Chapter 27
Chapter 27
gidan nan?", cewar Shema'u. "Kai Anty shaidar da za kiyi min kenan, yanzu fa zuwa na na uku kenan gidan nan, ai gara ni kefa zuwan ki biyu". Da hakan dai suka gama zolayar juna sannan suka gaisa, jugum ta yi kamar kar ta furta abinda ya kawo ta, sai kuma take tunanin duk duniya bayan Salmat babu wanda za ta iya gayawa halin da take ciki bayan Shema'u d'in, saboda ta yaba da hankali da nutsuwa irin tata, kuma ba mace ce mai yawan surutu ba ga alama za tayi rik'on sirri kuma gashi za ta girme ta da kusan shekara shida ko bakwai, sai da ta gama nazarin ta Shema'u na gurin kawo mata ruwa da d'an lemo ta dawo kenan take furta mata abinda ke tafe da ita kan ta yi mata magana da masu sayen kayan d'aki. "Ke ko Zajlah me zai kai ki siyar da kayan d'akin ki?, duka fa aure ko wata hud'u bai yi ba za ki siyar da kayan d'aki". Nan ta kora mata bayanin abubuwan da ke faruwa, sannan ta bata tabbacin za ta sa a nemo masu siya. "Kinga ko banyi mutunci ba wallahi ban shiga yiwa Mum Allah ya tsare gaba ba da abinda ya faru, Baban su Taheer d'ai yaje dubiya sau biyu". "Yanzu ko daga nan can zan shiga", "ina ga bara in d'auko hijab d'ina muje tare in dawo". Hakan suka fice zuwa gidan su Alamein, Shema'u ta yi jaje da Allah tsare gaba ta koma gida. ***** Su Imran suka samo masu sayen gida aka yi ciniki suka sai da inda Alamein ya nemi su bashi kwana biyu ya kwashe kayan shi daga gidan, da hakan suka fice zuwa gidan su shi da su Salis. Kamar yanda Shema'u ta yi alk'awari hakan ya sa ta nemo masu siyen kayan d'aki aka dace da masu siyen su cikin daraja Zajlah ta sai da, kayan kitchen sai kayan falo da keken d'inki kawai ta bari. ** 6angaren Alamein kuwa yaje gida gurin Mum sun tattauna yanda abubuwan suka kasance, sannan ya d'ora da gayawa Mum tasa a gyara masu d'ayan part d'in gobe da safe zai samu way'anda zasu kwaso masu kayan su, da hakan ya wuce gidan shi. Motsi ya ji a kitchen alamar Zajlah na ciki, yana son yashiga ya gaya mata ta kimtsa kayan ta zuwa gobe za su koma gidan Mum kuma yana jin nauyin yanda zai yi mata magana, saboda tun zamantakewar su maganar arzik'i bata ta6a had'a su ba, hakan ya sa ya tunkari kitchen d'in gaban shi na dukan tara-tara. Alamar mutum ta ji a bayan ta ta juyo ta ganshi tsaye ya jingina da k'ofa ya sako mata ido, "sannu da zuwa", cikin sark'ewar murya da in ina ta furta hakan. Da sakewar fuska ya amsa mata sannan ya d'ora da cewa "kar kiyi girkin dare saboda yau za mu yi parking kayan mu gobe a kaisu can, don an sayar da gidan kamar yanda kika buk'ata". "Ba matsala Allah ya kai mu lokacin", da hakan ya wuce d'akin shi. Bayan ta gama girkin ne ta ajiye mai nashi ta d'ibi nata ta ci, sai ta yi zugum tana so taje d'akin shi ta had'a mai kayan shi guri d'aya amma bata son abinda zai had'a ta dashi guri d'aya kuma tasan yanzu yana d'akin bai fita ba. Hakan dai ta daure ta nufi d'akin shi, ta fi minti biyar bakin k'ofa tana sak'a yanda za ta Shiga d'akin, jin motsin zai fito yasa ta k'wank'wasa k'ofar. Mamaki ya hana shi bud'e k'ofar ya yi zurum, sai da ta buga