k'aramar illah bace, itace jigo na farko dake fara taka rawa a lalacewar tarbiyyar yara". "Duk wannan kai ta shafa kuma matsalar kace ba tawa ba, ina ruwan k'wai da aski, kuma in ka zo ne kacika min kunne da surutu sai in ta shi in ba ka guri, saboda na ga ka zo da sabon salo kiran sallah da usur". "Wa ne ni in takura Ango, ai sai dai ni in d'aga in ba ka guri". Hakan ya gama zolayar shi suka fice daga gidan. (Ina so inyi kira gare mu iyayen yara akan sake ma yaran mu domin amfani da waya, muna ganin tamkar burgewa ce ko wayewa to gaskiya wannan bai yi ba. Ba'a ce kar ku bari yaran ku suyi amfani da waya ba, sai dai ya kama ta ku saka ido akan kowan ne tako na yaran ku saboda kaucewa fad'awa hatsari. Kar kice ai shiriya ba a hannu na take ba ga Allah take, kulawar ki zai sa Allah yadubi zuciyar ki ya tallafa maki gurin d'ora tarbiyyar yaran ki akan hanya madai-daiciya. Gare ku y'an mata, ina mai kira zuwa gare ku daku tsalkake zuciyar ku akan mu'amala da waya domin sharrinta ya fi alkhairin ta yawa. Ya Allah don darajar sunayen ka tsalkaka, don k'udurarka don iradarka don k'arfin mulkin ka ka shirya mana y'ay'an mu Maza da Mata.) A DALILIN GATA Part 11-15 . Sun baro part d'in shi ne suka had'u da Mum har za su fice daga gidan, bayan sun gaisa ne take tambayar su shirye-shiryen da suke yi a game da auren. "Gaskiya Mum babu wani abu da za muyi, saboda yanzu haka daga gurin yarinyar muke ita ma babu wasu events a tsarin ta, walima kawai za su yi a islamiyar su". "Ni ma ranar assabar zan had'a k'aramar liyafa insha Allah. Ku cigaba da lurar da mutumen ku had'e da shawarwarin da suka dace, Allah yak'ara had'a kan ku yabar zumunci". "Ameen Mum, ai tsakanin mu da Alamein sai dai godiya don ya yi mana duk yanda ake yi", cewar Imran. Nan Mum ta wuce bedroom d'in Dad, ta bi shi da ido hankalin shi kwance yana karatun jarida. Gefen shi ta samu ta zauna sannan ta fara magana. "Ya kama ta a fara shirye-shirye, na ga ko I.V baka bugo ba gashi lokaci sai k'aratowa yake yi". "Kisa a buga ko Abban Yusrah yasa a buga don ni na fad'a

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38