Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

A Dalilin Gata Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

na". "Ke ma za ki sani idan lokacin kisani yazo, wa yaga ana soyewa tsakanin Malami da D'alibar shi". "Allah ni ko guntun namiji bai cikin tsari na ko Aure zan yi, na fison dogon namiji wanda zai yi guda da rabi d'ina". Dundu Salmat ta kai mata had'e da furta, "makira kika ce baki san So ba kuma amma ga shi kina wassafa mijin da kike son Aure". "Shi ne sai aka ce maki wassafa ra'ayin ka shi ne So d'in?".. Yanzu bara in tambaye ki akawo maki gabjejen namiji wanda yayi hud'u d'in ki ya kika ga abin?", tana maganar ne had'e da dariyar k'eta. "Bakin ki yasari d'anyen kashi muguwa kawai, Allah ya kiyaye ni". Dariya Zajlah tayi sosai akan yanda Salmat ke maganar had'e da ya mutse fuska tamkar ga mijin nan gaban ta. Da hakan suka k'araso gida sannan suka gabatar da duk wani abu daya dace kafin Zajla taja sandar Baban ta su wuce gida. ** Har gida yau suka kawo mai ziyara shi da Salis, bayan sun gayar da Mum suka fita gardener, saboda a al'adar shi in har yana gida indai ba bacci yake yi ba to nan ne gurin hutawar shi. "Gaskiya (A.K.A) baka kyauta min ba, yanzu ace ayi birthday d'ina ko wa ya hallara kai baka je ba, kuma kana sane da ce wa duk duniya banda friends d'in da suka wuce ku kai da Imran". "To ku ne da jaye-jaye kuce duk abinda za kuyi sai kun saka Mata a ciki shi ne birgewa a gare ku, ni ko in har hakan za ta cigaba da kasancewa to ina mai tabbatar maku za kuyi lamurran ku ba dani ba". "Ni wannan abin na ka na d'aure min kai, zanga ranar auren ka da kuma matar da za ka aura, saboda wannan abin na ka ya yi yawa", ce war Imran. Murmushi ya rik'a yi sama-sama wanda har fararen hak'oran shi na bayyana had'e da dimple d'in shi. "indai ku kuka ta shi auren Allah sanya alkhairi don kunsan ba dani ba a y'an dinner da sauran su, zan dai je d'aurin aure shi ne na mu". Kallon da suka bi shi dashi ne ya sa ya yi saurin kauda kan shi yana dariya k'asa-k'asa. "Ka ma mayar damu wasu sha ka wuce za ka gani ne. Na ma manta in gaya ma Lubnah ta ce in ba ta number d'in ka". Mugun kallon da ya yimai ne ya sa ya fahimci amsar da yake nufi zuwa gare shi. "Baiwa wata Mace number ta na nufin rabuwar mu ta har abada dakai, ka sanni kasan waye ni. Duk cikin contacts d'ina number Mace biyu nake da, Mum da Lil Sis". Cikin 6acin rai ya mik'e ya tattara wayoyin shi ya nufi hanyar shiga gida, duk yanda ya so tsayar dashi don ya nuna mai wasa yake yi abin yaci tura. Bayan ya shige ne gidan Imran ya kai duban shi ga Salis had'e da hararar shi sannan ya furta. "Sai ka ta shi mu fice tunda ka takaro zuciyar manya". Dariya sosai Salis ya yi had'e da furta. "Ni fa suk'uwar shi dariya take ba ni, da abin 6acin rai da wanda bana 6acin rai ba za kaga ya had'e fuska ala dole shi fushi yake yi". "Allah wataran da gayya nake tsokanar sa saboda inyi dariya". "Don kasan duk rintsi yana tare damu ne, ko ya yi fushi dole yasauko shiyasa kake mai hakan", ce war Imran. Hakan suka had'a nasu da nasu suka fice saboda sanin in kwana za suyi gurin bazai kuma kula