a na ukun sannan ya murd'a k'ofar ya ra6e gefe d'aya. Tsaye ta yi tana wasa da yatsun hannun ta sannan ta furta, "kayan kane zan had'a ma". Hanya ya bata alamar ta shiga d'akin, k'ofar ya rufe ya dawo ciki shi ma, ganin hakan ya sa gaban ta ya bada daram!, saboda ta zata fita zai yi don da shirin shi ta ganshi. "Hala kin kammala na ki kayan guri d'aya?", tambayar ce ta doki dodon kunnen ta. "Eh" ta furta a gajarce. "To bara in kama maki aikin saboda suna da yawa". "Ah da ka wuce kawai ai zan iya tunda ba girkin dare zanyi ba", ta furta hakan ne saboda ta fi so ya fita ya bata guri tayi aikin ta za tafi Samun sakewa, amma tasan zaman shi zai takura ta. Shi ma 6angaren Alamein gidan su ya yi niyyar zuwa ya turo Saudat a zuwan za ta kama ma Zajlah had'a kayan, to yasan in har ta zo to Zajlah za ta kama suyi aikin tare ne, amma da ta nuna za tayi ne ya sa ya fasa fitar. Nan dai suka zauna jigum ba mai magana, shi ya yi k'arfin halin bud'e wardrobe yana jido kayan shi yana d'orawa saman gado, sannan ya bata umurnin ta d'auko akwati na ta jera kayan a ciki, ba k'aramin mamaki ta yi ba ganin yawan suturar shi kama daga manyan kaya zuwa k'anana. 6angaren turarukan shi suka koma ana jibga su guri d'aya, ta d'auko wani turare za ta ba shi yasaka a wata jaka karaf hannun su ya had'u guri d'aya, wani shocked da suka ji ne ya sa cikin sauri dukan su suka janye hannun su kowane a tsammanin shi d'ayan ya rik'a, hakan yasa kwalbar ta sauka k'asan tiles ji kake yi tarassss, da sauri ta ja baya sai ga k'afar ta saman kwalbar da ta fashe ta watsu a gurin. K'ara ta saki da k'arfi ta rik'e k'afar tana yarfe hannu, da saurin shi ya zo gurin ta ya bata umurnin ta zauna bakin gado, dak'yar ya samu ta tsaya ya cire mata guntun kwalbar inda jini ke ta zuba, nan ya samu ya yi mata dressing gurin had'e da duban ta irin yanda take ta zubar hawaye tana cije le6e had'e da runtse ido. Nan ya barta ya je ya kwashe kwalbar ya k'arasa had'a kayan, sai murmushi yake yi shi kad'ai ganin yanda ta yi kuka had'e da shagwa6a tamkar wata k'aramar yarinya, hakan ya sa ya ji ta burge shi. washe gari Jakar ta ta hannu kawai ta d'auka ta fice daga gidan tunda ya gaya mata zai samu way'anda za su kwashe kayan duka akai gidan su, ko da ta fita ko ruwan Lipton bata sha ba saboda ya gaya mata kar ta kunna komai na amfanin girki, kuma Mum ta kira ta gaya mata cewa za ta yi girkin safe dasu. Karfe 10:00am ta shiga gidan, bayan ta gaida Mum ta yi mata jagora ta k'ara duba jikin Dad had'e da gaida shi sannan suka dawo falo suka zauna. "Meke damun ki naga kina Jan k'afa?", Cewar Mum. Nan ta labarta mata abinda ya same ta da suna gyaran d'aki, jajanta mata tayi ganin abin da d'an sauk'i. "Ina Saudat halan? Banji motsin ta ba". "Ta ji sauk'i yau ta wuce skul, kinsan tun ciwon Dad bata koma skul ba, to suna ta shirye-shiryen exam ta k'arewa shiyasa yau ta je", "ok Allah ya taimaka". "Amein", ta furta sannan ta had'awa Zajlah kayan kari ta kai mata falon ta saboda tasan ba za taci tare da su
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38