Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

bakin ta ta yi shiru. D'aki Mum ta wuce tabar Saudat zaune a falon, ganin hakan ya sa ta bi sawun su Dad. ** Sanadiyyar yau ta kama alhamis ba islamiya ya sa tun safe tana siyo masu koko suka sha ta hau wankin su ita da Baban ta. Bayan ta gama ne tayi shara ta tsaftace gidan, yau girki ta d'ora masu sanadiyyar tsakin masarar da Mama Inno ta ba su jiya wanda zai kai kwano uku. Waje ta fita ta yi sa'a da yaran da ke tallan zogale dafaffe nan ta siyo ta had'o da d'an magi ta koma gidan. Faten tsakin masara ta yi wanda yaji zogale. Sai da ta samu guri ta saka ma su Mama Inno faten ta kai masu sannan ta dawo gidan. Ruwa ta ebo ta kaiwa Baban ta ya wanke hannun shi ita ma ta wanke sannan suka yi Bismillah suka fara ci. Suna gama wa ruwa ta fara kai mai ya yi wanka sai da ya fito ta taimaka mai ya shirya yana ta sanya mata albarka sannan ta shiga wankan ta fito. Sai bayan la'asar yau suka fita yawon su na bara, daka gansu tsaf dasu sai dai talauci dake barazana dasu. Hakan ta gayar da mutanen gurin sannan suka nemi guri suka zauna, sai gab da magrib suka wuce gida inda ya tsaya gurin su Mal Inuwa itako ta shiga gidan su Salmat. Sallah suka fara gabatarwa bayan sun k'are ne suka rik'awa juna bitar haddar su domin su k'ara daddak'awa. "Salma zo ki lek'a daga waje ki kira Sagiru yakaiwa su Baban ku abincin su". K'ur'anin ta ajiye ta fice bayan ta kira shi ne sannan ta dawo masu da nasu abinci d'akin, nan suka ci suka gama sannan suka gabatar da isha sai k'arfe tara sannan Zajla ta fita ta ja Baban ta suka wuce gida. . Zaune suke saman dinning table suna breakfast sai tattaunawa suke yi akan lamarin company. Sai da aka yiwa wayar shi Kira biyu ana ukun sannan ya d'aga wayar ya nufi hanyar d'akin shi, gaisawa suka fara yi sannan ya fara magana fad'a-fad'a had'e da ya mutse fuska. "Kana sane da ce wa duk inda ake taro in har akwai Mata ba na nufar gurin, saboda haka kuci gaba kawai idan kun gama ma had'u, ka isar da sak'on taya murna ta zuwa ga Salis, in ya natsu zan kira shi". Yana kai k'arshen maganar ya dak'ile wayar shi ya bita da wani kallo tamkar ta yimai wani laifi, gado ya fad'a domin ya d'an huta saboda ba mutum ne maison fita ba. ** Kwanci ta shi asarar mai rai, yau ta ka ma Larba wanda Zajla sai gaban ta ke fad'uwa sanadiyyar tunanin da wuya Ustaz Lukman bai fitar da ita cikin masu karatun k'arshen sati ba. Kamar kullum yau ma hakan ce ta kasance, bayan gabatar da sallahr azahar suka shiga class domin bitar haddar su saboda k'aratowar lokacin musabak'ar su. Bayan an gama sallar la'asar ne aka fitar da mimbari da kujeru domin zama tsakiyar makarantar a gabatar da ire-iren abubuwan da ake koya masu. Mutum uku cikin maza suka gabatar da yadda ake taimama da kuma sallar gawa, sai matan biyu da suka gabatar da koyar da alwala a aikace. Zajla ce za ta gabatar da bayanin wankan tsalki da kuma addu'o'i. . Bayan ta yi basmala ta gabatar da sunan ta da Zajla Abubakar Zubair sannan ta fara da ce wa'. "Shi dai wankan tsalki ya kasu zuwa kashi-kashi, akwai wankan janaba, akwai wankan haila, akwai wankan d'aukewar jinin bik'i (jego) da sauran su. "Kamar yanda kuka sani su dai wad'annan abubuwan wanka iri d'aya ake yi masu sai dai niyyar su ce data