su ba sai ranar da ya sauko daga zuciyar. . . Kamar kullum yau ma ta gama kimtsa komai na kula da gidan suka shirya suka fito sai mazaunin su na bara, wanda kullum suka fito wani irin mugun nauyi take ji a ranta. Saboda a tunanin ta kamar ta ya ci ace ta wuce zama y'ar jagora, sai dai ba yanda za tayi sanadiyyar in har bata kula da mahaifinta ba wa ye ta ajiye da zai kula dashi yanda yadace. . Ga shi dai in har ta ce baza su fito yawon bara ba to batasan wa zai ciyar dasu da sauran lalurorin su ba, tunda mahaifinta ba yada idon da zai fita yane mo musu abinda za suyi lalura. Don ma Malam Inuwa na k'ok'arin basu abincin dare, duk da shi kan shi ba wata wadata ce dashi ba saboda ba kullum za'a ci abinci sau uku a rana gidan shi ba. Duk ita kad'ai ke wannan tunanin a ranta, wanda har kullum take tunanin ina za ta ne mo masu mafita akan wad'annan matsalolin. Sanadiyyar bugawar da motocin biyu suka yi ya janyo hankalin tsirarrun mutanen da ke zaune gefen hanya. Dattijuwar na fitowa daga motor ta ya tayarda hannu zai sharara mata mari. Hannun da ya ji ya rik'e na shi hannu ne ya bi da kallo. "Ka daraja mutum ko da baka san shi ba, wanda ya girme ka haka yake tamkar yaya a gurin ka, haka zalika wanda ya yi sa'ar mahaifin ka tamkar mahaifin kane". "Bai kama ce kaba kuma hakan bai dace dakai ba, yanda ka daraja manyan ka haka Allah zai sa a daraja na ka iyayen ko bayan idon ka". Cikin sanyin jiki ya bi dattijuwar matar da kallo, sai wata irin kunya ce ke ratsa ga66an jikin shi, hak'uri yafara bawa matar had'e da neman yafiyar abinda ya tashi aikatawa. Su duka biyun suka bi gurin da kallo domin ganin ta ina za su ga yarinyar amma ina ta 6acewa ganin su. *** Sandar mahaifinta ta rika suka doshi hanyar gida. "Zajla ki daina saka kan ki a cikin rayuwar wa'annan mutanen, ba mutunci ne dasu ba". "Baba ai Ba komai na yi ba nasiha ce kawai na yimai saboda abinda naga ya kusa aikatawa bai dace ba". "To Allah yamaki albarka yaba ki miji nagari inga auren ki da jikoki na". "Baba ni fa na gaya ma bazan yi aure ba, saboda bansan wa zai kula dakai ba", tana maganar ne had'e da zum6uro baki tamkar yana ganin ta. "Haba Zajla kidaina fad'ar hakan, Allah zai kula dani saboda shi ya so gani na hakan kuma zai ya yemin lokacin da ya so. Tunda abin ciwo ne bana halitta ba kuma daga baya ya same ni". "Baba kayi ta addu'a Allah yaba ni hanyar samun kud'i insa a gyara ma idon ka". ** Fitowa tayi da sunan kai ziyara company maigidan ta, amma sanadiyyar abinda yafaru ne ya sa duk ta ji ba za ta iya k'arasawa ba akalar motar ta taja takoma gida. Da shigar ta falon Saudat tagani zaune tana waya, ganin shigowar Mum ne ya sa ta yi saurin tsinke wayar had'e da mik'ewa tsaye. "Mum ba dai har kinje company kin dawo ba?". "Ban k'arasa ba na dawo". Ta ba ta amsa a tak'aice, ganin 6acin rai kwance saman fuskar Mum ya sa bata k'ara magana ba. "Me ya hana ki zuwa skul yau?". "Mum fa har na shirya Hafsat takira ni ce wa lecturer d'in bai zo ba shiyasa nayi zama na saboda dama yau shi kad'ai muke da". . Bayan ta bawa y'an aiki

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38