Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

ya mutu ko? Shike nan yanzu ba mu da komai? Mum kisa a kashe wutar da takama a company". Sambatu yarik'a yi tamkar wani zautacce, hakan yasaka Mum ta fasa wani irin kuka mai cin rai. Da saurin ta ta zo ta toshe mai baki had'e da girgiza mai kai alamar yayi shiru inda ita ma sai hawaye ke sauka akan budurwar fuskar ta, ruwa ta kuma bashi tana dafe da k'irjin shi tana tofa mai addu'a, Zajlah kenan yarinya mai zuciyar tausayi. Wayar Imran aka kira had'e da gaya mai cewa an samu nasarar kashe wutar amma fa ta lashe komai na ma'aikatar wanda ko fallen takarda ba'a fita dashi ba, hakan ya yi dai-dai da kiran sallar asuba. (Hakan ya sa ni ma dole na dakata domin gabatar da farali). A DALILIN GATA Page 21-25 . Kiran sallar ne ya sa suka ta shi dukan su domin gana wa da ubangiji, matan kuwa gurin Mata y'an uwan su majinya ta suka nufa, nan aka ara masu kayan buk'ata suka sauke farali. Zajlah ta dad'e tana kwarara ma mijin ta da kuma surukin ta addu'ar samun sauk'i da kuma cin wannan jarabawar daga ubangiji, saboda ba k'aramin tausayi suka ba ta ba, asara ta farat d'aya akwai tashin hankali ba k'arami ba. Bayan mazan sun dawo ne Abban Yusrah ya umurce su dasu koma gida tunda su mazan suna nan, sai dai kash cikin su ba wanda ya ji zai iya d'aga wa nan da can ba tare da ya ga halin da Dad yake ciki ba. Mum ce ta yi k'arfin halin furta' "Zajlah kuje gida ku d'an huta, in Dad d'in ku ya farfad'o za mu iso". "Mum gaskiya bazan iya tafiya ba, kuyi hak'uri Abba har muga ya yanayin jikin Dad, amma yanzu zanje gida in samo mana abinda za'a ci". Direba ya kai ta gidan, gaggauce ta dafa ruwan Lipton sannan ta soya k'wai da dankali sai ferfesun kifi da ta yiwa Dad. Wanka ta shiga ta yo wanda ko mai bata shafa ma jikin ta ba ta zura wata doguwar riga y'ar kanti ta d'auki wasu kayan buk'ata ta fice. Ko da ta isa asibitin kowa ya yi jugum ana sauraren farfad'owar Dad, bayan ta gaida su ne ta zube kayan da ta zo dasu, kowa sai sannu yake mata sa6anin Alamein da bakin magana ya mutu sai dai binta da yake yi da ido had'e da jin tausayin ta can k'asan zuciyar shi. Dak'yar ta samu Mum ta sha tea kad'an sannan ta had'a wa Saudat ta rarrashe ta ita ma tasha kad'an, sa6anin mazan da suka nuna ba za su ci komai ba, tana so ta had'awa Alamein yasha ko kad'an ne amma nauyin Abba take ji. Fahimtar hakan ya sa ya furta' "su Mum ne ake rarrashi su karya ba za'a had'awa yaro na ba?". Cikin zolaya yake furta maganar. Kai ta soke tana wasa da yatsun hannun ta, ganin cewa tabbas ita Abba ke jira ya sa ta had'a tea d'in ta kawo mai, zurum kawai ya yi yana kallon ta sannan ya kauda kai, hakan ya sa ta girgiza mai kai alamar kar yace bai sha, nan ya kar6a ya sha kad'an ya bata cup d'in. **** 09:00am likita ya fito daga d'akin da aka kwantar da Dad, su duka suka tunkare shi domin jin ya jikin nashi, nan ya gaya masu cewa ya farfad'o za su iya shiga su ganshi amma kar su cika shi da hayaniya. Cikin murna suka fad'a d'akin dukan su, sai lokacin Alamein ya san meke faruwa da Dad, saboda ko da Abba ya yi bayani