ban-ban ta". "Da farko za'a so mutum ya sa mu ruwan shi tsaftatacce, wa'anda kalar su bata canja ba, d'an-d'anon su bai canja". "Anan abinda ake nufi da kala ko d'an-d'ano shine kar mutum ya d'ebi ruwan Lipton ko ruwan wankin shinkafa ko ruwan da ke da gishiri yace wankan tsalki zai yi dasu". "Da farko mutum zai fara wanke gaban shi, bayan ya wanke zai wanke hannun shi saboda najasar da ya ta6a, zai d'ebo ruwa har sau uku yazuba ma kansa, ya murza kansa har ruwan sukai k'asan kansa, daga nan zai yi alwala shud'i guda-guda sannan ya wanke 6angaren jikin shi na dama daga sama har zuwa k'asa, 6angaren hagu ma haka sannan ya game jikin sa da ruwa ya murza ko ina". "An samu sa6anin wasu maluma da suka ce idan mutum ya wanke gaban shi zai fara gabatar da alwala, wasu kuma sukace sai bayan ya k'are wankan gaba d'aya sannan yayi alwalar. Allah masani". "Addu'ar shiga kewaye (( Allahumma inni A'uzu bika minah khubithi wal khaba'ithi)) "Addu'ar fitowa daga kewaye". ((Gufranak)) "Addu'ar mugun mafalki". ((Allahumma inni A'udhu bika min sharri ma ra'aytu fii manaamee an yadurranee fii deeni wa dunyaay)) "Addu'ar kariya daga azabar k'abari". ((Allahumma innee As'alukar Jannah, wamaa k'arraba ilaiha min k'aulin wa amal, wa A'udhu bika minan naar wama k'arraba ilaiha min K'aulin wa amal, wa A'udhu bika min fitnatil mahya wal mamat wa min fitnatil k'abr wamin fitnatil masihid dajjal wamin Adhabin naari wasu'il maseer)) "Addu'ar neman ya fiyar sa6o. ((Allahumma inni a'uzu bika an ushrika bika wa ana a'alam wa astagfiruka li maala a'alam)) Gyaran muryar da akayi da speaker shi ya nu na mata alamar lokacin ta ya yi, speaker ta ajiye ta koma mazaunin ta. Kabbara ce ta biyo baya had'e da jin-jina mata akan abubuwan da ta gabatar. Nan akayi salati ko wa ya ka ma gaban shi sanadiyyar gabatowar magriba, kowa da maganar (ZAZ) ya fita a bakin shi sanadiyyar add'o'in da ta yi tamkar itama Malama ce ba d'aliba ba. . Gaskiya (ZAZ) kin kawo wuta sosai yau, kinji yanda kike rero addu'o'i tamkar Ustaz Yusuf?". "Banson sharri wallahi, kina ji yanda murya ta ke wani rawa-rawa alamar tsorace nake. Ni fa shiyasa kika ga ko wannan musabak'ar da za muyi gabana ke ta fad'uwa saboda na k'i jinin karatu a cikin bainar jama'a". "Tabbb ai wannan shafin mai ne wallahi, kina ganin yanda ake taro sosai idan lokacin musabak'a yayi. Kuma hakan da ake yi duk Larba anaso abin yabi jikin mune har mu saba mu daina jin tsoro", cewar Salmat. "Ranar da duk Ustaz Lukman ya ji kina furta wannan (ZAZ) d'in a bakin ki kya yi bayani, saboda kinsan ya ce adaina kira na da hakan". "Yo ai ba sai kin gaya min kina da mai tare maki ba, duk kauce-kaucen ku za ku fito kuyi bayani ne". "Shin tsaya me kike nufi ne, ban fahimce kiba?". "Kinsan dai ko kin 6oyewa ko wa soyayyar ku da Ustaz Lukman bai dace ni ki 6oyemin ba". Cikin gwalo ido da wani cin birki tamkar mai tuk'in mota ta ja ta tsaya, mamaki kwance fal a fuskar ta. "In har kin yarda kalmar "So" bata ta6a ratsawa tsakanina dashi ba, sai dai mutunci". "Ke ce baki fahimci hakan ba, amma duk wanda ya yi mai duba na natsuwa idan kina gaban shi to zai hango son ki kwance a k'wayar idon shi". "Allah yashirye ki, ke kika san wani abu "So" ni kam da saura

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38