yana nashi d'akin. Kowan nen su sai da ya zubarwa Dad da hawaye akan yanda ya koma cikin awa bakwai abin gwanin ban tausayi, lallai tabbas rayuwa ba a bakin komai take ba, rayuwa da lafiya ciwo da mutuwa duk ga hannun ubangiji suke, lokacin da ya d'oro ma d'aya ba wanda ya isa ya yaye ma sai Allah, an dai samu ya farfad'o amma ba uhm ba uhm-uhm sai dai ido, ga kuma 6angaren jikin shi da bai motsawa ko kad'an. Kukan da ya zo ma Mum ne ya sa ta fita daga d'akin ta jingina ga k'ofa tana rasgar kuka tamkar wata k'aramar yarinya, saboda hango tarin matsaloli masu tsabagen yawa a rayuwar su. Tunkarar Dad ya yi yana kuka zai fad'a saman jikin shi su Salis suka tare shi, Abba ne ya bada umurnin duk su fita daga d'akin, bayan sun fice ne ya je gab da d'an uwan shi yana magana ko zai kar6a mai sai dai babu nasarar ko da motsawar la66an shi, duk da k'arfin halin da yake yi sai da hawaye suka wanke dattijuwar fuskar sa. Fitowa ya yi daga d'akin yana mai shawartar su kan a wuce da Dad f.m.c Bk. Kowa ya yi na'am da maganar shi hakan suka yita rarrashin Alamein har suka fice su duka domin duba yanayin wutar da ta ci ma'aikatar, iya bincike anyi amma ba'a gano musabbabin wutar ba. *** Su Mum kuwa gida suka fice domin yin shiri zuwa Bk. "Mum in shirya muje ko?", cewar Zajlah. "A'ah kuyi zaman ku ke da Saudat har muga yanda abin zai kasance, ke Saudat kishirya kayan ki ki koma can gidan su har mu dawo". "Mum kibari ni zan d'ebo kaya na in dawo nan har zuwa dawowar ku, Allah ya tashi kafad'ar Dad yasa ayi farar jinya". Hakan yasa Mum ta yita saka mata albarka. Da hakan ta fice ta d'auko kayan da za ta buk'ata ta rufe gidan ta dawo, Baban ta ta kira ta gaya masu abinda ke faruwa da sauran y'an uwa daya dace su san da faruwar abin. Bayan Mum ta kimtsa ne suka raka ta asibitin, acan ne suka had'u da Salmat, da Yusrah, sai kuma iyaye daga 6angarori da dama da suka cika asibitin tamkar ad'auke wa Dad ciwon da ke damun shi. Ba abinda ni kai na yak'ara firgitani tamkar yanda aka d'auko Dad za'a saka a mota kai kace gawa ce, nan matan masu raunin zuciya suka rik'a kuka. Bayan an wuce dashi ne da Abban Yusrah sai Imran, Alamein, Salis da wasu abokanen Dad biyu. Nan su Mama Asabe suka wuce jiki a sanyaye, Mamar Yusrah da Salmat da Yusrah duk gidan su Mum suka wuce. . Kwanci tashi yau Dad satin shi biyu a asibiti ana yi mai gashin jiki wanda ga alama sauk'i ke shiga kad'an-kad'an, wanda har yanzu bakin shi bai koma dai-dai ba abin ya zamo tamkar mai kariyar halshe. ** ** ** 6angaren su Zajlah kuwa ita da Saudat da Yusrah suke kula gidan, saboda tun lokacin da ta biyo su daga asibitin take gidan, sun je ganin Dad kusan sau biyar, haka ma su Mal Inuwa sun je sau biyu duba jikin na shi sai dai fatar Allah yakawo sauk'i. * * * Yau ne aka sallamo Dad daga asibiti ba wai don ya murmure duka ba sai don ganin irin tsabagen kud'in da ake ci na jinya kuma ciwon sai dai hamdala ya sa Mum ta yi shawara da Abban Yusrah kan su nemi sallama aje gida a had'a da addu'o'i. . Ba hakan likitoci suka so ba,

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38